Friday, December 19
Shadow
Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Wata farfesa a kasar Amurka me suna Dr. Sandra Duru ta zargi Sanata Natasha Akpoti da nemanta da ta kullawa Sanata Godswill Akpabio sharri tace yana safarar sassan jikin dan Adam. Dr. Sandra Duru ta bayyana hakane a cikin hirar waya data nada da suka yi ita da Sanata Natasha Akpoti. Saidai Sanata Natasha Akpoti tace ita bata ma santa ba, dalili kenan da yasa Dr. Sandra Duru ta mikawa jami'an tsaro hirar da suka yi dan su yi bincike akai. Rahoton yace Sanata Natasha Akpoti ta yi hakanne a yayin da ta ga cewa sharrin da ta ke shirin kullawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio na cewa ya nemeta da lalata bai yi nasara ba. Matar wadda kuma 'yar jarida ce tace Sanata Natasha Akpoti bata da wata hujja akan zargin da takewa kakakin majalisar.
Da Duminsa: Kalli yanda Matan Jihar Rivers suka tashi suka kama gabansu yayin da ake tsaka da taro matar shugaban kasa, Remi Tinubu na jawabi, sun ce basa son jin jawabinta, Ance bai kamata su kunyata matar shugaban kasar irin haka ba

Rahotanni daga jihar Rivers sun ce matan jihar sun kunyata, matar shugaban kasa, Remi Tinubu yayin da ake gudanar da wani taro inda ana tsaka da taron suka tashi suka kama gabansu yayin da ta tashi take jawabi. Sun ce basa son jin jawabinta, jawabin matar dakataccen gwamnansu, Simi Fubara suke son ji. https://twitter.com/Jmartinsijere/status/1918268255355150504?t=fyRKau1lIoSZR6mBNTqBOQ&s=19 https://twitter.com/PH_Socials/status/1918254642372460688?t=temFX-6zzhfCPtMH45NXWA&s=19 Da yawa sun jinjinawa matan saboda wannan kokari
Munin Tattalin arzikin Najeriya a yanzu yafi na lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yanci a shekarar 1960>>Inji Shugaba  Bankin Afrika

Munin Tattalin arzikin Najeriya a yanzu yafi na lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yanci a shekarar 1960>>Inji Shugaba Bankin Afrika

Duk Labarai
Shugaban bankin Afrika, AFDB, Dr Akinwumi Adesina ya bayyana cewa, lalacewar tattalin arzikin Najeriya a yanzu ya fi muni fiye da lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1960. Ya bayyana hakanne a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Alhamis. Yace Abinda ake cewa GDP per capital wanda shine ake auna ma'aunin tattalin arzikin kasa dashi a yanzu yana kan Dala $824 ne. Yace a yayin da a lokacin da aka baiwa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1960 GDP per Capital yana kan Dala $1,847 ne. Yace hakan ba karamar matsala bace inda yace ya kamata Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye dan shawo kan wannan matsalar.
Hukumomin kasar Amurka sun nemi a kara musu kwanaki 10 kamin su fitar da bayanan zargin safarar miyagun Kwàyòyì da akewa shugaban Tinubu

Hukumomin kasar Amurka sun nemi a kara musu kwanaki 10 kamin su fitar da bayanan zargin safarar miyagun Kwàyòyì da akewa shugaban Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, Hukumar tsaro ta FBI da masu kula da harkar kwayoyi sun nemi a kara musu kwanaki 90 kamin su fitar da bayanai kan shari'ar zargin da akewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ta Safarar Kwayoyi. Ana zargin a shekarar 1990 ne dai Shugaba Tinubu da wasu mutane 3 Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, da Abiodun Agbele suka yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na kasar. Wani lauya a kasar Amurka, Aaron Greenspan ne ya nemi wadannan bayanai. Kuma kotu ta nemi hukumomin FBI da DEA su fitar da bayanan inda aka saka ranar 2 ga watan Mayu dan fitar dasu. Saidai yayin da ake dakon jiran wadannan bayanai, wadannan hukumomin sun bayyana cewa basu kammalu ba sai nan da kwanaki 90. Saidai Lauyan Aaron Greenspan ya bayyana cewa, kwanaki 90 ...
ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu ‘Yan ‘Halal Match’ Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba

ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu ‘Yan ‘Halal Match’ Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba

Duk Labarai
ALLURAR CIKIN RUWA: Duk Wadda Take Sona Da Aure Kofa A Bude Take, Kawai Ta Samu 'Yan 'Halal Match' Ta Ba Su Lambarta Su Ba Ni, Domin Ina Bukatar Auŕe, Inji Babba Ina 'yan mata? Kada ku bari wannan damar ta wuce ku! Alhaji Babba dai yana ikrarin shi matashin mai kudi ne. Kuma gashi mutum mai yawan fara'a.
KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar

KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar

Duk Labarai
KATSINA BA KORAFI: Gabanin Zuwan Tinubu Jihar Katsina An Hango An Rubuta Katsina Ba Ƙorafi A Allon Da Aka Sanya A Bakin Hanya Duk A Shirye-Shiryen Tarbar Shugaba Tinubu Zuwa Jihar Hakan na nufin Katsinawa sun gamsu da salon mulkin Tinubu kenan? Menene ra'ayinku?
Atiku Da Tinubu bai kamata su fito takarar shugaba cin Najeriya a shekarar 2027 ba>>Inji Baba Ahmad

Atiku Da Tinubu bai kamata su fito takarar shugaba cin Najeriya a shekarar 2027 ba>>Inji Baba Ahmad

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, da Atiku Abubakar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kamata su tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2027 ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV. Yace maganar tsayawa takarar Atiku a 2027 bai kamata ba, tunda ya gwada bai yi nasara ba, kamata yayi ya koma gefe ya zama mai bayar da shawara. Yace Tinubu ma haka ya dace dashi musamman ma lura da yanda tattalin arzikin Najeriya ya samu kansa. Yace har Peter Obi duk kamata yayi su hakura in kuma basu hakura ba, 'yan Najeriya su musu ritaya.
An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya

An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya

Duk Labarai
An shawarci Atiku cewa kar ya hada kai da El Rufai, domin zai sake yin kuskuren da yayai abaya ne, lokacin daya kai El Rufai wurin Obasanjo amma ya juya masa baya. Atiku ne dai ya gabatar da El-Rufai a wajan Obasanjo wanda daga baya aka bashi mukamin Ministan Abuja amma daga baya adawar siyasa tasa ya rika adawa da Atikun. Saidai yanzu sun sake hadewa.
Karyace ‘Yan Arewa na zaune cikin aminci da walwala kuma suna mallakar gidaje a yankunan mu>>Inyamurai da Yarbawa suka mayarwa da Dattawan Arewa martani kan cewa ‘Yan Arewa basa mallakar Filaye da gidaje a Kudu

Kungiyoyin kare muradun Inyamurai da Yarbawa na Afenifere da Ohanaeze IndiIgbo sun mayarwa da kungiyar tuntuba ta Arewa, Arewa Consultative Forum martani kan zargin da ta yi na cewa ba'a bari 'yan Arewa na mallakar Filaye da Gidaje a kudancin Najeriya, Musamman yankin Inyamurai. Kungiyar Ohanaeze Indigbo ce ta fara yin martanin inda tace 'yan Arewa da yawa na zaune lafiya a jihohin Inyamurai kuma wasunsu sun mallaki gidaje kuma babu me takura musu. Kungiyar ta bakin mataimakin sakataren yada labaranta, Mazi Godwin Okenwa tace Inyamurai suna da karbar baki a duka jihohinsu. Hakanan itama kungiyar kare muradin Yarbawa ta Afenifere tace wannan zargi ba gaskiya bane, kawai suna son saka siyasa ne a ciki. Kungiyar ta yo maganane ta bakin kakakinta me suna Jare Ajayi inda yace irin ...
Kalli Hotuna da Bidiyo yanda Ake zargin dan shugaban kasa, Seyi Tinubu yawa shugaban daliban Najeriya Tsirara yasa aka masa dukan kawo wuka jikinsa Duk burdi, kawai dan yace ba zai karbi Naira Miliyan 100 ba ya goyi bayan Tinubu

{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban daliban Najeriya, Ya zargi dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban NTA da wasu hadiman shugaban kasar da gayyatarsa zuwa Legas dan ya karbi Naira Miliyan 100 ya ce yana goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Saidai yace ya ki amincewa da wannan bukata. A wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta, An ga shugaban daliban yana cewa saboda ya ki amincewa da bukatarsu, sun sa an lakata masa duka aka dauki bidiyonsa tsirara aka kuma ce masa ko kashesh...