Tuesday, December 16
Shadow
Mataimakin shuaban kasa, Kashim Shettima ya isa Jihar Delta dan karbar gwamnan jihar da ya koma APC

Mataimakin shuaban kasa, Kashim Shettima ya isa Jihar Delta dan karbar gwamnan jihar da ya koma APC

Duk Labarai
Mataimakin shuaban asa, Kashim Shettima ya isa birnin Asaba na jihar Delta dan karbar gwamna jihar, Sheriff Oborevwori da ya kom jam'iyyar APC. Gwamnonin Kaduna, Nasarawa, Kogi, Sokoto, Gombe, Legas, da Yobene suka tarbi mataimakin shugaban kasar ayan isarsa birnin Asaba. A ranar 23 ga watan Afril ne gwamna Sheriff Oborevwori ya canja sheka daga PDP zuwa APC.
Ba a ga watan Zulki’ida ba a Najeriya – Fadar sarkin Musulmi

Ba a ga watan Zulki’ida ba a Najeriya – Fadar sarkin Musulmi

Duk Labarai
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar III ta ce ranar Talata ce 1 ga watan Zulki'ida na shekarar Hijira ta 1446. Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jaririn watan ba a ranar Lahadi. A ƙa'idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30. Hakan na nufin yau Litinin 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
Watanni 15 bayan fara biniken Tsaffin Ministocin jin kai, Sadiya Umar Farouk da Betta Edu har yanzu EFCC bata fitar da sakamakon binciken ba

Watanni 15 bayan fara biniken Tsaffin Ministocin jin kai, Sadiya Umar Farouk da Betta Edu har yanzu EFCC bata fitar da sakamakon binciken ba

Duk Labarai
A tsawon watanni 15 da suka gabata, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) bata fitar da cikakken rahoton binciken zargin almundahana da suka shafi tsofaffin Ministocin Harkokin Jinƙai, Gudanar da Bala’o’i da Ci gaban Zamantakewa — Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu. Binciken, wanda ya kuma shafi tsohuwar Shugabar Hukumar Tsarin Tallafin Jama’a ta Ƙasa (NSIPA), Halima Shehu, da wani ɗan kwangila mai suna James Okwete, ya ci gaba da gudana a karkashin jagorancin EFCC, duk da dogon lokaci da ya wuce tun fara shari’ar. Rahotanni sun nuna cewa, sama da naira biliyan 30 (N30bn) ne aka gano an dawo da su daga asusun bankuna kusan 50 da aka alakanta da ma’aikatar lokacin da Edu da Sadiya ke rike da madafun iko, bayan haɗin guiwa tsakanin EFCC da Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran L...
Farashin Buhun shinkafa me girman 50kg ya koma Naira Dubu 58

Farashin Buhun shinkafa me girman 50kg ya koma Naira Dubu 58

Duk Labarai
A yayin da aka fara shigo da shinkafa daga kasashen waje, misali kasar Benin zuwa Najeriya, farashin buhun shinkafa musamman a kauyuka ya koma Naira dubu 58,000. Kungiyar S&P Global ce ta fitar da wadannan bayanai inda tace farashin shinkafar a yankin Afrika ta yamma yayi faduwar da ba'a taba ganin irin ta ba tun shekaru 2 da suka gabata. Hakan na da alaka da cire harajin fitar da shinkafa zuwa kasashen waje da kasar India ta yi, kamar yanda rahoton ya nuna. Farashin shinkafar ya sauka daga Naira Dubu 80 zuwa Naira dubu 58 kan kowane buhu. Rahoton ya kara da cewa, kasar India ta ta kawo shinkafa me yawa yankin na Afrika maso yamma.
Shekarata 10 ina sana’ar sayar da sassan jikin mutane>>Inji Wannan wannan matsafin da aka kama

Shekarata 10 ina sana’ar sayar da sassan jikin mutane>>Inji Wannan wannan matsafin da aka kama

Duk Labarai
An kama wani me sana'ar sayar da sassan jikin dan Adam me suna Gani a yankin Kulanla Odomoola na jihar Ogun. Sojoji na runduna ta 81 ne suka kamashi a yayin da mutane suka rufar masa da duka ana shirin kasheshi. Ya amsa laifinsa inda yace shekara goma kenan yana wannan sana'a. Ya kara da cewa, yakan samu sassan jikin dan Adam ne a makabartu da kuma idan an yadda gawa. Ko yanzu ma da asirinsa ya tonu, an kamashi ne yana shirin kaiwa wani abokin huldarsa sassan jikin dan Adam ne. Me magana da yawun sojin, Lieutenant Colonel Olabisi Olalekan Ayeni, ya tabbatar da kamen inda yace sun mikashi hannun 'yansanda.
DA DUMI DUMI: Mutane Sama da Dubu ɗaya (1,000) Sun karɓi Addinin Musulunci a ƙasar Cameron da ƙasar Chadi,

DA DUMI DUMI: Mutane Sama da Dubu ɗaya (1,000) Sun karɓi Addinin Musulunci a ƙasar Cameron da ƙasar Chadi,

Duk Labarai
Wadannan Jama'a Da Kuke Gani Cikin Hotuna Kadan Ne daga Cikin Mutane Dubu 'Daya(1000) Da Suka Kar6i Addinin Musulunci 'Karkashin Da'awar MAULANMU SHEHU TAHIRU(R.A), Wanda Ya Samu Wakilcin 'Dansa; KHADIMUL - FAIDHA (Alh. Ibrahim Bn Maulana Sheikh), Wadannan Mutane Suna Zaune/Rayuwa Ne Tsakanin Jamhuriyar Kamaru Da Chadi. Allah Ya 'Kara Tabbatar Da Duga-Dugan Wadannan Bayin Allah Akan Wannan Tafarkin Na Musulunci, ku Tayamu Sharing zuwa group group domin Al'ummar Musulmai Su gani Suji daɗi
DA ƊUMI-ƊUMI: Wani Shùĝabàɲ Cøci Ya Ķarbì Mùsulunci A Masaĺlacìn Kùndila Dake Kano A Daĺilin Da’àwaŕ Baban Chìnedu

DA ƊUMI-ƊUMI: Wani Shùĝabàɲ Cøci Ya Ķarbì Mùsulunci A Masaĺlacìn Kùndila Dake Kano A Daĺilin Da’àwaŕ Baban Chìnedu

Duk Labarai
DA ƊUMI-ƊUMI: Wani Shùĝabàɲ Cøci Ya Ķarbì Mùsulunci A Masaĺlacìn Kùndila Dake Kano A Daĺilin Da'àwaŕ Baban Chìnedu. Wani Shugaban coci ya karbi addinin musulunci a Kano ALLHAMDULILLAH ALLAHU AKBAR WANI SHUGABAN COCHI YA KARBI ADDININ MUSULUNCI A YAU LAHADI A MASALLACIN JAMI'UR RAHAMA KUNDILA KANO. A yau Lahadi Wanda tayi dai dai da 27- April 2025, Musulunci ya samu karuwa da Daya daga cikin shugaban Coci wato leader of the church Wanda yasa mu jagoran ci Yusuf Baban chinedu Mai gudanar da Da'awah da Hujjah, a shafukan Sada zumunta. inda shi leader of the church din bayan sun samu zama da Baban chinedu ya gamsu da Addinin musulunci yakuma bukaci yanaso yayiwa Shechk MUHAMMAD AUWAL (Director Zaitun Da'awah institute) tambayoyi akan Addinin Christianity bayan Kammala tambayoyin s...
Ji Rashin Tsoron Allah: Mun gano ma’aikata 240 da ke karɓar albashi nunki biyu a Kano>>Inji Gwamnatin Jihar

Ji Rashin Tsoron Allah: Mun gano ma’aikata 240 da ke karɓar albashi nunki biyu a Kano>>Inji Gwamnatin Jihar

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bankado wasu kura-kurai a tsarin biyan albashin ma’aikata, inda ta bayyana cewa ma’aikata 240 ne ke karbar albashi biyu. Dakta Sulaiman Wali Sani, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin ma’aikata kuma shugaban kwamitin gudanarwa na jiha da aka dorawa alhakin tsaftace albashin gwamnatin jihar, ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai a nan Kano. Dakta Sani, wanda ya wakilci sakataren gwamnatin jihar (SSG) a yayin taron, ya ce wannan bincike na daga cikin kokarin da ake yi na tsaftace ma’aikatan jihar. Kazali ka Ya ce binciken ya biyo bayan wani aikin tantance ma’aikata da kuma ayyukan kwamitoci guda biyu - daya kan batun biyan albashin kananan hukumomi da aka kafa domin tantance tsarin albashi. Ya kara da cewa ma’aikata 1,335 su ma s...
Na yafe wa waɗanda su ka mini ƙage da sharri da ƙazafi – Amarya Aisha Humaira

Na yafe wa waɗanda su ka mini ƙage da sharri da ƙazafi – Amarya Aisha Humaira

Duk Labarai
Aisha Humaira, amaryar kuma abokiyar aikin mawaki Dauda Kahutu Rarara ta magantu a karon farko bayan auren su, wanda aka daura a Maiduguri a ranar Juma'a. A wani faifen bidiyo da ya karade kafafen sadarwa, an gano Aisha Humaira sanye da hijabi tana kira ga waɗanda ke fadar maganganu na ƙage akan alaƙar ta da Rarara da su dena kuma ta yafe musu. "Ina masharranta, ina munafukai, ina masu shedar zir, ko kuma wani ya ji labari ha je ya dorar? Ina masu zama su ce wance ta yi kaza, wane ya yi kaza, an yi kaza, an yi kaza kuma bayan duk basu gani ba ba su ji ba. "Ina wadanda su ka zage ni ban sani ba, ina waɗanda su ka zage ni na sani? Ina magulmata masu kaiwa da kawowa, masu cewa Aisha Humaira ta yi kaza, ta yi kaza? "Duk wanda ya zage ni a bayan ido na da wanda ya zage ni d gaban wa...