Jadawalin Sojoji 43 da IBB ya kàshè wanda suka yi yunkurin yi masa juyin mulki
Tarihin Yunkurin Juyin Mulkin Ďa Janar Babangida Ya Tsàĺĺakè Rijiya Da Baya A Shekarar 1990,
..da kuma wasu jihohin Aŕewa guda biýar da aka sanar da ķorar su daga Nijeriya a lokacin juyin mulkin
Daga Muhammad Cisse
A rana mai kamar ta yau ne 22 ga watan Afrilu 1990. An yi yunkurin juyin mulkin a Nijeriya, wani yunkuri ne na juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijeriya a ranar 22 ga Afrilun 1990, a lokacin da wani bangare na hafsoshin Sojin kasar, karkashin jagorancin Manjo Gideon Orkar, suka yi yunkurin hambarar da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida.
Dakarun Sojoji masu yunkurin juyin mulkin sun kwace gidan rediyon FRCN da ofisoshin sojoji daban-daban a kewayen Legas, ciki har da hedkwatar sojoji da gidan shugaban kasa a Barrack Dodan. Babangida yana wurin lokacin da aka kai hari a...








