Saturday, December 13
Shadow
Darajar Naira ta fadi a kasuwar Chanji

Darajar Naira ta fadi a kasuwar Chanji

Duk Labarai
Naira ta samu tasgaro a kasuwar Chanji inda ta fadi zuwa N1,510 akan kowace dala a jiya. Wanan farashi yayi sama idan aka kwatanta da yanda aka kulle kasuwar a makon da ya gabata inda Nairar ke akan farashin N1,505. Saidai a kasuwar Gwamnati Nairar tashi ta yi inda aka sayi dala akan N1,499. Za'a iya fahimtar hakan idan aka yi la'akari da farashin da aka kulle kasuwar a makon da ya gabata na N1,500 akan kowace dala.
Hotuna: Ɗan gidan shugaban shugaban kasa, Seyi Tinubu, ya gudanar da shan ruwa tare da yan siyasa da sauran al’umma a jihar Kano

Hotuna: Ɗan gidan shugaban shugaban kasa, Seyi Tinubu, ya gudanar da shan ruwa tare da yan siyasa da sauran al’umma a jihar Kano

Duk Labarai
Ɗan gidan shugaban shugaban kasar Najeriya Seyi Tinubu, ya gabatar da shan ruwa tare da yan siyasa da sauran al'umma a jihar Kano. Cikin wadanda suka halarci taron shan ruwan da Seyi Tinubu, ya shirya akwai yan jam'iyyar NNPP mai adawa da APC. Shima shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano Hashimu Dungurawa, ya halarci wajen shan ruwan.
Mata a jihar Bayelsa sun fito zanga-zanga inda suka ce Sanata Natasha Akpoti ta janye ‘sharrin’ da tawa Sanata Godswill Akpabio

Mata a jihar Bayelsa sun fito zanga-zanga inda suka ce Sanata Natasha Akpoti ta janye ‘sharrin’ da tawa Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Wata kungiyar mata daga yankin Kudu maso kudu a jihar Bayelsa ta fito zanga-zanga akan rikicin sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio. Kungiyar matan tace kada Sanata Natasha Akpoti ta zubarwa da Sanata Godswill Akpabio mutuncinsa da ya dade yana karewa. Sun yi Allah wadai da halinta inda suka ce ba irin halin matan Najeriya bane, kamar yanda daya daga cikin matan me suna Hon. Ebiere Akpobasa ta bayyana.
Babban Dansandan Najeriya da aka yi Gàrkùwà dashi a Abuja ya kubuta

Babban Dansandan Najeriya da aka yi Gàrkùwà dashi a Abuja ya kubuta

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce jami'inta da aka bayar da rahotonnin cewa an sace ya koma gida tuni. Da take tabbatar wa da BBC ta wayar tarho, kakakin rundunar Josephine Addeh ta ce da ma ba wani mummunan abu ne ya faru da Sufuritanda Modestus Ojiebe ba. "Motarsa ce ta samu matsala kawai a kan hanya, kuma gaba ɗaya abin da ya faru bai fi 'yan awanni ba ya kuɓuta kuma ya koma gida," in ji ta. Tun da farko was kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa motar ɗansandan ce ta samu matsala a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ake zargin masu garkuwa ne suka yi awon gaba da shi.
Tinubu ya amince da kasafin kammala titin Abuja-Kano cikin wata 12

Tinubu ya amince da kasafin kammala titin Abuja-Kano cikin wata 12

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin wata 12. Mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya, Sunday Dare, ya ce a yau Litinin shugaban ya amince bayar da umarnin. "Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kammala wuraren da ba a gama ba a kan titin Abuja-Kaduna, da na Kaduna-Zaria cikin wata 12," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na dandalin X. Ya ƙara da cewa "wannan titi ne mai muhimmanci ne a kodayaushe". A watan Janairu gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da bai wa wani sabon kamfani ƙarashen aikin titin bayan ta ƙwace kwangilarsa daga hannun Julius Berger.
An mai daurin shekaru 14 saboda ya cire kwandam ba tare da budurwarsa ta sani ba yayin da suke jima’i

An mai daurin shekaru 14 saboda ya cire kwandam ba tare da budurwarsa ta sani ba yayin da suke jima’i

Duk Labarai
An daure wani direban babbar mota tsawon shekaru 14 saboda ya cire kwandam yayin da yake jima'i da budurwarsa ba tare da ta sani ba. Wannan mutumi me suna Laurence Rafter, dan kimanin ahekaru 43, ya hadu da wadda yawa wannan laifi me shekaru 32 a wata kafar sadarwa ta yanar gizo ne. Saidai ya bata sunan karya da Address din karya sannan yace mata yana da katon gidan Alfarma. Hakanan sun hadu inda suka yi jima'i amma kamin su fara ta gaya masa cewa yasa kwandam, kuma ya yadda ashe suna cikin yi ya cire bata sani ba. Bayan sun rabu ya ce mata yana dauke da cutar kan jamau amma daga baya aka gane karya yake kawai dan ya bata tsorone, mutumin dake zaune a north London an daureshi shawon shekaru 14 bayan samunsa da laifi.
Kamfanin mai na NNPCL ya rage farashin litar man fetur zuwa Naira 860.

Kamfanin mai na NNPCL ya rage farashin litar man fetur zuwa Naira 860.

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa NNPCL, ya rage farashin litar mai daga naira 920, zuwa naira 860. An samu wannan cigaba a daidai lokacin da ake samun gasa tsakanin manyan yan kasuwar mai dangane da farashin fetur, wanda a makon daya gabata matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man daga naira 890 zuwa naira 825. Haka zalika hawa da saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya na taimakawa wajen samun hawa da saukar farashin.
Kungiyar dalibai ta kasa NANS zata yi zanga-zangar kalubalantar rufe Makarantun Boko a wasu jihohin arewa saboda Azumin Ramadan.

Kungiyar dalibai ta kasa NANS zata yi zanga-zangar kalubalantar rufe Makarantun Boko a wasu jihohin arewa saboda Azumin Ramadan.

Duk Labarai
Kungiyar dalibai ta kasa NANS zata yi zanga-zangar kalubalantar rufe Makarantun Boko a wasu jihohin arewa saboda Azumin Ramadan. Kungiyar tace zata yi zanga-zangar ce in har jihohin Kano, Bauchi da Kebbi da Katsina basu janye umarnin rufe Makarantun da suka yi ba. Itama kungiyar Kristocin Najeriya ta kalubalanci rufe Makarantun. Wadannan jihohi sun bayar da hutun ne don saukakawa al'umma musamman Malamai wahalhalun Azumin.
An yiwa wannan faston daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa yarinya me shekaru 13 fyàdè

An yiwa wannan faston daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa yarinya me shekaru 13 fyàdè

Duk Labarai
Kotu dake za zama a jihar Ekiti a ranar Litinin dinnan ta daure wani Fasto me sunan Adeleye Akingbaso da shekaru 47 bisa laifin yiwa yarinya me shekaru 13 fyade. Wanda ake zargi din abokin mahaifiyar yarinyar da yawa fyadene. da take bayar da labarin yanda lamarin ya faru tace Adeleye yakan kwana a gidansu, tace ranar da abin zai faru mahaifiyarta tana aikin dare ne. Tace tana kwance ya tashe ta yace wai ta yi fitsarin kwance tace abin ya bata mamaki, nan dai ya ciro wani mai ya shafa mata a gabanta. Tace daga nan bata san abinda ya faru ba da ta tashi ta ga an yi mata fyade tace ya gargade ta da cewa idan ta fada zai kasheta. Tace a rana ta biyu ya isketa a dakin dafa abinci shima mahaifiyarta bata nan inda yace mata yana son kammala abinda ya fara saidai anan ta ki yadda i...