Monday, December 15
Shadow
Da Duminsa: An dakatar da sanata Natasha Akpoti daga ayyukan majalisa na tsawon watanni 6, an dakatar da Albashinta an kuma janye jami’an tsaron dake bata kariya saboda karya dokar majalisa

Da Duminsa: An dakatar da sanata Natasha Akpoti daga ayyukan majalisa na tsawon watanni 6, an dakatar da Albashinta an kuma janye jami’an tsaron dake bata kariya saboda karya dokar majalisa

Duk Labarai
A zaman majalisar tarayya na yau, Alhamis, majalisar ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6. Tun farko dai shugaban kwamitin ladaftarwa na majalisar, Sanata Neda Imasuen ne ya bayar da shawarar dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan a dakatar da albashinta da kuma janye jami'an tsaron dake bata kariya. Yace ya kamata a dauki wannan mataki ne saboda sanata Sanata Natasha Akpoti ta karya dokokin majalisar sannan an gayyaceta zuwa gaban kwamitin ladaftarwa saidai ta ki amsa gayyatar. A karshe dai majalisar ta amince da dakatar da sanata Sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 sannan kuma jami'an tsaro sun tasa keyarta zuwa waje. Saidai kamin ta fita tace wannan rashin adalcin ba zai dore ba. kalli Bidiyon anan
Har Majalisa Sanata Natasha Akpoti ta zo mana da Mijinta suka sumbaci juna, su rasa inda zasu je su yi hakan sai a gaban mu, Tana zargin Sanata Godswill Akpabio da nemanta ne kawai dan daukar hankalin mutane>>Inji Majalisar Dattijai

Har Majalisa Sanata Natasha Akpoti ta zo mana da Mijinta suka sumbaci juna, su rasa inda zasu je su yi hakan sai a gaban mu, Tana zargin Sanata Godswill Akpabio da nemanta ne kawai dan daukar hankalin mutane>>Inji Majalisar Dattijai

Duk Labarai
Majalisar dattijai ta bayyana cewa, Sanata Natasha Akpoti ta zargi kakakin majalisar da neman yin lalata da itane kawai dan ta dauki hankulan nmutane. Kakakin majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana haka a hirar da kafar ChannelsTV ta yi dashi. Yace har kofar majalisa Sanata Natasha Akpoti ta je ta yi kiss ita da mijinta. Yace ba yace hakan ya sabawa doka bane amma ai ana barin halas dan kunya dan kuwa hakan ya sabawa al'ada da dabi'ar mutanen kasarnan. _Yace Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata ne kawai dan ta dauki hankalin mutane.
Labari me Dadi: Za’a sake rage farashin man fetur

Labari me Dadi: Za’a sake rage farashin man fetur

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar farashin man fetur zai sake sauka saboda farashin danyen man fetur din wanda daga cikinsa ake fitar da man fetur din yana ci gaba da sauka. Hakan zai kuma kara tabbata ne muddin aka ci gaba da samun karuwar karfin kudin Naira. Farashin danyen mai ya fadi ne saboda sanarwar da kungiyar OPEC ta fitar cewa zata kara yawan man fetur din da take hakowa
Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà’àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà’àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Duk Labarai
Najeriya ce ta zo matsayi na 6 a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan ta'addanci a Duniya a shekarar 2025. A shekarun 2023 da 2024 Najeriya tana matsayi na 8 ne. Kasar Burkina Faso ce ta zo a matsayi na farko sai kuma kasar Pakistan na biye mata baya inda kasar Syria ta zo ta 3. Mali ce ta 4 sai kasar Nijar ta 5 sai Najeriya ta zo ta 6. Hakanan rahoton yace an samu yawan mutanen da aka kashe ta sanadiyyar ta'addanci a Najeriya wanda yawansu ya kai mutane 565 jimulla.
An sako daliban jami’an da aka yi gàrkùwà dasu a Makurdi

An sako daliban jami’an da aka yi gàrkùwà dasu a Makurdi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, daliban jami'ar University of Agriculture Makurdi ta jihar Benue da aka yi garkuwa dasu an sakosu. Garkuwa da daliban ya jefa makarantar cikin yanayin damuwa wanda sai da yasa aka kulle makarantar har na tsawon mako guda. https://www.youtube.com/watch?v=I2vvoBY9v7E?si=3IqJB8_RA4UOnFlq Sako daliban yasa an barke da murna a makarantar. kalli Bidiyon lamarin a nan
Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar ta tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman a faɗin jihar. Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ftitar, ta ce tallafin - wanda ya ƙunshi rabon kuɗi - zai shafi masu buƙata ta musamman duka ƙananan hukumomin jihar. Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce tallafin zai shafi cibiyoyi 27 na masu buƙata ta musamman a fadin jihar. Gwamnan kuma yi kira ga waɗanda za su amfana da tallafin su bayar da haɗin kai domin kauce wa turmutsitsi a wajen raba tallafin
Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin Natasha

Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin Natasha

Duk Labarai
Kwamitin ɗa'a da ladabtarwa da sauraron ƙorafin jama'a na majalisar dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita. Kwamitin ya bayyana ƙorafin da cewa ''ya zo gaban kwamitin a mace'', saboda rashin bin ƙa'ida wajen shigar da shi. A yayin zaman sauraron ƙorafin, shugaban kwamitin Sanata Neda Imasuen, ya karanto doka ta 40 cikin dokokin majalisar dattijai, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha ta sanya hannu kan ƙorafin da kanta maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya lalace. Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su. Tuni d...
Mai Ɗaukar Hoton Da Ya Lashe Kambun Bajinta Na (Guinness World Record) Sa’idu Abdulrahman Ya Gana Da Captin Ahmed Musa

Mai Ɗaukar Hoton Da Ya Lashe Kambun Bajinta Na (Guinness World Record) Sa’idu Abdulrahman Ya Gana Da Captin Ahmed Musa

Duk Labarai
Matashin mai sana’ar ɗaukan hoto ɗan asalin Jihar Yobe, wanda ya samu nasarar lashe kambun bajinta na Duniya kan sana’arsa, (Guinness World Record In Photography), Sa’idu Abdulrahman, ya gana da fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Captin Ahmed Musa MON. Ganawar wadda ta gudana a jiya, matashin ya gabatar wa Captin ɗin kundin nasa na bajinta da ya samu bayan da ya yi nasarar ɗaukan hotuna 897 cikin mintuna 60. Sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da rawar da za su taka wajen tallafa wa masu tasowa cikin ayyukan fasaha a Najeriya ta yadda su ma za su samu damar bayyanawa Duniya irin tasu ƙwarewar. Matashin ya yaba da yadda ya samu Ahmed Musa a matsayin mutum mai nasara a Duniyar ƙwallon ƙafa wanda kuma a kullum yake ƙoƙarin tallafawa masu tasowa da...
Ba zamu saurareki ba, Majalisar Dattijai ta yi watsi da korafin Sanata Natasha Akpoti akan Sanata Godswill Akpabio  na zargin ya nemeta da lalata

Ba zamu saurareki ba, Majalisar Dattijai ta yi watsi da korafin Sanata Natasha Akpoti akan Sanata Godswill Akpabio na zargin ya nemeta da lalata

Duk Labarai
Kwamitin da'a na majalisar Dattijai yayi watsi da korafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar gabansa inda take zargin cewa, kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata. Sanata Natasha Akpoti a zaman majalisar a jiya, Laraba ta gabatar da korafi a hukumance gaban majalisar inda kakakin majalisar Godswill Akpabio wanda shine take zargi da neman yin lalata da ita yace mata ta mika takardar korafin inda a karshe yace a kai takardar gaban kwamitin da'a na majalisar. Saidai a zaman Kwamitin da'a na majalisar, shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen ya bayyana cewa ba zasu saurari korafin na Sanata Natasha Akpoti ba saboda maganar na kotu. Yace a dokar majalisa, duk maganar dake kotu, kwamtinsu ba zai tattaunata ba. Saidai kamin a tashi daga zaman majalisar, Sanata ...