Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi yayi bayani dalla-dalla dalilin da yasa yake son su hada kai dan kayar da Shugaba Tinubu
Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan hamayya a ƙasar domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.
Amaechi - wanda ɗan jam'iyyar APC ne - ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira ƙuncin rayuwa da ƙasar ne ciki.
A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.
Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.
Kalaman Amaechi na zuwa ƙasa da wata ɗaya bayan jagororin jam'iyyar APC sun amince da Bola Tinubu a matsayin "ɗan takara ɗaya tilo" a zaɓen 2027.
Sai dai tsohon ministan ya ce har yanzu yanan nan a jam'iyyar APC, kuma ''bai zama dole sai ka goyi bayan gwamnati ba, don kawai kana APC.
''Idan gwamnati t...








