‘Yadda tsohon mijina ya sake ni bayan ƙwace min kwangilar biliyoyin naira’
Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu, wanda ta bayyana cewa ya zo mata a wani yanayi na ba-zata, kamar almara.
Mansurah ta ce ita aure ta yi na soyayya, domin a cewarta, "so makaho nr", amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba.
Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda BBC ta tattauna da ita tare da tsohuwar jaruma a masana'antar, Fati Mohammad kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure.
Da take shimfiɗa, Fati Mohammad ta ce mutane ne suke musu gurguwar fahimta, domin "shi aure ai yana da rai, kuma idan Allah ya kawo ƙarshensa, dole sai ya ƙare. Mutane da yawa aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, sai ba za a ji ba," in ji ta.
Ta ce yawanci...








