Tuesday, December 16
Shadow
Hukumar ‘yansandan Abuja ta ce tsohon shugaban hukumar Immigration David Shikfu Parradangba garkuwa aka yi dashi ba, ya mutu ne a dakin Otal bayan sun shiga shi da wata mata

Hukumar ‘yansandan Abuja ta ce tsohon shugaban hukumar Immigration David Shikfu Parradangba garkuwa aka yi dashi ba, ya mutu ne a dakin Otal bayan sun shiga shi da wata mata

Duk Labarai
A dazu ne dai muka samu rahoto daga jaridar The National cewa tsohon shugaban hukumar shigi da fici, Immigration me suna David Shikfu Parradang an yi garkuwa dashi kuma an kasheshi. Saidai sabbin bayanai da hukumar 'yansandan Abuja suka fitar sun ce ba a yi garkuwa dashi ba. Bayanan sun ce David Shikfu Parradang ya je otal din Joy House Hotel dake Area 3 inda ya biya kudin daki na kwana daya dubu 22. Ya shiga otal dinne da misalin karfe 12 na yamma da bakar mota kirar Mercedes Benz. Jim kadan bayan shigarsa sai ya baiwa me karbar baki dake aiki a otal din umarnin ta shigo masa sa wata bakuwa da yayi. Da misalin karfe 4 na yamma bakuwar ta fita ta tafi abinta. Da Misalin karfe 4 na dare sai ga abokinsa soja yana nemansa, ko da suka shiga dakin sai suka tarar dashi a zaune ka...
Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba>>Inji Dan Jarida Sam Omatseye

Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba>>Inji Dan Jarida Sam Omatseye

Duk Labarai
Dan Jarida, Sam Omatseye ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai so Tinubu ya zama ahugaban kasa ba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace tun a shekarar farko aka so a samu matsala tsakanin Buhari da Tinubu amma saboda Buharin na tunanin zarcewa, shiyasa ba'a yi fadan ba. Yace cire tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole daga mukamin shugaban APC na daya daga cikin dabarun hana Bola Ahmad Tinubu zama shugaban kasa da Gwamnatin Buhari ta bijiro dasu. Yace hakanan akwai wasu gwamnoni ma da basu so Tinubu ya zama shugaban kasa ba.
Da Duminsa: Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na shirin soke dokar data halasta auren jinsi na ‘yan Luwadi da Magido a kasar Amurka

Da Duminsa: Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na shirin soke dokar data halasta auren jinsi na ‘yan Luwadi da Magido a kasar Amurka

Duk Labarai
'Yan Jam'iyyar Republican dake mulki a kasar Amurka a majalisar kasar na shirin soke dokar amincewa da auren jinsi na 'yan Luwadi da madigo a kasar. A watan Janairu ne aka fara samun wanna kira daga 'yan majalisar jihar Idaho inda suka nemi kotun kolin kasar data sake duba dokar da ta yi a shekarar 2015 data halasta auren jinsi. Bayan su, an sake samun wasu 'yan majalisar daga jihohin Michigan, Montana, North Dakota da South Dakota suma suna kiran kotun kolin data sake duba wannan hukunci nata. Dama dai tun a ranar da aka bayyana cewa, Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasar Amurka aka rika samun 'yan Luwadi da madigo da yawa na kuka suna cewa sun shiga uku inda wasu suka bar kasar ta Amurka saboda sun san shugaban kasar, Donald Trump baya shiri dasu. Tuni dai shugaba Tru...
Da Duminsa: Masu Gàrkùwà da mutane sun kkàshè tsohon shugaban Hukumar shige da fici ta Najeriya

Da Duminsa: Masu Gàrkùwà da mutane sun kkàshè tsohon shugaban Hukumar shige da fici ta Najeriya

Duk Labarai
Masu garkuwa da mutane sun kashe tsohon shugaban hukumar kula da shige da fici ta Najeriya, watau Nigerian Immigration me suna David Shikfu Parradang. Rahoton theNation yace an yi garkuwa dashine a daren jiya a abuja. Ya shafe shekaru 30 yana aiki da hukumar inda yayi aiki a jihohin Kano, Lagos, Kwara, Enugu da babban birnin tarayya Abuja.
Jahilci da sakarci ne yasa Gwamnonin Arewa suka bayar da hutun Azumin watan Ramadana, idan na zama shugaban kasa ba zan yadda da wannan ba>>Sowore

Jahilci da sakarci ne yasa Gwamnonin Arewa suka bayar da hutun Azumin watan Ramadana, idan na zama shugaban kasa ba zan yadda da wannan ba>>Sowore

Duk Labarai
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma me ikirarin fafutukar 'yancin dan Adam, Omoyele Sowore ya bayyana cewa Gwamnonin jihohin Bauchi, da Katsina, da Kano, da Kebbi da suka bayar da hutun makaranta na Azumin watan Ramadana Jahilaine kuma sakarkarune. Yace Makka da ake zuwa yin hajji basu kulle makarantun su saboda Azumin watan Ramadana ba wanda hakan yake nuna cewa su wadannan gwamnoni sun jahilci addinin. Yace idan ya zama shugaban kasa, ba zai bari wani gwamna yayi irin wannan abin ba. Sowore ya kara da cewa, cikin makarantun da aka kulle hadda na islamiya inda yace idan makarantun Islamiya na kulle ta yaya yara zasu koyi Qur'ani?
Ƴansanda sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa a Bauchi

Ƴansanda sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa a Bauchi

Duk Labarai
Rundunar ƴansanda a jihar Bauchi ta ce ta kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa. Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan jihar, CSP Ahmed Wakili ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Fabrairu a wata unguwa mai suna Abujan Kwata. Ya ce ana zargin matashin mai suna Safiyanu Dalhatu ɗan shekara 20, da amfani da taɓarya wajen lakaɗawa mahaifiyarsa duka har ta kai ga mutuwarta. "Matashin ya yi wa mahaifiyar tasa mai suna Salama Abdullahi mai shekara 40 munanan raunuka a hannu kuma ya yi mata jina-jina abin da ya kai ga mutuwarta," in ji sanarwar ƴansandan. CSP Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da faru ne suka aika tawagar jami'ansu zuwa anguwar, inda suka ɗauki mahaifiyar matashin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa - inda wani likita y...