Muzanta Naira: Kotu ta yanke wa wani dan Tiktok hukunci a Kaduna
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC reshen Kaduna ta samu nasara bayan da kotu ta yanke hukunci ga wani a mai amfani da shafukan Tiktok da Instagram, Muhammad Kabir.
An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Mai Shari’a R.M. Aikawa na Babban Kotun Tarayya dake zamanta a Kaduna, bisa laifin wulakanta kudin Naira.
Shugaban sashen hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na Tiktok da Instagram (@youngcee0066), yana watsar da takardun kudi na Naira a ƙasa, yana taka su da kafa, tare da furta wasu kalmomi cikin harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda aka san yana zaune.
An kama shi bisa karya dokar Babban Bankin Najer...








