Tuesday, April 7
Shadow
YANZU-YANZU: ‘Yan Majalisar Tarayya Biyu Daga Jihar Kano, Honarabul Kabir Rurum Da Abdullahi Sani Sun Sanar Da Ficewar Su Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC A Hukumance

YANZU-YANZU: ‘Yan Majalisar Tarayya Biyu Daga Jihar Kano, Honarabul Kabir Rurum Da Abdullahi Sani Sun Sanar Da Ficewar Su Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa APC A Hukumance

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} 'Yan Majalisar Tarayya Biyu Daga Jihar Kano, Honarabul Kabir Rurum Da Abdullahi Sani Sun Sanar Da Ficewar Su Daga Jam'iyyar NNPP Zuwa APC A Hukumance
Masu Ikirarin Jìhàdì sun shiga Uku, An fito da rundunar sojojin da basu taba yin rashin nasara ba an kaisu Arewa Maso gabas, sojojin kansu sai murna suke

Masu Ikirarin Jìhàdì sun shiga Uku, An fito da rundunar sojojin da basu taba yin rashin nasara ba an kaisu Arewa Maso gabas, sojojin kansu sai murna suke

Duk Labarai
Rahotanni da hutudole ke samu na cewa Rundunar sojojin Najeriya ta fito da daya daga cikin rundunar sojojin ta mafi karfi da bayar da sakamakon da ake so wajan yaki inda aka kaisu Arewa maso gabas. Sunan rundunar shine 134 Special Forces Battalion Wanda a baya sun yi yaki tare da rundunar sojoji da Najeriya ta dauoo haya daga kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2013 suka yaki Boko haram,. Rundunar ta kuma taba yaki a Kangarwa dake jihar ta Borno a lokacin da aka yi fama da 'yan Bindiga wadanda ba B0k0 Hàràm ba kuma ta gama dasu. Sannan a shekarar 2019, sun kuma yaki B0k0 Hàràm inda kuma suka yi nasara. Hakanan a shekarar 2022 an kai rundunar jihar Kaduna inda ta yaki 'yan Bindiga a camma kuma ta yi nasara. Sojojin dake Arewa maso gabas rahotanni sun bayyana cewa sai murna suke d...
Ji yanda dan majalisa yawa abokan aikinsa tonon silili, yace yanzu kowane Sanata ana bashi Naira Biliyan 2 dan majalisar wakilai kuma Naira Biliyan 1 dan suwa mutanen mazabarsu aiki tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur

Ji yanda dan majalisa yawa abokan aikinsa tonon silili, yace yanzu kowane Sanata ana bashi Naira Biliyan 2 dan majalisar wakilai kuma Naira Biliyan 1 dan suwa mutanen mazabarsu aiki tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur

Duk Labarai
Wani dan majalisar tarayyar Najeriya yawa abokan aikinsa Tonon Silili inda yace babu dan majalisar dake samun kasa da Naira Biliyan 2 na yiwa mazabarsa aiki a majalisar dattijai. Yace hakanan a bangaren 'yan majalisar wakilai, babu wanda ke samun kasa da Naira Biliyan 1 shima dan yiwa 'yan mazabarsa aiki. Ya bayyana hakane a jihar Osun, kamar yanda jaridar Sahara reporters ta ruwaito. Saidai ba'a bayyana sunansa ba, yace 'yan majalisar sun samu karin kudinne bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur. Hakanan yace suma Gwamnoni an kara musu kudaden da ake basu na yiwa jihohinsu aiki. Wannan dai ya zowa mutane da mamaki ganin yanda 'yan majalisar ke kukan suma suna cikin wani hali a yayin da 'yan Najeriya ke kokawa da tsadar rayuwa.
Sojojin Najeriya sun tsere daga sansaninsu a Gubio dake Jihar Borno bayan da masu ikirarin Jìhàdì suka durfafesu zasu kai musu hari

Sojojin Najeriya sun tsere daga sansaninsu a Gubio dake Jihar Borno bayan da masu ikirarin Jìhàdì suka durfafesu zasu kai musu hari

Duk Labarai
Rahotanni da hutudole ke samu daga garin Gubio na jihar Borno na cewa, Kungiyar ÌSWÀP ta yi yunkurin kaiwa garin hari ranar Litinin amma Sojoji suka dakile harin. Saidai Ranar Talata, Kungiyar ta sake durfafar garin inda ta nufi sansanin sojojin da afka mai da yaki. Saidai mutanen garin na sanar da sojojin, a wannan karin sai aojojin suka tsere. Rahoton yace ko da kungiyar ta ji sojojin sun tsere sai ta fasa kai harin suka juya. An ce dai daga baya sojojin sun koma sansanin nasu.
In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati

In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati

Duk Labarai
Tsohon shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban kungiyar Kwadago ta NLC ne, watau Adams Oshiomhole ya nemi tsohon kakakin shugaban kasa, Reuben Abati da ya fito su daku idan ya isa. Ya bayyana hakanne a ganawarsa da gidan Talabijin na Channels TV. Yace hakane bayan da Abati a wata hira da aka yi dashi a Arise TV ya ce shin ko Ifeanyi Okowa ya tambayi Oshiomhole an yafe masa zunubansa kamin komawa APC? A baya dai lokacin yana shugaban APC, Adams Oshiomhole ya taba cewa, duk laifin mutum idan ya shiga APC an yafe masa. Saidai yanzu yace wannan magana da Abati yayi bata dace ba, shi a matsayinsa na Sanata menene hadinsa da binciken me laifi? Sannan yace shin ko Abati yana jin haushin kamun da EFCC suka masa ne bayan saukar Jonathan daga Mulki, yac...
An sake Kai wani mummunan hari jihar Filato

An sake Kai wani mummunan hari jihar Filato

Duk Labarai
An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da fiye da shanu 100 a jerin hare-haren da aka kai kan makiyaya a ƙauyuka biyu da ke cikin Kananan Hukumomin Jos na Kudu da Jos na Arewa na Jihar Filato. Hare-haren, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai ta hanyar buɗe wuta kan makiyayan da ke kiwo, sun sake jaddada yadda tsaro ya taɓarɓare a yankunan da ke fama da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, rikice-rikicen da a kullum ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren. Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin farfagand...