Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya bayar da Umarnin a dauki matasa 130,000 aiki dan su shiga daji su gama da ‘yan Bìndìgà da ake fama dasu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron dazuka a ƙasar baki ɗaya, domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Najeriya.
A karkashin wannan shiri, za a ɗauki sama da masu tsaro 130,000 da za su kasance da kayan yaƙi da horo na musamman domin kare dazukan ƙasar guda 1,129.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya wallafa ta a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce "Wannan mataki na tsaro an amince da shi ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.'
"A cikin wannan tsari, shugaba Tinubu ya umurci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 domin zama masu tsaron daji, dangane da ƙa...








