Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci
Zargin wulakanta Naira: Kotu ta saka ranar da za ta yankewa Murja hukunci.
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage ranar yanke hukunci kan shahararriyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, har zuwa ranar 20 ga watan Mayu, bayan da masu gabatar da kara su ka nemi izini don gyara tuhumar da a ke yi mata.
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa hukumar EFCC ce ta gurfanar da Murja da tuhuma daya tak kan zargin cin zarafin Naira.
An ga Murja a wani faifen bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta tana watsar da kudi har Naira 400,000 tare da rawa a lokacin wani biki da aka gudanar a otal din Tahir Guest Palace a watan Disamba na shekarar 2024.
Tuni dai wanda ake tuhumar ta amsa laifin da ake zarginta da shi.
A zaman kotun na ranar Talata da aka tsara domin yanke hukunci, lauyan EFCC...








