Tuesday, December 16
Shadow
Hukumomi a jihar Anambra zasu fara kamen mata masu shigar banza

Hukumomi a jihar Anambra zasu fara kamen mata masu shigar banza

Duk Labarai
Wata hukumar tsaro a jihar Anambra ta bayyana aniyarta na fara kamen mata dake shigar banza wanda ke yawo babu rigar nono ko dan kamfai a cikin mutane. An nadi sautin sanarwar inda aka rika yayatashi a kafafen sadarwa. Hukumar tsaron ta bayyana cewa, Gwamnan jihar, Chukwuma Soludo ne ya bayar da umarnin yin hakan, saidai gwamnatin jihar bata fitar da sanarwa ba game da lamarin. Sanarwar tace mata masu saka dan kamfai kadai suma za'a fara kamasu.
Kalli Hotuna:An tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano

Kalli Hotuna:An tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano

Duk Labarai
'Yan Bijilante sun tsinci gawar jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala Tagarji dake Kano. 'yan Bijilanten sun fita aiki ne da dare inda suka ga kwali a cikin wani rami an ajiye, nan suka budeshi suka ga ashe gawar jariri ne a ciki. Kwamandan Bijilante din, Sulaiman Rabiu ne ya tabbatar da haka inda yace sun tsinci gawar jaririnne da misalin karfe 2 na daren ranar Asabar. Yace sun dauki gawar zuwa ofishinsu inda suka kira me unguwa ya gani kamin daga baya su kai jaririn zuwa ofishin 'yansanda. 'Yansandan sun gaya musu cewa su tafi da gawar zuwa Asibiti dan a dubata inda likitoci suka tabbatar jaririn ya mutu. Sulaiman yace sun yiwa jaririn sallah inda aka binneshi kamar yanda addinin Musulunci ya tanada. Daga baya dai ya jawo hankalin iyaye da su rika saka ido akan 'ya...
Fusatattun Matasa sun Bankawa jami’in NDLEA wuta ya kone kurmus a Kaduna

Fusatattun Matasa sun Bankawa jami’in NDLEA wuta ya kone kurmus a Kaduna

Duk Labarai
Fusatattun matasa a garin Gadan Gayan dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna sun bankawa wani jami'in hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA me suna Aliyu Imran wuta ya kone kurmus. Lamarin ya farune bayan da Aliyu me mukamin Assistant Superintendent of Narcotic 1 tare da abokan aikinsa suka bi wani da ake zargi da safarar kwaya inda ya tsere a mota. Saidai garin gujewa ma'aikatan motar wanda ake zargin ta yi hadari inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 3. Daga nan ne dai Aliyu yayi kokarin kwantar da tarzomar inda anan fusatattun matasa suka dakeshi tare da caka masa wuka. Anan 'yansanda suka daukeshi suka kaishi Asibiti, saidai daga baya matasan sun bishi har asibitin inda suka janyoshi suka banka mai wuta ya kone kurmus. Lamarin ya farune a ranar ...
Kuma Dai: Jirgin saman yakin sojojin Najariya ya kara Kkàshè farar hula 6 a katsina bisa kuskure

Kuma Dai: Jirgin saman yakin sojojin Najariya ya kara Kkàshè farar hula 6 a katsina bisa kuskure

Duk Labarai
Jirgin yakin sojojin Najariya ya kashe farar hula 6 a kauyen Zakka dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina bisa kuskure. Hakan ya farune bayan da wasu 'yan Bindiga suka kai hari ofishin 'yansanda suka kashe 'yansanda 2. Harin ya farune ranar Asabar data gabata inda sojojin suka wurga bama-bamai akan wasu bukkoki dake wajen garin na Zakka. Wasu shaidu 3 sun tabbatar da faruwar lamarin ga majiyarmu. Kamfanin dillancin labaran AFP ya tabbatar da faruwar lamarin.
An Kkàshè Wani tsageran limamin masallaci da ya fito ya bayyana cewa shi dan Luwadi ne

An Kkàshè Wani tsageran limamin masallaci da ya fito ya bayyana cewa shi dan Luwadi ne

Duk Labarai
Wani limamin masallaci a kasar Afrika ta Kudu me suna Moegsien Hendricks ya bakunci lahira bayan da ya yi yunkurin daura auren jinsi. Limamin wanda ya riga ya fito ya bayyanawa Duniya cewa shi dan luwadine ya shahara sosai. Wata yarinya ce wadda itama musulmace amma take son auren 'yar uwarta mace dan yin madigo ta gayyaceshi ya daura mata aure da wadda take so wadda ba musulma bace. An kasheshi ne a garin Bethelsdorp a ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu yayin da ya kai inda zai daura auren. Kakakin 'yansanda na birnin, Captain Sandra Janse van Rensburg ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mutane biyu ne fuskokinsu a rufe suka je da mota kirar Hilux suka kashe limamin. Ta kara da cewa, ba'asan manufarsu ta aikata hakan ba inda tace duk wanda ke da bayani akan maharan ya k...
Tsare-Tsarena sun sa farashin kayan abinci sun sauka fiye da kamin in hau mulki>>Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Tsare-Tsarena sun sa farashin kayan abinci sun sauka fiye da kamin in hau mulki>>Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, farashin kayan abincin ya sauka saboda tsare-tsaren gwamnatinsa. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV. Ya kara da cewa, idan aka kwatanta yanda Najeriya take a yanzu da yanda take kamin shugaba Tinubu ya hau mulki za'a ga banbanci. Ya koka da cewa kasafin kudin Najeriya duka bai wuce dala Biliyan $30 ba sannan ga asibitoci a lalace ga tituna a lalace da sauransu. A karshe dai ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya sauka.
Dansandan Najeriya ya mutu a dakin Otal bayan ya shiga ciki da wata mata

Dansandan Najeriya ya mutu a dakin Otal bayan ya shiga ciki da wata mata

Duk Labarai
An gano gawar wani dansandan Najeriya a dakin otal dake Uzum Estate, Oyeyemi Akute jihar Ogun. Sunan Otal din Super G Royal Hotel sannan sunan dansandan da aka gawarsa, Inspector Haruna Mohammed. Saidai matar da suka shiga dakin otal din da ita ta tsere ba'a san inda ta yi ba. Rahoton jaridar thenation ya bayyana cewa, dansandan ya shiga otal din da matar ranar February 15, 2025 da misalin karfe 1 na dare. Ganin karshe da akawa matar da suka shiga dakin da ita shine da misalin karfe shida na safe inda ta bukaci a bata ruwan sha. Manajar otal din wadda macece ta fara ganin gawar dansandan inda tuni aka tafi da ita ofishin 'yansandan dan gudanar da bincike. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun gano gawar babu wata alamar...
Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam'iyyar APC ba. Ya bayyana hakane a wajan taron Jam'iyyar PDP da aka gudamar a Jiya Asabar inda yace masu ruguguwar komawa APC suna yi ne dan neman na Abinci. Yace ba dan mutane 'yan siyasar suke komawa APC ba inda yace ta yaya zasu rika saurin komawa Jam'iyyar duk da matsin tattalin arzikin da ake fama dashi da kuma rashin iya mulki na Jam'iyyar. Yayi kira ga 'yan Adawa da su hada kai a shekarar 2027 su kawar da Jam'iyyar ta APC daga mulki.
A 2027 ‘yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa>>Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

A 2027 ‘yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa>>Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, a shekarar 2027 'yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa. Ya bayyana hakanne a ranar Asabar a Dandalin Murtala dake Kaduna inda aka yi bikin karbar wasu sabbin 'yan jam'iyyar APC. Yace 'yan Najeriya zasu sabi APC dinne saboda Adalcin data musu. Ya kara da cewa a shekarar 2027 za'a sake zabar Tinubu a matsayin shugaban kasa inda kuma za'a sake zabarsa a matsayin gwamna sannan duka 'yan majalisar wakilai da jihohi ma haka. Yace sabbin 'yan jam'iyyar da suka shigo ba za'a nuna musu wariya ba, zasu samu iko kamar kowane dan Jam'iyyar inda yace kan Jam'iyyar APC a hade yake.
Kiristancin Arewa, Maguzawa, da sauran mutanen Arewa ta tsakiya sunce basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Tinubu

Kiristancin Arewa, Maguzawa, da sauran mutanen Arewa ta tsakiya sunce basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Tinubu

Duk Labarai
Mutanen Arewa ta tsakiya da suka hada da Kiristoci da Maguzawa, da mutanen jihar Jos da sauransu sun bayyana cewa, basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Sun bayyana cewa su a shekarar 2027, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ne zabinsu. Saidai wadannan mutane dake son ballewa dan nuna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, kalilan ne daga cikin mutanen Arewa. Saidai a gefe daya kuma, Mafi yawan 'yan Arewa sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce ba zasu zabeshi ba a zaben 2027. Kungiyoyin fafutuka da yawa daga Arewa sun bayyana cewa ba zasu goyi bayan sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027 ba. Shugaban kungiyar hadaka ta kungiyoyin Arewar, Jamilu Charanchi ya bayyana cewa ...