Saturday, December 20
Shadow
Za a ƙara kuɗin kiran waya a Najeriya – Gwamnatin Najeriya

Za a ƙara kuɗin kiran waya a Najeriya – Gwamnatin Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirin ƙara kuɗin kiran waya da na data, nan ba da jimawa ba. Ministan sadarwar ƙasar, Bosun Tijani ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja. Ya ce hukumar sadarwa ta ƙasar, NCC ce za ta tsara yadda ƙarin zai kasance. Tijani ya ƙara da cewa, “Kafin mu zo da wannan shawara, sai da muka yi la'akari da abubuwa masu yawa na yadda hakan zai taimaka wajen gina ƙasarmu''. “Wasu daga cikin abubuwan sun haɗa da tabbatar da inganta hanyoyin sadarwarmu da inganta kamfanoninmu na cikin gida da tabbatar da ɗorewar kamfanonin kansu''. ''Haka ma kamar yadda muke ganin hauhawar farashin kayayyaki a duniya, su ma kamfannonin sadarwar na fuskantar wannan matsala, don haka ba za mu bari su durƙushe ba, dole mu yi wani abu don tabbatar ...
Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

Duk Labarai
Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, a jihar mai fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga. Wata sanarwa da ta samu sa hannun Garba Mohammed, mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta ce tawagar ta ƙunshi jami'an ƴansanda da jami'an tsaro ƙarƙashin gwamnatin jihar Sokoto. Bayanin ya bayyana cewa an kuɓutar da mutanen ne a tsawon kwana huɗu, daga ranar Lahadin da ta gabata. Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa. Haka nan a baya-bayan nan an samu ɓullar wata ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaƙar ƴan bindiga tun bayan ɓullar ƙungiyar ta...
NAPTIP ta kuɓutar da mutum 285 da aka yi safararsu zuwa Kano a 2024

NAPTIP ta kuɓutar da mutum 285 da aka yi safararsu zuwa Kano a 2024

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da safarar mutanen da Najeriya, NAPTIP, reshen jihar Kano ta ce ta kuɓutar da wasu mutum 285 da aka yi yunkurin safararsu tare da kama masu safarar 22 a shekarar 2024. Kwamandan hukumar a reshen jihar, Abdullahi Babale ne ya bayyana haka cikin wata hira da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN a Kano. Babale ya ce daga cikin mutum 285 da aka kuɓutar, 78 maza ne, yayin da 97 daga ciki mata ne, da ƙananan yara 110. Yayin da babban jami'in hukumar a jihar Kano ya ce sun kama mutum 22 bisa zargin hannu a laifin ciki har da maza takwas da mata 14. Abdullahi Babale ya ce laifukan da ake zarginsu sun haɗa da cin zarafin ƙananan yara da tilasta musu aikin ƙarfi, da cin zarafi ta hanyar lalata da sauran laifuka ƙarƙashin dokokin cin zarafin ɗan'adam.
Gwamnatin Bauchi ta ware Naira miliyan 400 don sayen kwamfuta guda shida ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar

Gwamnatin Bauchi ta ware Naira miliyan 400 don sayen kwamfuta guda shida ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar

Duk Labarai
Gwamnatin Jihar Bauchi ta ware Naira miliyan 400 a cikin kasafin kudin shekarar 2025 don sayen kwamfuta guda shida domin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar. Jaridar The Guardian ta rawaito cewa, haka kuma, gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan daya don “sayen fili domin gina ofisoshi da gine-gine.” Za ta kuma kashe Naira miliyan 170 don sayen janareta domin samar da wutar lantarki a ofishin SSG. Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Ibrahim Musa, ya soki wannan kasafi, yana mai bayyana shi a matsayin rashin fifikon abubuwan da suka dace a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da wahalhalu sakamakon manufofin tattalin arzikin gwamnati. Musa ya bukaci Gwamnatin Jihar Bauchi da ta kauce wa yin hakan tare da mayar da hankali kan ayyukan da za su kawo ci gaba a rayuwar al’ummar jiha...
Ban taba ganin mutane a cikin yunwa me tsanani ba irin a mulkin Tinubu>>Inji Omoyele Sowore

Ban taba ganin mutane a cikin yunwa me tsanani ba irin a mulkin Tinubu>>Inji Omoyele Sowore

Duk Labarai
Dan gwagwarmaya kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa bai taba ganin mutane a cikin tsananin yunwa irin ta zamanin mulkin Tinubu ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Sahara Reporters. Yace Gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin idan ta cire tallafin man fetur, zata yi amfani da kudin wajan gina kasa da ayyukan ci gaba. yace bai dade da dawowa daga jiharsa ta Asaliba, jihar Ondo amma bai ga wani abin ci gaba ba da aka gina. Yace rabon da ya ga lalataccen titi irin wanda ya gani an dade.
An kama malamar makaranta bayan da ta ddaki dalibarta me shekaru 3

An kama malamar makaranta bayan da ta ddaki dalibarta me shekaru 3

Duk Labarai
Wata malamar Makaranta ta shiga hannun hukuma bayan data daki dalibarta me shekaru 3 saboda ta kasa rubuta lamba 6. Lamarin ya farune a makarantar Christ-Mitots School dake Ikorodu, Legas. Bidiyo ya bayyana yanda malamar ta rika dukan dalibartata Abayomi Micheal me shekaru 3. Hakan ya jawo Allah wadai wanda yayi sanadiyyar kama malamar. Kalli Bidiyon anan Tuni Hukumar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da kama matar inda sukace za'a tabbatar da an yi adalci wajan hukuntata.
Ganduje ya goyi bayan kakakin APC kan rikinsa da Obi

Ganduje ya goyi bayan kakakin APC kan rikinsa da Obi

Duk Labarai
Shugaban Jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan kakakin Jam'iyyar APC, Felix Morka game da cacar bakin data kaure tsakaninsa da Peter Obi. Peter Obi dai ya zargi Felix Morka da cewa ya mai barazana wanda hakan yasa magoya bayan Peter Obi din suka rika tutrawa Felix din barazanar kisa. A martanin Ganduje yace babu inda Felix yawa Peter Obi barazana inda yace kuma APC ba zata yi shiru idan dan Adawa ya fadi maganar karya da ba haka take ba, zasu ci gaba da fitowa suna kare Gwamnatinsu.
Ka dakatar da shirin shigo da kayan abinci daga kasar waje, saboda tabbas farashin kayan abinci zai yi sauki amma mu kuma kasuwancin mu zai lalace>>’Yan kasuwar Najeriya suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Ka dakatar da shirin shigo da kayan abinci daga kasar waje, saboda tabbas farashin kayan abinci zai yi sauki amma mu kuma kasuwancin mu zai lalace>>’Yan kasuwar Najeriya suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shan matsin lamba akan lallai sai ya dakatar da cire harajin da yace zai yi akan kayan abinci da na magani da sauransu da ake shigowa dasu daga kasashen waje saboda kayan su yi sauki, 'yan Najeriya su siya da Arha. Majiyoyi da yawa daga fadar shugaban kasar sun tabbatar da wannan batu inda suka ce 'yan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu ne suke matsawa shugaban kasar akan lallai ya janye wannan abu da yake son gudanarwa. Suna bada dalilin cewa idan shugaban yace sai yayi hakan, to lalai zai dakushe zuba jari a Najeriya kuma za'a rasa ayyukan yi. Hakanan wasu daga cikin kamfanonin da 'yan kasuwar sun tabbatar da wannan batu inda suka ce idan shugaban kasar ya cire harajin aka fara shigo da kayan daga kasashen waje suka yi sauki a Najeriya, to s...
An saka kalmar tsire a cikin Dictionary din Turanci na kasar Ingila

An saka kalmar tsire a cikin Dictionary din Turanci na kasar Ingila

Duk Labarai
An saka wasu kalamai da ake amfani dasu a Najeriya a cikin Dictionary din turanci na kasar Ingila. Kalam da aka saka yawanci na Turancin Pidgin ne wanda aka fi sani da Broken English. Kalaman sune "Japa" wadda ke nufin tserewa daga Najeriya zuwa turai dan cirani, sai kuma kalmar “Agbero” wadda ke nufin dan tasha ko kuma marasa jin magana na kan titi, Akwai kuma kalmar "419" dake nufin rashawa da cin hanci ko zamba cikin aminci. Sauran kalmomin sun hada da cross-carpet, cross-carpeting, eba, Edo, gele, Kanuri, Kobo, Naija, suya(watau tsire), Yahoo, Yahoo boy and Yarn Dust. Jami'in tuntuba wanda dan Najeriya ne a Oxford English Dictionary, Kingsley Ugwuanyi ne ya tabbatar da hakan.
Duk da kashe Naira Biliyan 9 dan samar da tsaro a iyakokin Najeriya, Haka bata cimma ruwa ba

Duk da kashe Naira Biliyan 9 dan samar da tsaro a iyakokin Najeriya, Haka bata cimma ruwa ba

Duk Labarai
Tun a shekarar 2019 ne gwamatin tarayya ta kashe Biliyoyin Naira dan samar da tsaro a iyakokin Najeriya musamman dan hana baki daga kasashen Chad, Niger, Mali, Cameroon, da Benin Republic shigowa Najeriya. Mutanen dake shigowa daga wadannan kasashe ne ake zargi da hannu a matsalolin ta'addanci da garkuwa da mutane da sauransu. Hakanan a wannan Gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu, Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ma ya bayyana cewa, a yanzu haka ana kan saka kyamarori da sauran kayan aiki na zamani a iyakokin Najeriya dan hana baki da basu da takardun izini shigowa Najeriya. Yace a yanzu haka, fiye da rabin iyakokin Najeriya an saka musu kyamarorin inda yace kuma aiki na kan ci gaba. Hakanan yace akwai jami'an hukumar kula da shige da fici ta Immigration dake kula da...