YANZU YANZUHukumar EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, akan zargin wawure Naira biliyan 528
EFCC Ta Yi Alkawarin Bincikar Matawalle akan zargin wawure sama da Naira biliyan 528.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi alkawarin gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudi da aka yi wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, biyo bayan wani koke da jam’iyyar All Progressives Congress Young Leaders Alliance (APC-YLA) ta gabatar.
Zarge-zargen dai na zargin Matawalle da wawure sama da Naira biliyan 528 a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara.
Wannan tabbacin ya zo ne a wata zanga-zangar da aka gudanar ranar Juma’a a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda shugaban jam’iyyar APC-YLA Convener, Mohammed Ireji, da sauran masu zanga-zangar suka bukaci a sake bude shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Matawalle.
Ireji ya nuna shakku kan jinkirin...








