Thursday, January 15
Shadow
Man Fetur din Najeriya yayi kwantai a kasuwar Duniya

Man Fetur din Najeriya yayi kwantai a kasuwar Duniya

Duk Labarai
Rahotanni sun ce ganga kusan miliyan 20 na danyen man fetur din Najeriya da ake son sayarwa a tsakanin watannin Disamba zuwa January har yanzu yana nan ba'a sayar dashi ba. Kafar Reuters tace itama kasar Angola danyen man nata nacan Jibge an kasa sayar dashi. Rahoton yace kasashen biyu na ta kokarin ganin sun samu masu sayen danyen man fetur din nasu amma abu ya faskara. Rahotanni sun ce kasar China wadda tana daya daga cikin manyan masu sayen danyen man na kasashen Afrika ta fara komawa sayen man daga kasashen Larabawa saboda yafi saukin farashi da kuma saukin sufuri.
Da Duminsa: Rahotanni na cewa sojan da ya shirya jhuyin mulki a kasar Benin Republic ya samu tserewa zuwa kasar Nijar, inda aka bashi mafakar siyasa acan

Da Duminsa: Rahotanni na cewa sojan da ya shirya jhuyin mulki a kasar Benin Republic ya samu tserewa zuwa kasar Nijar, inda aka bashi mafakar siyasa acan

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, sojan da ya jagoranci juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Benin Republic, Pascal Tigri yanzu haka yana zaune a kasar Nijar. Rahoton yace Pascal Tigri ya samu mafakar siyasa a kasar ta Nijar inda yanzu haka yake zaune a wani gidan gwamnati dake kusa da fadar shugaban kasar Nijar. Rahoton yace yanzu haka ana zargin kasar ta Nijar da hannu ko da ba kai tsaye bane a yunkurin juyin Mulkin. Pascal Tigri da farko ya tsallaka zuwa kasar Togo ne inda daga nan ya hau jirgi zuwa Burkina Faso. Daga baya kuma ya sake hawa jirgi zuwa kasar Nijar. Najeriya dai ta taimakawa kasar ta Benin Republic aka murkushe yunkurin juyin mulkin.
Mun Gama da ‘Yan Adawa: Yanzu sanatoci 5 ne kadai suka rage a jam’iyyar Adawa a majalisar Dattijai, suma se rokona suke in musu jagora zuwa gurin shugaban kasa su koma APC>>Inji Sanata Godswill Akpabio

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, a lokacin da ya zama kakakin majalisar Dattijai, akwai sanatoci kusan 50 a jam'iyyun adawa. Yace amma yanzu wanda ke jam'iyyar adawa basu wuce 4 zuwa 5 ba. Yace suma sai rokonsa suke ya kaisu wajan shugaban kasa su koma APC. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/2001970822454591647?t=WxAMejfKUrJ0YdoZOAuxJg&s=19
Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta fara karbar Haraji daga masu amfani da Janareta saboda damun mutane da karansa ke yi

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta fara karbar Haraji daga masu amfani da Janareta saboda damun mutane da karansa ke yi

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, hukumar birnin ta fara karbar haraji daga hannun masu amfani da janareta saboda damun mutane da kararsa ke yi. Hakan na zuwane mutane ke kukan rashun wutar Lantarki da kuma matsin rayuwa da suka fada cikin. An ga takardar karbar irin wannan haraji na ta yawo a kafafen sada zumunta inda da yawa ke ta mamaki.
Hukumar ‘yansandan kasar Ghana ta gargadi matan aure cewa duk matar data hana mijinta mu’amalar aure, Zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari

Hukumar ‘yansandan kasar Ghana ta gargadi matan aure cewa duk matar data hana mijinta mu’amalar aure, Zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari

Duk Labarai
Jami'in Hukumar 'yansandan kasar Ghana, (ACP), Dennis Fiakpui yace takura a aure da saka damuwa babban laifine a kasar. Yace a tsakanin ma'aurata, duk wanda ya hana dan uwansa ma'amalar aure, misali mace ta ki yadda da mijinta a gado, idan ya kai kara kuma kotu ta samu matar da laifi, zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari. Yace hakanan itama idan macence mijinta baya kwanciyar aure da ita, zata iya kaishi kara a nema mata hakkinta. Yace hakanan idan miji na dadewa a waje baya komawa gida da wuri ko kuma ya daina cin abincin matarsa, duka zata iya kaishi kara a bi mata hakkinta.
Babana yana sane da cewa da yawan ‘yan Najeriya basu ji dadin mulkinsa ba>>Inji Diyar tsohon shugaban kasa, Halima Buhari

Babana yana sane da cewa da yawan ‘yan Najeriya basu ji dadin mulkinsa ba>>Inji Diyar tsohon shugaban kasa, Halima Buhari

Duk Labarai
Diyar tsohon shugaban kasa, Halima Buhari ta bayyana cewa, Mahaifinsu yana sane da cewa, mutane da yawa basu ji dadin mulkinsa ba kuma sun rika sukarsa. Ta bayyana hakane bayan wallafa littafi akan tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar. Tace duk da yake akwai wanda suka godewa shugaban kasar saboda irin yanda rayuwarsu ta canja, amma tabbas akwai da yawa wanda basu dadin mulkin mahaifin nata ba.
Kalli Bidiyo: Karya kuke, Wannan ba Samha M. Inuwa bace, baba Tambayace>>Inji Gfresh bayan da wadannan hotuna na Samha M. Inuwa ke ta yawo a kafafen sada zumunta

Kalli Bidiyo: Karya kuke, Wannan ba Samha M. Inuwa bace, baba Tambayace>>Inji Gfresh bayan da wadannan hotuna na Samha M. Inuwa ke ta yawo a kafafen sada zumunta

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya yi raddi ga wasu hotunan Samha M. Inuwa dake ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ganta babu Make-Up ko Filter kamar yanda aka saba gani a baya. A Bidiyon daya wallafa na kare Samha M. Inuwa, Gfresh yace wannan baba Tambaya ce ba Samha M. Inuwa ba. Yace shima an rika yada irin wadannan hotunan nasa na karya. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7585239692669472007?_r=1&_t=ZS-92Lj7DN2bAG