Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa s5ojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.
Yayin da yake jawabi ga sojojin ƙasar ranar Juma'a a wata ziyara da ya kai jihar Katsina - ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan fashin daji, shugaban ƙasar ya ce matsalar ƴanta'adda da masu garkuwa da mutane da ƴan fashin daji ta jima a ƙasar.
"Ƴan Najeriya sun zuba muku ido, suna jiran ku kawo ƙarshen matsalar tsaro tare da ƙwato kowane yanki na ƙasarmu, ku nuna wa maƙiyan Najeriya cewa ƙaryarsu ta ƙare'', in ji Shugaba Tinubu.
''Gwamnati na ɗaukar matakan samar muku isassun kayan aiki, da suka haɗ da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi, ba wai don kare ƙasarmu kaɗai ba, sai don samun ƙar...








