Monday, December 15
Shadow
Hankula sun koma kan Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL yayin da saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki

Hankula sun koma kan Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL yayin da saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki

Duk Labarai
Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPLC, Mele Kolo Kyari, saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki watau 60. Nan da ranar 8 ga watan Janairu ne dai Mele Kolo Kyari zai cika shekaru 60 wanda a doka ya kamata ya sauka daga kan mukaminsa dan a nada wani shugaban kamfanin. Mele Kolo Kyari shine shugaban kamfanin NNPCL da yafi dadewa akan kujerar tun bayan da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nadashi mukamin a ranar July 2019 inda a yanzu ya shafe shekaru sama da biyar akan kujerar kenan. Saidai inda gizo ke sakar shine Bayan da kamfanin NNPC ya koma na 'yan kasuwa ya fita daga hannun Gwamnati ya kuma canja suna zuwa NNPCL, doka ta baiwa Mele Kolo Kyari damar zai iya ci gaba da zama a matsayin shugaban kamfanin har nan da shekarar 2027. Wasu rahotanni kamar yanda jarid...
Mutanen dake zaune kusa da iyakar Najeriya da Nijar sun shiga fargaba biyo bayan sa in sar data barke tsakanin kasashen biyu

Mutanen dake zaune kusa da iyakar Najeriya da Nijar sun shiga fargaba biyo bayan sa in sar data barke tsakanin kasashen biyu

Duk Labarai
Wasu daga cikin mutanen dake zaune akan iyakokin Najeriya da Nijar sun shiga zullumi biyo bayan cece kucen da ya barke tsakanin kasashen biyu. Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Brig Gen Abdourahmane Tchiani ya zargi cewa Najeriya ta girke sojojin kasar Faransa tare da kafa sansanin yiwa 'yan ta'adda atisaye. Saidai me baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya karyata wannan zargi inda yace Babu inda Najeriya ta kafa sansanin sojojin kasashen waje. Ribadu yace wannan kokari ne na kawar da hankalin mutane daga gazawar gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar. Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan lamarin, wani mazaunin jihar Sokoto, Muhammad Illiyasu ya rantse da Allah cewa, cikin shekaru 30 da yake rike da sarautar Magajin garin Balle a karamar hukumar G...
Saboda jin dadin Cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tinubu ta yi da kakaba Haraji kala-kala akan ‘yan kasa, bankin Duniya ya baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan $1.5

Saboda jin dadin Cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tinubu ta yi da kakaba Haraji kala-kala akan ‘yan kasa, bankin Duniya ya baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan $1.5

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, biyo bayan cire tallafin man fetur da kakaba haraji kala-kala akan 'yan Najeriya da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi, bankin Duniya ya baiwa Najeriya bashin dala Biliyan $1.5. Cire tallafin man fetur da kakaba haraji, sharudane da bankin Duniyar ya gindayawa Najeriya wanda sai ta cikasu kamin ya bada bashin da ake nema. Bankin Duniyar da farko ya fara sakin dala Miliyan $750m a cikin watanni shida wanda masana suka ce shine mafi saurin lokaci da Najeriya ta samu bashi. Saidai sauran kudin bankin Duniyar yayi jan kafa wajan amincewa ya bayar dasu saboda Najeriya ta ki saurin kaddamar da fara karbar haraji. Sauran kudin dai a hankali za'a ci gaba da sakarwa Najeriya su bisa sharadin cika wasu sharudda da bankin Duniyar zai gindaya.
Cutar Prostate Cancer grade 3 ta kama Shugaban Israela Benjamin Netanyahu

Cutar Prostate Cancer grade 3 ta kama Shugaban Israela Benjamin Netanyahu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Likitoci sun tabbatar da cutar Prostate Cancer grade 3 ta kama Firaiministan Israela, Benjamin Netanyahu. Hakan ya haifar masa da cutar yoyon Fitsari. Dalilin hakan ne yasa dole za'a yi masa tiyata. Hakan yasa aka dage shari'ar da ake shirin yi akansa a kotu ta zargin rashawa da cin hanci. Wasu dai na ganin cewa, wannan dabara ce da Benjamin Netanyahu yake yi an kawar da hankali akan Shari'ar tasa har maganar ta shirice. Hakanan ko da yakin da Benjamin Netanyahu ke ta dagewa ake yi da kungiyar Hamas, ana ganin kamar yana yin wannan dagiya ne saboda ya gujewa zarge-zargen rashawa da cin hanci da ake masa da kuma tsawaita ranar yin zabe.
Kalli Bidiyo: Wannan matashin ya raba gardama kan su wanene a gaba tsakanin yaran shago a Farm Center da Kwari

Kalli Bidiyo: Wannan matashin ya raba gardama kan su wanene a gaba tsakanin yaran shago a Farm Center da Kwari

Duk Labarai
Wani matashi da bidiyonsa ke ta yawo a shafukan sada zumunta ya dauki hankula bayan raba gardama da yayi tsakanin matasan Farm Center dana Kwari. Yace ya ziyarci wani abokinsa a Farm Center inda ya siyasa musu abincin dubu 3 kowannensu. kalli Bidiyon anan https://twitter.com/bapphah/status/1872882854084132903?t=ihZdF9d8gJOVb5acIaJlUQ&s=19 A bayaninsa yace, idan a Kwari ne yaron shago yayi haka ko ya yake saka kaya masu tsada, korarsa za'a yi a ce yanawa me gidansa sata. Masu Sharhi akan wannan bayani na wannan matashi da yawa dai wasu sun yadda dashi inda wasu suka karyatashi. Wasu kuwa sun ce Farm Center ta matasa ce inda ita kuma Kwari ta dattawa ce, shiyasa.
An yi Allah wadai da wadannan matan saboda yanda suke kiran sauran mata da su je su bayar da kansu maza su basu kudi

An yi Allah wadai da wadannan matan saboda yanda suke kiran sauran mata da su je su bayar da kansu maza su basu kudi

Duk Labarai
Wannan bidiyon na wasu matan banza na yawo sosai a kafafen sada zumunta saboda yanda suka rika kiran sauran mata da su je su bayar da kansu dan a basu kudi. Sun dai baiwa mata shawarar cewa su yi amfani da lokacin kirsimeti da ake ciki dan samun kudi sosai ta hanyar bayar da jikinsu a yi lalata da su. Danna nan dan kallon Bidiyon https://twitter.com/GeneralSnow_/status/1872974616312086556?t=qoqQbMSOjAwQvRdz4ECUgw&s=19 Da yawa sun yi Allah wadai da su.
Bidiyo:An kamashi yana kaiwa ‘yan Bìndìgà mata suna biyanshi Naira dubu 10

Bidiyo:An kamashi yana kaiwa ‘yan Bìndìgà mata suna biyanshi Naira dubu 10

Duk Labarai
Wannan wani bawan Allah ne da aka kama yana aikin kaiwa 'yan Bindiga mata suna biyanshi Naira dubu 10. Ya bayyana hakanne da bakinsa a yayin da yake amsa tambayoyi kan laifukan da yake aikatawa. https://twitter.com/ZagazOlaMakama/status/1872989588832063595?t=3JI1WrDlaqaeBHe2s-7-lw&s=19 Masu baiwa 'yan Bindiga bayani na daya daga cikin masu yaimakawa ayyukansu inda suke cutar da Al'umma.
An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

Duk Labarai
Bataliyar rundunar sojin Najeriya mai yaƙi da yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ake kira da Operation Fansar Yamma, ta samu nasarar cafke wata mata mai shekaru 25 da haihuwa dauke da alburusai 764 da kuma bindigogi guda shida, da ake zargin za ta kai sansanin madugun ƴan fashin dajin nan Bello urji Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar laftanal kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce an kama matar ne a ranar 28 ga watan Disamban 2024 da ake ciki, tare da wani abokin tafiyarta a yankin Badarawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Kamen dai ya biyo bayan wani rahoton sirri da aka samu game da safarar makaman ƴan bindigar a kan hanyar Kware zuwa Badarawa a karamar hukumar ta Shinkafi. Bayan samun waɗannan bayanai ne dakarun rundunar ta Operation Fansar ...