Saturday, April 11
Shadow
Da Duminsa: Ji Abinda mataimakin Gwamnan Bauchi yace bayan da “ya zabgawa Minista mari”

Da Duminsa: Ji Abinda mataimakin Gwamnan Bauchi yace bayan da “ya zabgawa Minista mari”

Duk Labarai
Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Muhammad Jatau ya yi magana akan rahoton dake cewa ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar mari. Jatau yayi magana ta bakin kakakinsa, Muslim Lawal inda yace rahoton marin ba gaskiya bane Yace su basu ma da labari game da maganar marin a bakin 'yan jarida suke ji. Yace babu ta yadda za'a yi mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya mari minista, yace ko gwamna ba zai mari minista ba ballantana mataimakinsa. Kokarin jin ta bakin ministan ya ci tura.
Kalli yanda matashi ya Kàshè kansa bayan kama Budurwarsa na cin amanarsa

Kalli yanda matashi ya Kàshè kansa bayan kama Budurwarsa na cin amanarsa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani matashi dalibin jami'a a kasar Ghana ya kàshè kansa ta hanyar rataya bayan kama budurwarsa na cin amanarsa. Lamarin ya farune a jami'ar University of Education, Winneba dake kasar ta Ghana ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu. Saidai ba'a bayyana sunan dalibin ba. Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin ya yanke jiki ya fadi bayan kama budurwar tasa inda kuma daga bisani ya shiga daki ya rataye kansa. 'Yansandan garin Winneba sun dauke gawar matashin inda suka tafi da ita suka...
Da Duminsa: An Zargi Mataimakin gwamnan Bauchi Auwal Jatau da Zabgawa Ministan Harkokin Waje Mari..

Da Duminsa: An Zargi Mataimakin gwamnan Bauchi Auwal Jatau da Zabgawa Ministan Harkokin Waje Mari..

Duk Labarai
A ranar Juma’a ne wani Al'amari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a fadar Sarkin Bauchi, inda aka zargi mataimakin gwamnan jihar Auwal Jatau da Zabgawa ministan harkokin kasashen Waje Yusuf Maitama Tuggar Mari a Sa'ilin da wata hatsaniya mai zafi ta barke Tsakannin Ministan Da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad. Lamarin ya faru ne a lokacin da ake bikin nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, a matsayin Makama Babba na Masarautar Bauchi, wanda ya yi daidai da daurin auren diyarsa, Khadija Mohammed. Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan yan siyasa da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima,da gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da dai sauransu. A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya samo asali ne bayan da rahotanni suka ce minist...
Cikin sauki zan sake cin zabe a shekarar 2027, ‘Yan Najeriya sun shaida kokarina, kar har Kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina min>>Shugaba Tinubu

Cikin sauki zan sake cin zabe a shekarar 2027, ‘Yan Najeriya sun shaida kokarina, kar har Kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina min>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayarwa da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Datti Baba Ahmad martani bayan da yace idan shugaban kasar na da wayau kada ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 saboda faduwa zabe zai yi. A martaninsa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace maganar Datti ta banza ce wadda ba basira ko kadan a ciki. Da yake magana da bakin kakakinsa, Daniel Bwala, Shugaba Tinubu yace Datti Ahmad ya daina shiga harkar da bai iya ba, watau siyasa, ya barwa wanda suka iya su yi. Yace yayi kokari sosai na daukar matakan gyara wanda 'yan Najeriya sun shaida kuma har kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina masa inda suka ce ya Dora Najeriya a turbar karfafa tattalin arziki.
Babu Dan Arewa da ya isa ya zama shugaban kasa a 2027 sai 2031 bayan Tinubu ya gama saboda Buhari ma sau biyu yayi mulki>>Inji Wike

Babu Dan Arewa da ya isa ya zama shugaban kasa a 2027 sai 2031 bayan Tinubu ya gama saboda Buhari ma sau biyu yayi mulki>>Inji Wike

Duk Labarai
Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa babu dan Arewar da ya isa ya zama shugaban kasa sai a shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gama wa'adinsa karo na biyu. Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja. Wike yace dan Arewa ya yi mulki har sau biyu dan haka Shima Tinubu sai yayi sau biyu daga kudu kamin wani dan Arewa ya sake mulka. Yace babu wani yanki da zaice shi kadai zai ta yin mulkin Najeriya, tsarin karba-karba za'a ci gaba da yi.
Jam’iyyar NNPP ta yi bayani dalla-dalla kan komawar Kwankwaso APC

Jam’iyyar NNPP ta yi bayani dalla-dalla kan komawar Kwankwaso APC

Duk Labarai
NNPP ta karyata jita-jitar sauyin sheka na Kwankwaso Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta karyata jita-jitar da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC. Shugaban jam’iyyar a jihar, Hashimu Dungurawa, ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Kano. Dungurawa ya ce Kwankwaso ba ya bukatar shawarar kowa wajen yanke shawarar siyasa, amma ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya sheka. “Ba mu da wata alaka da APC, kuma ba mu da niyyar sauya sheka,” in ji Dungurawa, yana karyata jita-jitar da cewa wani makirci ne kawai. Ya nuna tabbaci cewa gwamnatin NNPP a Jihar Kano tana samun nasara kuma tana maido da doka da oda a yankin. An rawaito shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano yana cewa kofar jam’iyyar a bude take ga Kwankwaso da sa...
Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu

Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu

Duk Labarai
Ba wanda ya hana ni shiga fadar shugaban kasa - Kashim Shettima Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana rahotannin da ke yawo cewa an hana shi shiga fadar shugaban kasa a matsayin karya maras tushe. Daily Trust ta rawaito cewa a daren jiya Juma’a ne wasu rahotanni su ka fito daga wata kafar labarai ta yanar gizo suna cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga fadar shugaban kasa ta hannun wasu jami’an tsaro, tare da cewa an killace shi a gidansa har sai shugaban kasa ya dawo daga tafiyarsa ta kasashen waje. Amma cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Mista Stanley Nkwocha, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, ya ce: “A 'yan kwanakin nan, an shirya kuma an tsara yada labaran karya da gangan akan...
Miji ya kàshè mutumin dake shirin auren tsohuwar matarsa da yawa saki 3 a jihar Naija

Miji ya kàshè mutumin dake shirin auren tsohuwar matarsa da yawa saki 3 a jihar Naija

Duk Labarai
Wani mutum me suna Alhaji Yikangi daga kauyen Chikan na karamar hukumar Gbako jihar Naija ya kashe bazawarin tsohuwar matarsa me suna Muhammad Ma’aba. Alhaji Yinka yawa matarsa me suna Fatima Suleiman saki 3 wanda bisa tsarin addinin Musulunci ba zai iya sake aurenta ba sai bayan ta sake yin wani auren ta fito. Saidai Alhaji Yinka ya sha Alwashin matar tasa saidai ta dawwama ba aure dan kuwa ba zai barta ta yi auren ba. Rahoton yace ya jagoranci mutane inda sukawa Muhammad Ma'aba Kwantan Bauna suka ta dukansa har sai da ya mutu. Kakakin 'yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna bincike dan kama duka masu hannu a lamarin.