Thursday, January 15
Shadow
Buhari har yayi Mulkinsa ya gama bai kama kowa ba, kuma baisa a kama kowa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Buhari har yayi Mulkinsa ya gama bai kama kowa ba, kuma baisa a kama kowa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai kama kowa ba kuma bai sa a kama kowa ba har yayi mulkinsa ya gama. Ya bayyana hakane a martanin da yakewa Dawisu, Watau Salihu Tanko Yakasai da yace Buhari ya kamashi. Bashir yace idan dai Dawisu zai ce an kamashi a zamanin Mulkin Buhari zai yadda amma maganar cewa Buhari yasa an kamashi ba gaskiya bane. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/2001370109445562762?t=pvR-855gABYzJoFn1hwUeA&s=19
Kalli Hotunan yanda ganawar Wakilan Najeriya da shugaban kasar Burkina Faso ta kasance

Kalli Hotunan yanda ganawar Wakilan Najeriya da shugaban kasar Burkina Faso ta kasance

Duk Labarai
Wadannan wakilan Gwamnatin Najeriya ne karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje Yusuf Tuggar inda suka gana da shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore. Sun mikawa Shugaba Traore da sakon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna goyon bayan gwamnatinsa. Sannan sun bayar da hakuri game da shiga kasar Burkina Faso da jirgin Najeriyar yayi. Sun bayyana muhimmancin ci gaba da dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Burkina Faso.
Da Duminsa: EFCC sun kulle gidan da matar Malami, Diyar Tsohon shugaban kasa take ciki

Da Duminsa: EFCC sun kulle gidan da matar Malami, Diyar Tsohon shugaban kasa take ciki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun kulle gidan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami inda matarsa, diyar tsohon shugaban kasa, Fatima Buhari take. Jam'iyyar ADC ce ta bayyana hakan inda ta zargi Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da wulakanta Buhari ta wannan hanya. Ana zargin Malami da Almundahanar kudade da yawa ciki hadda kudaden Abacha da aka kwato daga kasashen waje.
Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa bayan da Dangote ya zargeshi da kashe dala Miliyan $7 wajan kai ‘ya’yansa kasar Switzerland karatu

Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa bayan da Dangote ya zargeshi da kashe dala Miliyan $7 wajan kai ‘ya’yansa kasar Switzerland karatu

Duk Labarai
YANZU-YANZU: Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar mai ta NMDPRA Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen sababbin shugabannin NUPRC da NMDPRA domin amincewa, bayan murabus ɗin Engr. Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe. Sabbin waɗanda aka naɗa su ne Oritsemeyiwa Eyesan da Engr. Saidu Aliyu Mohammed. Farouk dai shine ke rikici da Aliko Dangote Me zaku ce?
Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Duk Labarai
Najeriya ta aika da wakilai na musamman zuwa kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za'a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu C-130. Wadanda aka aika din daga ma'aikatar harkokin kasashen waje ne da kuma ma'aikatar tsaro ta kasa. Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya jagoranci tawagar. Zasu tattauna maganar sasanci tsakanin kasashen biyu da kuma inganta tsaro.
Kalli Hoto: Nuna wayar ta ta iPhone 17 Pro Max ta jawowa kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom cece-kuce inda da yawa ke cewa Albashinta bai isa ya saya mata wayar ba

Kalli Hoto: Nuna wayar ta ta iPhone 17 Pro Max ta jawowa kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom cece-kuce inda da yawa ke cewa Albashinta bai isa ya saya mata wayar ba

Duk Labarai
Kakakin 'yansandan jihar Akwa-Ibom, Timfon John ta dauki hankula bayan da aka ganta rike da wayar iPhone 17 Pro max ta Naira Miliyan 2.5 a yayin da Albashinta bai wuce Naira 300,000 ba. Da yawa dai sun rika caccakar ta da cewa ina ta samo wayar dan Albashinta dai ba zai iya saya mata wayarba. https://twitter.com/officerTimzy/status/2000986882457371048?t=jgvbDoV1hReDR0MGGKKa_g&s=19 Saidai kakin 'yansandan jihar Delta, Bright Edafe ya kare abokiyar aikin nasa inda yace watakila ta tara kudinne ta siya. Yace akwai wanda da gaske suna satar amma an zuba musu ido. https://twitter.com/Brightgoldenboy/status/2001283075662025113?t=g01jqwU9KgVSOJXaRylpsw&s=19
Tauraron Dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya kwallo

Tauraron Dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya kwallo

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya wasa bayan shekaru 15 da ya shafe yana buga wasa. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta. Ahmed Musa ya bugawa Najeriya wasanni 111 inda kuma shine wanda yafi kowane dan wasa yawan kwallaye a gasar cin kofin Duniya a Najeriya. https://twitter.com/Ahmedmusa718/status/2001265044110135753?t=lKaDFBWYJpufeS7G-QIDjQ&s=19
Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abinda ya faru a masallacin Hotoro Kano, ya sake faruwa a Arewa

Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abinda ya faru a masallacin Hotoro Kano, ya sake faruwa a Arewa

Duk Labarai
A yayin da ake tsaka da alhinin abinda ya faru a Masallacin dake Hotoro Kano inda wani yawa Ladani yankan Rago ya ciro Makogoronsa. A jihar Bauchi kuma wani gidane aka kama ma matsafa dake daukar 'yan mata suna zuwa suna tsafi dasu. Saidai dubunsu ya cika. https://www.tiktok.com/@usmaniyya61/video/7584529260925259029?_t=ZS-92Ik6NRW9hZ&_r=1 Hakanan a Kanon dai a shekar Mai Daki an samu wasu marasa Imani sun shiga har gida suka qàshè wata mata da danta, sannan suka Qònà Gawarsu. https://www.tiktok.com/@shataaliyu/video/7584775592344718613?_t=ZS-92IkYNI269Q&_r=1 Sai a Legas kuma da Wani Uba ya Hallaqa dansa har lahira wanda shima dan Arewa ne. https://www.tiktok.com/@danhajia_ojo/video/7584599644395556117?_t=ZS-92Il0bOAmPZ&_r=1