Sunday, April 19
Shadow
Labari Me Dadi: Majalisar Tarayya tace hukumar sadarwa ta NCC ta gaggauta toshe duk wani shafin dake nuna bidiyo da hotuna na tsìraìcì watau Blù Fìm

Labari Me Dadi: Majalisar Tarayya tace hukumar sadarwa ta NCC ta gaggauta toshe duk wani shafin dake nuna bidiyo da hotuna na tsìraìcì watau Blù Fìm

Duk Labarai
Majalisar tarayya ta amince da kudirin dokar toshe duk wani shafin yanar gizo dake nuna Bidiyo da hotunan tsiraici wanda aka fi sani da Blù fìm. Majalisar tace hukumar sadarwa ta kasa,NCC ta baiwa duka kamfanonin dake samar da Internet a Najeriya umarnin toshe shafukan dake nuna batsa nan take. Dan majalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki ne ya kai kudirin dokar majalisar wanda kuma sauran 'yan majalisar suka amince dashi.
El-Rufai baya mutunta watan Ramadan, Tunda watan ya kama, bashi da aiki sai zagi da sukar shugaban kasa, Bola Ahmad>>Inji Reno Omokri

El-Rufai baya mutunta watan Ramadan, Tunda watan ya kama, bashi da aiki sai zagi da sukar shugaban kasa, Bola Ahmad>>Inji Reno Omokri

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya soki tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan da ya bar APC ya koma Jam'iyyar SDP. A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Reno Omokri ya zargi El-Rufai da rashin girmama watan Ramadana me Alfarma. Ya bayyana cewa tun da aka kama watan Azumin Ramadana El-Rufai bai yi amfani da shafukansa na sada zumunta ba wajan fadakar da Musulmai kan watan ba, maimakon hakan sai zagi da sukar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. ...
Kasuwanci Miliyan 7.2 ne aka kulle suka rushe a karkashin mulkin Tinubu saboda matsin rayuwa

Kasuwanci Miliyan 7.2 ne aka kulle suka rushe a karkashin mulkin Tinubu saboda matsin rayuwa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, daga shekarar 2023 zuwa 2024 kasuwanci miliyan 7.2 aka kulle suka ruguje saboda rashin tabbas na tattalin arzikin Najeriya. Shugaban hukumar bincike akan tattalin arziki ta kasa, NESG me suna Dr. Segun Omisakin ne ya bayyana hakan. Ya kara da cewa, hakan ya jawowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 94. Ya bayyana hakane a yayin kaddamar da rahoto akan kamfanoni inda yace kaso 30 cikin 100 na kananan kasuwancin da ake dasu a Najeriya sun kulle. Yace Najeriya na da jimullar kananan kasuwanci miliyan 24 kuma a yanzu gida Miliyan 7.2 daga cikinsu sun kulle. Yace rashin tabbas na tattalin arziki da hauhawar farashin kayan masarufi da kashe kudi da yawa wajan gudanar da ayyukan su ne ya jawo hakan.
Mahaukaciyace kawai da bata da rabon arziki dana zaice yana son dirka mata cikin shege amma tace bata yadda ba>>Inji Mahaifin me kudin Duniya Elon Musk dake da ‘ya’ya 13 wanda kusan duk ba ta hanyar aure ya samesu ba

Mahaukaciyace kawai da bata da rabon arziki dana zaice yana son dirka mata cikin shege amma tace bata yadda ba>>Inji Mahaifin me kudin Duniya Elon Musk dake da ‘ya’ya 13 wanda kusan duk ba ta hanyar aure ya samesu ba

Duk Labarai
Mahaifin me kudin Duniya, Elon Musk watau Errol Musk ya kare dansa bayan da aka tambayi ra'ayinsa game da da na 13 da dansa ya haifa da wata shahararriyar me amfani da kafafen sadarwa me suna Ashley St. Clair. Mahaifin na Elon Musk yace ai mahaukaciya ce kawai ba zata amincewa dansa ya dirka mata cikin shege ba. Elon musk dai yana da jimullar 'ya'yaye 14 wanda ya haifa tare da mata 4. Shima dai mahaifin na Elon Musk, Errol 'ya'yansa 7 2 daga cikinsu ya haifesu ne tare da diyar matarsa, watau Agola.
Matashi ya jawo cece-kuce bayan da ya bayyana cewa, yana soyayya da uwa da ‘yarta kuma kwacce ya dirka mata ciki

Matashi ya jawo cece-kuce bayan da ya bayyana cewa, yana soyayya da uwa da ‘yarta kuma kwacce ya dirka mata ciki

Duk Labarai
Wani shahararren me wallafa a kafar YouTube, Nicholas Hunter ya bayyana cewa, yana soyayya da abokiyar aikinsa, Nicholas Hunter me shekaru 22 da kuma mahaifiyarta. Sannan yace ya dirkawa kowacce daga cikinsu ciki. Saidai a hirar da aka yi dashi a jaridar Daily Mail, yace cikin na wasane amma maganar soyayya akwaita tsakaninsa diyar da mahaifiyar duka yana soyayya dasu. Saidai yace shi nishadi yake baiwa mutane dan haka yake yin duk abinda ya kamata dan nishadantar da mabiyansa.
Yanzu dole zamu sa ido akanka tunda kana barzanar kwace mana mulki>>Gwamnatin Tinubu ga El-Rufai bayan da ya canja Jam’iyya daga APC zuwa SDP

Yanzu dole zamu sa ido akanka tunda kana barzanar kwace mana mulki>>Gwamnatin Tinubu ga El-Rufai bayan da ya canja Jam’iyya daga APC zuwa SDP

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata saka ido akan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan da ya canja Jam'iyya daga APC zuwa SDP. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin me baiwa shugaban kasar shawara kan yada labarai, Daniel Bwala. Bwala yace basu da matsala da El-Rufai akan canja Jam'iyya. Amma barazanar da yake musu ta cewa, zai hada kan 'yan adawa dan su taru su hana APC cin mulki a shekarar 2027 yasa dole su saka ido akansa. El-Rufai yace banba...
Yaro daya ya Mùtù wasu 21 sun jikkata bayan da tukunyar gas ta fashe a Goron Dutse, Kano

Yaro daya ya Mùtù wasu 21 sun jikkata bayan da tukunyar gas ta fashe a Goron Dutse, Kano

Duk Labarai
Yaro dan shekaru 14 ya mutu wasu mutane 21 suka jikkata bayan da tukunyar gas ta fashe a Goron Dutse dake Jihar Kano. Lamarin ya farune da misalij karfe 2:30 na rana a gidan Malam Isiyaka Rabiu yayin da tukunyar gas din ta fashe a dakin girki. Rahoton yace wuta ta kama bayan fashewar gas din. Tawagar 'yansanda bisa jagorancin ACP Nuhu Mohammed Digi ta kai dauki inda lamarin ya faru. An kai wadanda suka jikka zuwa asibitocin Gamji Hospital, Dala Orthopaedic Hospital, da Murtala Mohammed Specialist Hospital dan kula dasu. 'Yansandan sun mika sakon ta'aziyya zuwa ga iyalan wanda ya rasu.
Lauyoyi sun yi Allah wadai da ‘yansanda kan yanda suka nuna gawar tsohon shugaban Immigration da ya mutu a dakin otal bayan ganawar sirri shi da wata mata

Lauyoyi sun yi Allah wadai da ‘yansanda kan yanda suka nuna gawar tsohon shugaban Immigration da ya mutu a dakin otal bayan ganawar sirri shi da wata mata

Duk Labarai
Wata kungiyar Lauyoyi daga jihar Filato sun yi Allah wadai da hukumar 'yansandan kan yanda suka nuna gawar tsohon shugaban hukumar Immigration da ya mutu a dakin otal bayan ganawa da wata mata. Tsohon Kwamandan na hukumar Immigration David Parradang da farko an ruwaito cewa an yi garkuwa dashi ne, saidai daga baya an musanta wannan ikirarin. Hukumar 'yansandan Najeriya a ranar 4 ga watan Maris sun bayyana cewa, ya mutu ne a dakin otal bayan ganawa da wata mata. Da take mayar da martani kan lamarin, kungiyar Lauyoyin daga jihar Filato, The PLBF ta bayyana cewa, nuna hoton gawar David cin fuska ne wanda bai kamata ba. Ta kara da cewa yada labarin da bai inganta ba akan David din bata masa sunane Hakanan kungiyar Lauyoyin ta bayyana cewa, shiruj da hukumar Immigration ta yi aka...
Yaran da ba’a haifa bane nake son baiwa Kariya shiyasa na cire tallafin Man fetur>>Tinubu

Yaran da ba’a haifa bane nake son baiwa Kariya shiyasa na cire tallafin Man fetur>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yaran da ba'a haifa nan gaba bane yake son ya baiwa kariya shiyasa ya cirw tallafin man fetur. Shugaban ya bayyana hakane a fadarsa wajan kaddamar da kwamitin ci gaban matasa inda yace gwamnatinsa zata ci gaba da baiwa matasa kwarin gwiwa. Shugaban yace idan ka duba masu karfafa cewa a bar Najeriya a tafi wata kasa ci rani, saboda babu ci gaba sosai, amma idan aka samu ci gaba, babu wanda zai so ya tafi wata kasar. Shugaban yace a lokaci da ya fara mulki, matsaloli sun yi yawa inda ake ta kuka, yace amma yanzu tattalin arziki ya fara farfadowa inda farashin kayan masarufi ya sauka.