Abubuwan da ya kamata ka sani game da komawar El-Rufai SDP
A jiya ne tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana komawa Jam'iyyar SDP inda yace ya fita daga Jam'iyyar APC.
A takardar barin APC da ya aikewa ofishin Jam'iyyar ya bayyana banbantar ra'ayi wanda yace ya gano ba zasu samu jituwa ba shi da Jam'iyyar ta APC.
Yace a baya yana da niyyar saidai idan ya daina siyasa ne zai daina yin Jam'iyyar ta APC amma a yanzu saboda kaucewa tsari da banbancin ra'ayi, yace ya bar Jam'iyyar duk da yana daya daga cikin wanda suka kafata.
El-Rufai yace babban abinda zai mayar da hankali a yanzu shine hado kan 'yan Adawa dan su hade su kayar da Jam'iyya me mulki zabe a shekarar 2027.
Saidai a martanin da fadar shugaban kasa ta mayarwa da El-Rufai ta hannun ms baiwa shugaban kasar shawara a fannin sadarwa, Daniel Bwala yace zasu s...







