Wani Bidiyon yanda fada ya kaure a tsakiyar titin babban birnin tarayya Abuja ya dauki hankula.
Bidiyon ya nuna wani mutum da mutane 3 suka tarar masa amma duka ya gagaresu.
https://twitter.com/abujastreets/status/1918291259908571165?t=t2fwv9g8VCD2370fkNWNMw&s=19
Saidai da dama sun bayyana mamakin faruwar irin hakan a tsakiyar Abuja.
Gwamman Jihar Osun, Ademola Adeleke kenan a wannan Bidiyon inda aka ganshi yana tika Rawa tare da wasu mutanensa a wajan motsa jiki.
Lamarin ya dauki hankula duk da yake cewa ba yau ya fara rawa a bainar jama'a ba.
https://twitter.com/AsakyGRN/status/1918055113672785996?t=CRdua9ANHmlPHeOHYHeKHA&s=19
Adeleke dai Kawune a wajan shahararren mawakin Najeriya, Davido.
Kasar Kenya ta kera mota me amfani da wutar Lantarki.
Bidiyon yanda aka gabatar da motar ya dauki hankula inda aka rika yabawa kasar.
https://twitter.com/dom_lucre/status/1918088873046904966?t=V96O174iY2-Var-6Argq7A&s=19
Motar dai ta burge wasu inda wasu kuma suka rika kusheta.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa iayalinsa musamman dansa, Seyi Kunne.
Atiku yace Najeriya ba kayan Tinubu bane kasa ce ta al'umma dan haka bai kamata a bar dan shugaban kasar yana abinda yake ba na yawo yana nemawa mahaifinsa goyon baya ba.
Atiku yace ya zama wajibi a binciki zargin da shugaban kungiyar daliban Najeriya ya yiwa Dan shugaban kasar dan gano gaskiya.
Atiku yace kuma ko me ya faru da Shugaban daliban ba zasu amince ba zasu tsaya mai.
Yace abin takaici ne ace irin wannan abin yana fitowa daga iyalin shugaban kasa.
Atiku yace wannan abu ne da ba za'a amince dashi ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kaiwa sojojin Najeriya na rundunar Operation FANSAR YAMMA dake yaki da 'yan Bindiga a jihar Katsina ziyarar ba zata dan ya ga yanda ake gudanar da aiki.
Shugaban ya je ne ba tare da jami'an tsaronsa ba kamar yanda aka saba.
Ya karfafa sojojin musamman yanda suka sadaukar da rayuwarsu dan samarwa mutanen Najeriya tsaro.
Yace zasu yi kokarin biyan sojojin dukkanin hakkokinsu da kuma inganta rayuwarsu data iyalinsu.
Irin Yadda Allah Ya Daukaki Kuŕ'ani Da ManźonŠà, Allah Ya Daukaka Sarki Aminu Ado Bayero Ya Kuma Daga Martabarsa, Inji Sheik Lawal Triumph.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Shehin Malamin ya gabatar da wannan addu'ar ne a wajen bikin saukar karatun Alƙur’ani da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya halarta a jiya Alhamis, Kofar Gidan Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babbba Ɗan'agundi, Dake Unguwar Gini Musa Da Ofishin 'Yan Śanda na Kwalli a cikin birni Kano.
Wannan wata mata ce data bayyana inda ta yi ikirarin Annabta.
Matar tace tana da wata karama a kanta da duk wanda ya shafa yake samun waraka musamman daga kangin Talauci.
Mutane maza da mata na ta tururuwa zuwa gidanta dan taba kanta kamar yanda Bidiyon ya nunar.
https://www.youtube.com/watch?v=0jH98leT6fs
Sai Muce Subhanallah.
Hotunan tsohuwar tauraruwar kafafen sada zumunta me suna Leemah sun dauki hankula sosai.
An ga yanda wasu ke hada hotunanta na da dana yanzu inda ake mamakin yanda girma ya fara kamata.
Da yawa dai sun mata fatan Alheri.
Jam'iyyar adawa ta LP a Najeriya ta nesanta kanta daga shiga kowace irin ƙawance dmin tunkarar zaɓen 2027.
Kwamitin zartarwar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ne ta tababtar da haka lokacin wani taro da ta gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar.
A baya-bayan nan dai jam'iyyun hamayya a Najeriya na ta ƙoƙarin ƙulla wata haɗaka domin tunkarar jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
To sai dai jam'iyyar ta LP ta ce ba za ta shiga kowace irin haɗaka.
“Taronmu a jajjada cewa jam'iyyarmu ba ta ciki, kuma ba za ta shiga kowane irin haɗaka ba domin tunkarar zaɓen 2027, a maimakon haka jam'iyyar LP za ta mayar da hankali wajen sake gina kanta ta hanyar ɓullo da sabbin sadaru da ƙarfafa kanta domin samun nasara a zaɓen 2027'', in ji Abure.