Saturday, December 6
Shadow
Kalli Bidiyo:Ni dai indai da wannan makamin ne zamu Yhaqi America to dan Allah Tinubu ya baiwa Trump hakuri kawai dan ban Shirye Tafiya Lahira ba

Kalli Bidiyo:Ni dai indai da wannan makamin ne zamu Yhaqi America to dan Allah Tinubu ya baiwa Trump hakuri kawai dan ban Shirye Tafiya Lahira ba

Duk Labarai
Wannan bawan Allahn ya dauki hankula bayan da yace in dai da wannan makamin ne Najeriya zata yaki Amirka to yana kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa Amirka Hakuri dan shi bai shirya Mutuwa ba. Bidiyon da yayi wannan jawabi ya dauki hankula sosai. https://www.tiktok.com/@makeel.backup/video/7568258557234122002?_t=ZS-916Qf50GRAP&_r=1
Da Duminsa: Biyo bayan Barhazhanar Amurka na kawo hari Najeriya Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da shuwagabannin tsaro sun yi ganawar sirri

Da Duminsa: Biyo bayan Barhazhanar Amurka na kawo hari Najeriya Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da shuwagabannin tsaro sun yi ganawar sirri

Duk Labarai
Biyo bayan Barazanar shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta kai hari Najeriya kan masu Khisan Kiristoci, Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya kira taron gaggawa na shuwagabannin tsaro da leken Asiri. Taron wanda aka farashi da yammacin ranar Lahadi ya mayar da hankali ne kan barazanar shugaban kasar Amurka a Najeriya da kuma abinda hakan ka iya haifarwa. Sannan Rahoton Sahara Reporters yace an kuma tattauna matakan shirin da za'a dauka dana kota kwana da kuma irin martanin da ya kamata a yi.
Kowa ya Kwantar da Hankalinsa: Trump bai isa ya kawo Khari Najeriya ba sai na amince>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Kowa ya Kwantar da Hankalinsa: Trump bai isa ya kawo Khari Najeriya ba sai na amince>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa Amurka bata isa ta kawo Hari Najeriya ba sai da amincewarsa. Ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara kan sadarwa, Daniel Bwala a hirarsa da manema labarai. Daniel Bwala yace Keta dokar kasa da kasa ne wata kasa ta kaiwa wata kasa hari ba tare da sanin kasar da aka kaiwa harin ba. Yace ba'a fahimci abinda Trump ya fada bane, wannan abu ne da zasu warwareshi ta hanyar Diplomasiyya. Ya bayyana cewa, Suna godiya ga Trump da amincewa da yayi ya sayarwa da Najeriya makamai a zamanin mulkinsa na farko.
Kalli Bidiyon: Wai ku ‘yan Najeriya kun rainamu koh, kuna ganin ba zamu iya da sojojin Amurka ba? To Wallahi Kharo da kaiy kawai idan nawa Sojan Amurka ko shurhawa ba zai yi ba>>Inji Wannan sojan Najeriyar

Wani sojan Najeriya ya bayyana yana cewa, 'yan Najeriya su daina musu kallon ba zasu iya da sojojin kasar Amurka ba. Yace Karo da kai kawai idan yawa sojan Amirka ko shurawa ba zai yi ba. Yace su da ake kaisu kasashe su taimaka wajan samun zaman Lafiya shine za'a ce wai wata Amurka zata gagaresu? Yace mutane su daina wannan tunanin: https://twitter.com/AsakyGRN/status/1985323453948321847?t=aeOzMrIF9t_KuYK8xXj7Hg&s=19
Wallahi Sharri aka kala min ban zaghi Shugaban Amurka, Donald Trump ba, Inji Sanata Godswill Akpabio bayan da wani Rahoto ya bayyana dake cewa ya gayawa Trump maganganu marasa dadi

Wallahi Sharri aka kala min ban zaghi Shugaban Amurka, Donald Trump ba, Inji Sanata Godswill Akpabio bayan da wani Rahoto ya bayyana dake cewa ya gayawa Trump maganganu marasa dadi

Duk Labarai
Kakakin Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa sharri ake masa rahoton dake cewa wai ya zagi shugaban kasar Amurka Donald Trump. Rahotan wanda wata kafa me suna Rant HQ Politics ta wallafa tace Akpabio yace ai a Najeriya ake Shekye mutane ba'a Amurka ba dan haka Ba ruwan Trump da Najeriya. Saidai a sanarwar daya fitar, Akpabio yace shi bai fadi wannan magana ba, sharri aka kala masa. Akpabio yace yana girmama Trump a matsayin shugaban kasa me karfi sannan ba zai tsoma bakinsa akan abinda ke faruwa a kasar Amurka ba.
Kalli Bidiyon: Dan Allah a samu malaman (Gaskiya) su fito su yi bayani, Samarin mu sun dauki fatawar Sheikh Karmawi, idan suka zo neman auren mu sai su ce wai sai sun leka>>Inji Murja Kunya

Tauraruwar Tiktok Murja ta bayyana cewa suna neman Agaji daga malamai su fito su fayyace maganar Sheikh Alkarmawi wanda yace ya halasta idan mutum ya je neman aure a bude masa ya leka. Murja tace samarinsu sun damesu duk wanda yaje sai yace malam yace a rika lekawa. Tace dan Allah a samu wani malami ya fito yayi bayanin gaskiyar lamarin. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7567958837995654456?_t=ZS-915ifq9Co1Q&_r=1
Fadar Shugaban kasa ta karyata Rahoton dake cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump

Fadar Shugaban kasa ta karyata Rahoton dake cewa, Shugaba Tinubu zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta musanta Rahoton dake cewa shugaban kasar zai gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Wani Rahoto da Sahara Reporters suka ruwaito sun ce sun samu daga fadar shugaban kasa cewa shugaba Tinubu zai gana da mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance a ziyarar da zai kai kasar. Saidai fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tace ba gaskiya bane, kuma idan ma shugaba Tinubu zai je kasar Amurka, da shugaban kasar, Donald Trump zai gana ba da mataimakinsa ba.
Da Duminsa: Kasar Chadi ta kulle iyakarta da Najeriya bayan rahotan cewa Amurka zata kawo Khari Najeriya

Da Duminsa: Kasar Chadi ta kulle iyakarta da Najeriya bayan rahotan cewa Amurka zata kawo Khari Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa, kasar ta kulle iyakokinta da Najeriya bayan bayyanar Rahoton cewa Amurka na iya kawo Hari Najeriya. Kafar Zagazola Makama ce ta ruwaito cewa shugaban soji na kasar Chadi Muhammad Idris Derby Itno ne ya bayar da wannan sanarwar. Yace sojojin kasarsa su tare iyakar kasar da Najeriya saboda ana tsammanin 'yan Bindiga zasu iya tserewa can yayin da Amurka ke shirin kawo hari Najeriya. Hakanan sanarwar tace kasar Chadi ba zata bari wasu 'yan kasar waje su shigar mata kasa ba.