Wannan Bidiyon na yanda wasu daga kudancin Najeriya suka yi murnar saukar Qur'ani ya jawo cece-kuce sosai.
An gansu suna sumbatar juna.
https://www.tiktok.com/@elegance.eventandparty/video/7584219580126465300?_t=ZS-92I8xu5PKl7&_r=1
Tauraron Mawakin Hausa da akawa Nadin Sarkin Wakar Qasar Hausa, Alhaji Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, daga yanzu ko sauraren waka sai da izininsa.
Rarara yace idan mutum ya saurara sau daya biyu sai ya dakata ya nemi izininsa.
https://www.tiktok.com/@ibrahimwisdomtv/video/7584542635965123861?_t=ZS-92I3mW6yftB&_r=1
Baffa Hotoro yawa Dr. Hussain Kano wankin babban bargo kan kalaman da yayi na cewa yana son shiga Aljannah ba tare da ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba.
Baffa Hotoro yace wannan magana akwai wauta, Hauka, da Jahilci a cikinta.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyon martani da yawa Dr. Hussain Kano.
Yace ko Annabi Ibrahim AS sai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi, duk da kasancewar Annabi Ibrahim AS badadin Allah ne
Yace dan haka kuskurene tunanin wai me laifi ne kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama ko kuma ace wanda suka cancanci shiga wutane kadai Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) zai ceta a ranar tashin qiyama.
Yace dan haka suna baiwa Dr. Hussain Kano shawarar ya daina wa'azi, ya koma yayi karatu tukuna.
https://www...
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanonin dake samar da wutar lantarki na Najeriya na fama da karancin gas wanda ake amfani dashi wajan samar da wutar.
Dalilin haka kuwa Najeriya na iya fadawa cikin duhu a yi bukukuwan kirsimeti babu wutar lantarki.
Kamfanonin rarraba wutar na Enugu da Fatakwal sun sanar da abokan hukdarsu cewa sun rage yawar wutar da suka baiwa mutane saboda wannan matsala.
Wata majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng da wannan labarin.
Hakan na faruwa ne saboda gazawar gwamnati waja biyan bashin da kamfanonin iskar gas din ke bi wanda rahoton yace idan ba'a biya ba ka iya sa kasar ta fada Duhu.
Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, Babban me baiwa shugaban kasa, Shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu da kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke hana shugaban kasar samar da tsaro yanda ya kamata.
Yace Ribadu kowane bafulatani na Najeriya na da lambar wayarsa.
Ya nemi shugaban kasar ya canjasu.
https://twitter.com/Chude/status/2000995541656986105?t=CJ4K9Ld4wGdyDgivJ9REAg&s=19
Wani mutum da ya bayyana ya soki kanawa saboda Qàshè wanda ake zargi da cire Makogoron Ladani a Hotoro.
Yace da aka kamashi ba kasheshi ya kamata a yi ba, kamata yayi a mikashi hannun hukuma ta yi bincike.
Yace ta hanakane za'a gano duk masu alaka dashi amma yanzu gashi an kasheshi an koma ana ta zargin wai waye ya aikosshi.
Yace shi yanzu duka shi da ladanin yakewa addu'a.
https://www.tiktok.com/@nationalbestblogger/video/7584503733317422392?_t=ZS-92HUYUe04B7&_r=1
Tauraron mawakin Arewa, Naziru Sarkin Waka, yace bai yi Hira da Freedom Radio ba akan sarautar Sarkin Waka da aka baiwa Rarara ba.
Yace idan da gaske ya fadi cewa sarautar irin ta Alutace ai ya karawa abin daraja ne tunda masu ilimi ne ke Aluta.
Yace idan amincewa da sarautar da aka baiwa Rarara zata sa a shafa musu Lafiya, yayi mubaya'a ya amince.
https://vt.tiktok.com/ZSPmqvYq2
Shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi martani kan zargin da Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya masa na cewa ya kashe dala Miliyan $7 wajan biyawa 'ya'yansa kudin makaranta.
Yace 3 daga cikin 'ya'yansa sun samu scholarship inda aka biya musu kaso me yawa na kudin karatunsu.
Sannan yace akwai kudaden da mahaifinsa wanda dan kasuwane ya tara dan ilmin 'ya'ya da jikoki sannan 'yan uwa na taimakawa hakanan shima yana taimakawa 'ya'yan nasa.
Yace ta hakane ya samu ilmantar da 'ya'yan nasa amma ba sata yayi ba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya saka karin kasashe 15 da ya hanasu shiga kasar Amirkar.
Kasashen sune:
AngolaAntigua and BarbudaBeninCote d’IvoireDominicaGabonThe GambiaMalawiMauritaniaNigeriaSenegalTanzaniaTongaZambiaZimbabwe
Yace ya dauki wannan mataki ne dan inganta tsaron kasar Amirkar.
Saidai Haramta shigar bata dindin bace ta wucin gadi ce.