Matatar Ɗangote ta sake rage farashin man fetur
Matatar Man Ɗangote ta sake rage farashin man fetur daga naira 890 a kan lita zuwa naira 825 - wato ragin naira 65 kenan a kan kowace lita ga 'yan kasuwa.
A wata sanarwa da ta kamfanin ya fitar a yau Laraba, ya ce ragin zai fara aiki ne daga gobe Alhamis, 27 ga watan nan na Fabarairun 2025.
kamfanin ya ce ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa al'umma Najeriya, yayin da suke shirin fara azumin watan Ramadana, tare kuma da tallafa wa shirin Shugaba Tinubu na neman farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar rage wa al'ummar ƙasar nauyin kuɗaɗe da ke kansu.
Wannan shi ne karo na biyu da matatar take rage farashin man fetur a watan na Fabarairun 2025, inda da farko ta yi ragin naira 60.
Haka kuma a watan Disamba na 2024 lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, matatar ta rage farashin ...







