Saturday, January 3
Shadow
Da Duminsa: A karin Farko, Kwankwaso ya jefawa Abba Gida-Gida Magana

Da Duminsa: A karin Farko, Kwankwaso ya jefawa Abba Gida-Gida Magana

Duk Labarai
A karin farko tunda aka fara maganar cewa Abba Kabir Yusuf, Gwanan Kano zai koma jam'iyyar APC, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya jefawa Abban magana Kwankwaso a wajan taron ya jefawa Abban Magana inda yace babu wanda ke Cin Amanarsu ko ya musu Butulci yayi nasara. Kwankwaso yace yayi mamakin ganin yawan mutanen da ya tara a waja taron nasa inda yace yayi tsammanin duk sun koma bayan Abba. https://twitter.com/ADCVanguard_/status/2005997894755664328?t=pUPjgKU6fLPrXGApU6VvDw&s=19
Wannan cibiyar Koyar da kimiyya da Fasahar da kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya gina akan Sama da Naira Miliyan 300 a mazabarsa ta jawo cece-kuce

Wannan cibiyar Koyar da kimiyya da Fasahar da kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya gina akan Sama da Naira Miliyan 300 a mazabarsa ta jawo cece-kuce

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya gina cibiyar kimiyya da fasaha a Etim Ekpo dake jihar Akwa-Ibom akan kudi sama da Naira Miliyan 300. Saidai da yawa na ganin cewa, kudin sun yi yawa, bai kamata ace karamin gini kamar wannan ya cinye wadannan kudade ba. Da yawa dai sun ce basu yadda an kashe wannan makudan kudade wajan gina wannan cibiyar ba. https://twitter.com/afrisagacity/status/2005979617379967110?t=vs96Z8YSC4t2O5WbAU7ZHA&s=19 https://twitter.com/monitng/status/2005749623860912171?t=zoDev-gpZObCWixmYrCGjw&s=19
Peter Obi ya bayyana cewa, Abin takaici ne ganin Babu Motar Kwana-Kwana data je wajan da Dan Damben Najeriya, Anthony Joshua yayi Khàdàrì

Peter Obi ya bayyana cewa, Abin takaici ne ganin Babu Motar Kwana-Kwana data je wajan da Dan Damben Najeriya, Anthony Joshua yayi Khàdàrì

Duk Labarai
Peter Obi ya bayyana rashin jin dadin rashin ganin Motar Kwana-kwana a wajan hadarin da ya auku da dan damben Najeriya, Anthony Joshua. Ya bayyana cewa, Abin takaici ne faruwar hakan. Peter Obi ya mai fatan samun sauki, saidai lamarin ya jawo cece-kuce sosai. https://twitter.com/PeterObi/status/2005717751999172959?t=oN4nhLLF5KybGkAI5ENLuw&s=19
Wani Inyamuri yayi mamakin wai ta yaya Atiku ke iya ci gaba da rayuwar Facaka haka duk da cewa shekaru 18 kenan da ya sauka daga Matsayin mataimakin shugaban kasa?

Wani Inyamuri yayi mamakin wai ta yaya Atiku ke iya ci gaba da rayuwar Facaka haka duk da cewa shekaru 18 kenan da ya sauka daga Matsayin mataimakin shugaban kasa?

Duk Labarai
Wani inyamuri yace akwai mamakin ta yanda Atiku ke iya ci gaba da rayuar Facaka duk da cewa, shekaru 18 kenan da saukarsa daga mukamin mataimakin shugaban kasa. Ya bayyana hakane bayan wallafa Bidiyon Tawagar Motocin Atiku. Yace wai bai kamata a yadda da Atiku a matsayin shugaban kasa ba dan ba lallai yawa mutane Adalci ba. https://twitter.com/afrisagacity/status/2005941401792508335?t=EettuUe6LeKlFOYfRawzBg&s=19
Har na tuna sanda Abubakar Malami ya rika bani Wahala kullun ina kotu, yau gashi shi da iyalinsa a gidan yari>>Inji Sanata Dino Melaye

Har na tuna sanda Abubakar Malami ya rika bani Wahala kullun ina kotu, yau gashi shi da iyalinsa a gidan yari>>Inji Sanata Dino Melaye

Duk Labarai
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, ya tuna irin wahalar da Abubakar Malami ya bashi a lokacin yana ministan shari'a. Yace kullun suna kotu. Yace amma ya godewa Allah yanzu gashi Malami ne a Gidan yari da iyalinsa, Yace yana masa fatan Alheri. https://twitter.com/_dinomelaye/status/2005956277776654452?t=LXRo54pb-tkXuTK69whJEw&s=19
Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta kori shugabanta na Kano

Da Duminsa: Jam’iyyar NNPP ta kori shugabanta na Kano

Duk Labarai
Rahotanni daga Kano na cewa, Jam'iyyar NNPP a jihar ta kori shugabanta, Hashim Suleman Dungurawa. NNPP tace ta kori Hashim Suleman Dungurawa ne saboda zargin kawo rarrabuwar kai a cikin jam'iyyar. Shugaban jam'iyyar NNPP a Mazabar Gargari dake karamar hukumar Dawakin Tofa, Shuaibu Hassan ne ya bayyana haka ga BBChausa. Korar shugaban NNPP din ta fara ne daga ranar 30 ga watan Disamba. Hakan na zuwane a yayin da ake rade-radin Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC.
Da Duminsa: Kotu ta aika Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami, da Dansa da matarsa gidan yarin Kuje

Da Duminsa: Kotu ta aika Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami, da Dansa da matarsa gidan yarin Kuje

Duk Labarai
Rahotanni daga Abuja na cewa babbar kotun tarayya dake Abuja ta aika da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami da dansa, Abubakar Abdulaziz Malami da matarsa kotu. EFCC ta gurfanar dasu 3 ne tana zarginsu da almundahanar kudade da aikata laifuka 16. Saidai duk sun musanta wannan zargi da ake musu. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2005951870141927742?t=9X9j8HocHDeVrd_BSpFToA&s=19 Kotun ta kuma saka ranar January 2, 2026 dan sauraren bukatar Belin da Malami da iyalinsa suka nema. https://twitter.com/channelstv/status/2005950377061982698?t=rKoYsDwfPI02QJGx0ZvjtA&s=19
Su Kwankwaso da Abba suna son shiga APC ne dan su lalata mana ita>>Inji Ganduje

Su Kwankwaso da Abba suna son shiga APC ne dan su lalata mana ita>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa su Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf zasu shiga APC ne dan su lalatata. Saidai yace abinda basu sani ba shine ba zasu barsu ba. Yace idan suna tunanin suna Yaudarar Talakawa, su gogaggun 'yan siyasa ne ba zasu iya yaudararsu ba. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2005922151933571520?t=4U2ryTNwQPRMV3Y2ayJb9g&s=19