Saturday, December 6
Shadow
Da Duminsa: A karo na biyu, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace ba fa zai ci gaba da ganin cin kashin da akewa Kiristoci a Najeriya ba sai ya kawo musu dauki

Da Duminsa: A karo na biyu, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace ba fa zai ci gaba da ganin cin kashin da akewa Kiristoci a Najeriya ba sai ya kawo musu dauki

Duk Labarai
Donald Trump ya jaddada cewa Amurka za ta iya tura dakaru Najeriya ko kuma kaddamar da hare-hare domin hana abin ya kira kisan Kiristoci da ake yi. Ya shaida wa manema labarai cewa ba zai bari a ci gaba da kisan ba. "Ana kashe kiristoci da dama a Najeriya kuma adadi da yawa, ba zan bari a ci gaba ba." in ji Trump. Fadar gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi maraba da samun hadin kan Amurka wajen yaƙi da mayaka masu tsattsaran ra'ayin addini tare da musanta cewa mayakan sun fi kashe kiristoci. A watan da ya gabata Amurka ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da take da damuwa da su kan take ƴancin addini. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta'adda mas...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara kasar Amurka ranar Talata dan shawo kan kasar karta Afkawa Najeriya da Khare-Khare

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara kasar Amurka ranar Talata dan shawo kan kasar karta Afkawa Najeriya da Khare-Khare

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai kai ziyara kasar Amurka dan jawo hankalin kasar da fahimtar da ita halin da ake ciki a Najeriya ba kamar yanda ake cewa ana yiwa Kiristoci Khisan Khiyashi ba. Rahoton yace Shugaban kasar Amurkar ya wakilta mataimakinsa, JD Vance ya gana da shugaba Tinubu a yayin ziyarar. Kafar Sahara Reporters ce ta bayyana haka inda tace ta samu bayanan ne daga fadar shugaban kasa Bola Tinubu. Hakan na zuwane a yayin da ake tsaka da fargabar kawo hari na kasar Amurka a Najeriya.
Ku yi hakuri, Akwai Yiyuwar Shugaban kasar mu na da Tabin hankali, Wani Ba’murke ya gayawa ‘yan Najeriya

Ku yi hakuri, Akwai Yiyuwar Shugaban kasar mu na da Tabin hankali, Wani Ba’murke ya gayawa ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Wani ba'amurke kuma dan Jarida, me suna Ron Filipkowski ya bayyana cewa akwai yiyuwar shugaban kasarsu, Donald Trump na da tabin hankali. Ya bayyana hakane a yayin da yake martani game da barazanar kawo hari Najeriya da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi. https://twitter.com/RonFilipkowski/status/1984792639607091558?t=5-p17OuQfTRrXGwoPH-gvw&s=19 Barazanar ta Trump dai ta tayar da kura sosai inda akai ta mata fassara daban-daban inda wasu ke ganin ba maganar Khisan Kiristoci ce zata kawoshi Najeriya ba, akwaidai wata manufa.
Da Duminsa:Turawa sun fara kiran cewa a Rhaba Najeriya saboda ta kasa yiwa kowane bangare Adalci

Da Duminsa:Turawa sun fara kiran cewa a Rhaba Najeriya saboda ta kasa yiwa kowane bangare Adalci

Duk Labarai
Bayan da Kasar Amurka ta farawa Najeriya katsalandan akan harkar tsaro da sunan ana yiwa Kiristoci Khisan Kiyashi, Har shugaban kasar Trump yayi barazanar kawo hari, Mutane na ta tunanin abinda Kasar ke son cimmawa a Najeriya. Wani bature wanda wakili ne a kungiyar NATO, Gunther Fehlinger-Jahn ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kokarin ganin ya yi fafutuka da hada kan kasarsa amma Najeriya bata amfanar kowa da kowa. Yace dan haka raba kasar shine Mafita. https://twitter.com/GunterFehlinger/status/1984891493979685072?t=8DZ4YRQ5pkNHe1QBDvF2SA&s=19 Da yawa dai sun bayyana mamaki da jin wannan magana da ta fito daga bakin wannan bature inda Kiristoci da yawa ke fadar cewa ba abinda suke nema kenan ba.
Dr. Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta nemi Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya idan kuma yaki janyewa Najeriya ta yanke alakar jakadanci da Amurka

Dr. Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta nemi Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya idan kuma yaki janyewa Najeriya ta yanke alakar jakadanci da Amurka

Duk Labarai
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya. Yace shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka ya bukaci kasardu ta janye barazanar da tawa Najeriya. Sheikh Gumi yace kasa bata fi kasa ba, Najeriya kasa ce me con gashin kanta dan haka bai kamata ta tsaya ana gaya mata abubuwan da basu kamata ba. Sheikh Gumi yace idan Trump yaki janye kalaman nasa, Najeriya ta yanke huldar jakadancin da Amurkar. Ya kuma baiwa Gwamnatin shawarar cewa, ta fara neman wasu abokan huldar kasuwanci da sayen makamai bayan Amirka.
Wasu na zargin matatar man Dangote ce data dauko hanyar Zama babu irinta a Duniya ke tsolewa Thurawa ido shine suke son ganin sun daidaita Najeriya

Wasu na zargin matatar man Dangote ce data dauko hanyar Zama babu irinta a Duniya ke tsolewa Thurawa ido shine suke son ganin sun daidaita Najeriya

Duk Labarai
Tun bayan da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ana kashe kiristoci da yawa a Najeriya ne da yawa ke ta sharhi da bayyana abinda suka fahimta game da lamarin. Wasu sun bayyana cewa suna zargin ci gaban da matatar man Dangote ta dauko ne inda nan da wani Lokaci Dangoten yace zata zama ta daya a Duniya wajan yawan tace man Fetur da ganga Miliyan 1.4 a kullun shine ya hana Turawa sakat suke kokarin ganin sun Lalata kasar. A gefe guda kuma wasu na ganin cewa Arzikin da Allah yawa Najeriya ne Turawan ke son zuwa su kwasa. Wasu dai na cewa, zuwan Amurka Najeriya da sunan yakar 'yan ta'adda ba abin Alheri bane musamman lura da irin yanda suka lalata kasashen Libya, Afghanistan, Syria da sauransu.
Ku daina Murna, Trump ba ruwanshi da Kirista ko Musulmi kowa zai dandana kudarsa idan ya kawo khari Najeriya>>Sowore ya gayawa ‘Yan Uwansa Kirista

Ku daina Murna, Trump ba ruwanshi da Kirista ko Musulmi kowa zai dandana kudarsa idan ya kawo khari Najeriya>>Sowore ya gayawa ‘Yan Uwansa Kirista

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Sahara reporters kuma dan Gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Kiristoci su daina murna saboda Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yace zai kawo hari dan Khashye masu yiwa kiristoci Khisan Qare dangi. Sowore yace abin zai shafi kowa ne. Shugaban kasar Amurka Donald Trump yace ba zasu zuba ido suna ganin ana kashe Kiristoci ba, yacw idan Gwamnati bata dauki mataki akan lamarin ba zasu dauki mataki ta hanyar soji.
Da Duminsa: Mun fara shirye-shiryen kai Fharmaki Najeriya>>Inji Sakataren Yhaqi na kasar Amurka

Da Duminsa: Mun fara shirye-shiryen kai Fharmaki Najeriya>>Inji Sakataren Yhaqi na kasar Amurka

Duk Labarai
Sakataren Yaki na kasar Amurka, Pete Hegseth ya bayyana cewa sun fara shirin afkawa masu khashe Kiristoci a Najeriya. Yace muddin ba'a dakile matsalar ba suna nan shigowa su Shekye masu Khashe kiristocin. Ya bayyana hakane a matsayin martanin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya basu na cewa su shirya kai hari Najeriya idan Gwamnatin Najeriya bata hana kisan da akewa kiristoci ba.