Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa
Mutane huɗu sun ƙone ƙurmus wasu goma kuma sun ji raunuka yayin da wata mota ƙirar bas (Hummer) ta kama da wuta a garin Gwaram da ke jihar Jigawa.
Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a jiya Asabar a kusa da makarantar sakanadare ta haɗaka ta gwamnati ta 'yammata da ke garin na Gwaram (Government Girls Unity Secondary School )
Wata sanarwa da kakakin 'yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta nuna cewa motar ta tashi ne daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
Sanarwar ta ce, ''motar na ɗauke ne da fasinja 44, da suka haɗa da manya 25 da yara 19.''
Kakakin 'yansandan ya ce, wutar ta kama ne sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa ...







