Dalla-Dalla: Ji Yanda Kawu sumaila ya fadi dalilan da suka sa ya koma APC
Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam'iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam'iyyarsa ta NNPP a jihar Kano.
A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano.
A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al'ummar mazaɓarsa.
Ya ce ''Wasu daga cikin dalilan da za su sa mu fice shi ne yankin da muka fito. Ya za mu iya samar wa mutanen yankin mu wani abu da zai amfanar da su, kuma ai ita siya...








