Sunday, July 12
Shadow
An samu babbar Baraka a jam’iyyar APC inda wasu suka fito suka ce basu tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

An samu babbar Baraka a jam’iyyar APC inda wasu suka fito suka ce basu tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Tsohon Ministan Shari'a na Najeriya, Dakta Abubakar Malami, SAN, ya yi watsi da iƙirarin da wasu ƴan tsohuwar jam'iyyar CPC - da ta narke cikin haɗakar APC - suka yi na nesanta tsohuwar jam'iyyar daga ficewa daga haɗakar. A farkon makon nan ne wani tsagin tsohuwar jam'iyyar CPC ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Almakura suka yi taro a Abuja, inda suka jaddada goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Tinubu tare da nesanta kansu daga ficewa daga APC. Daga cikin waɗanda suka harci taron har da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da tsohon ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu da Hon Farouk Adamu Aliyu, tsohon ɗan majalisar daga jihar Jigawa da wasu ƙusushin tsohuwar CPCn. To sai toshon Ministan ya yi watsi da wannan iƙirari da tsagin Almakuran suka yi, yana mai...
PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba – Wike

PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba – Wike

Duk Labarai
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar, PDP ba ta da kyakkyawan shiri da tsarin kayar da APC a zaɓen 2027 ba. Yayin da yake jawabi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Juma'a, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce a yanayin da jam'iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ba za a ce ta shirya wa zaɓen 2027, saboda rikicin shugabanci da jam'iyyar ke ciki. ''PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba, wannan a bayyane yake. Ga yadda suke tafiya a yanzu rikicin jagoranci na ci gaba da yi wa jam'iyyar tarnaƙi'', in ji shi. A baya-bayan nan dai wasu daga jam'iyyun hamayyar ƙasar ciki har da PDp na ƙoƙarin samar da wata haɗaka domin tunkarar APC a 2027. To sai dai da alama tafiyar na ci gaba da fuskantar tasgaro, saboda muradun wasu ƴansiyasar.
Kalli Hotuna yanda aka jìkkàtà jami’an NDLEA yayin da suka kai samamen kwace miyagun Kwàyòyì a Abuja

Kalli Hotuna yanda aka jìkkàtà jami’an NDLEA yayin da suka kai samamen kwace miyagun Kwàyòyì a Abuja

Duk Labarai
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi, NDLEA sun fuskanci matsalar harin kwantan Bauna da aka kai musu yayin da suka kai samame kan wasu masu harkar miyagun kwayoyi a Jahi dake Abuja. Jami'an NDLEA sun kai samamenne bayan da suka samu bayanan sirri game da harin inda suka shiga wani kango suka kwace kwayoyin. Saidai a yayin da suke shirin ficewa daga cikin kangon, maharan sun bude musu wuta inda aka jikkata ma'aikatan hukumar su 3. Daya daga cikin ma'aikatan an sameshi ne a kirjinshi inda daya kuma sauran aka samesu a kafa. Tuni dai aka garzaya dasu Asibiti dan basu kulawa ta musamman. Shugaban hukumar, Brig Gen Mohamed Buba Marwa (Rtd) ya jinjinawa ma'aikatan asibitin Abuja bisa kulawar da suka baiwa ma'aikatansa inda kuma yayi magana da wadanda aka jikka...
FASAHA: Matashi Ya Kirkiri Na’urar Dake Gano Makamai Ko Ma’adanai A Cikin Dakika Daya

FASAHA: Matashi Ya Kirkiri Na’urar Dake Gano Makamai Ko Ma’adanai A Cikin Dakika Daya

Duk Labarai
FASAHA: Matashi Ya Kirkiri Na'urar Dake Gano Makamai Ko Ma'adanai A Cikin Dakika Daya. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matashi dan asalin kljihar Kano mai suna Khalifa Aminu ya kirkiri na'urar dake gano makamai da ma'adinai dake ƙarƙashin ƙasa. Na'urar za ta iya gano makamai waɗan da aka binne akarkashin kasa, da kuma ma'adanai dake ƙarƙashin ƙasa. Wasu daga cikin abubuwan da na'urar zata iya gano wa, sun haɗa da, Gün, Bôóm, Bûllet dai sauran ma'adinai dake ƙarƙashin ƙasa. Daga Ibrahim Dau Dayi...
Ƴànbìndìgà sun kàshè mutane biyu tare da sàcè mutum ɗaya a Kano

Ƴànbìndìgà sun kàshè mutane biyu tare da sàcè mutum ɗaya a Kano

Duk Labarai
Wasu da ake zargin ƴan fashin jeji ne sun kai hari garin Faruruwa da ke Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a kasuwar garin da misalin karfe 7 na dare a jiya Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan me uwa da wabi. Wani shaida, Ibrahim Faruruwa, ya ce maharan sun yi yunkurin sace wani hamshakin dan kasuwa, Alhaji Haruna Halilu, sai dai ba ya shagon nasa a lokacin harin. Ya ce: “Da basu samu Alhaji Haruna ba, kawai sai suka sace dansa, Mas’ud.” Ya kara da cewa maharan sun kashe mutane biyu — wato Alhaji Rabiu Faruruwa da Sahabi Dankwaro a yayin harbe-harben da su ka riƙa yi. Wani mazaunin garin, Abubakar Hamza Adam, ya ce dan uwansa karami, ...
Ji dalilin da ya sa farashin fetur bai faɗi ba a Najeriya ba duk da faɗuwar sa a kasuwar duniya

Ji dalilin da ya sa farashin fetur bai faɗi ba a Najeriya ba duk da faɗuwar sa a kasuwar duniya

Duk Labarai
Dillalan man fetur da masana sun bayyana dalilan da suka sa ba a ganin sauƙin kirki na man fetur a gidajen mai duk da faɗuwar fashin gangar mai a kasuwar duniya. Ƴan Najeriya a yanzu na sayen man fetur tsakanin N940 zuwa N970 a Abuja babban birni ƙasar. Farashin gangar ɗanyen mai ya sauka a kasuwar duniya sakamakon yakin kasuwanci da shugaba Trump na Amurka ya ƙaddamar kan China da sauran ƙasashen duniya, inda ake sayar da ganga kan dala 61 zuwa 65. Kodayake a ranar Laraba farashin ɗanyen man ya ƙaru bayan sabbin takunkuman Amurka kan man Iran da ake shigar wa China. Rikicin haraji ya rage buƙatuwar man fetur a duniya saboda raguwar samar da abubuwa, dalilin da ya sa man fetur ya yi arha a Najeriya da sauran ƙasashe. Sai dai kuma wasu na ganin ya kamata sauƙin ya fi wanda ak...
Mun kusa ƙaddamar da haɗakar kawar da APC – Ƴan adawa

Mun kusa ƙaddamar da haɗakar kawar da APC – Ƴan adawa

Duk Labarai
Manyan ƴan siyasar Najeriya da ke jagorantar shirin yin haɗaka tsakanin jam'iyyun hamayya domin tunkarar APC a zaɓen 2027, sun mayarwa ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP martani, a kan matsayar da gwamnonin suka ɗauka cewa ba su goyon bayan ƙulla duk wata haɗaka da za ta fitar da su daga PDP. Gamayyar ƴan adawar da ta haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da dai sauran ƴan siyasa, ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ƙulla sabuwar haɗakar siyasa da za ta ceto Najeriya daga mulkin APC. Ɗaya daga cikin jagororin tafiyar ƙulla sabuwar haɗakar siyasar ta Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma, Sali...
‎Hukumar tace fina-finai ta Kano ta fara kamen Baburan Adai-daitasahu masu ɗauke da hotuna da rubuce-rubuce na rashin ɗa’a

‎Hukumar tace fina-finai ta Kano ta fara kamen Baburan Adai-daitasahu masu ɗauke da hotuna da rubuce-rubuce na rashin ɗa’a

Duk Labarai
‎‎‎‎Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta kaddamar da wani sabon atisayen kama baburan adai-daita sahu da ke dauke da hotunan batsa da rubuce-rubuce marasa tarbiyya a manyan titunan jihar.‎‎Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ne ya tura jami’an sa don gudanar da wannan aiki, inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin nauyin da ke kan hukumar na tabbatar da tsaftar hotuna da rubuce-rubuce da ke bayyana a fili ga al’umma.‎‎Sanarwar ta fito ne daga Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano.‎‎‎“Aikinmu shi ne tabbatar da cewa babu wani hoto ko rubutu da zai cutar da tarbiyya ko dabi’un al’umma, musamman matasa, ya fito fili ba tare da tantancewa ba,” in ji Abba El-Mustapha.‎‎‎Daraktan Sashen Dab’i na hukumar, Alhaji Abub...
Wani matashi da ya kàshè mutane wajen ƙwacen waya ya kai kan sa wajen ƴansanda a Kano

Wani matashi da ya kàshè mutane wajen ƙwacen waya ya kai kan sa wajen ƴansanda a Kano

Duk Labarai
Wani matashi mai shekaru 20 da ya amsa da bakin da cewa ya kashe mutane wajen ƙwacen waya a gurare daban-daban ya miƙa kansa da kansa ga rundunar ‘yansanda ta jihar Kano. Wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Umar Auwal, mai lakabi da ‘Abba Dujal,’ mazaunin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, ya amsa cewa yana da hannu a laifukan kisan kai, fashi da makami da kuma sata, musamman na babura da wayoyin hannu. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa miƙa kansa da Auwal ya yi ya biyo bayan zurfafa samame da rundunar ke yi a maboyar ‘yan ta’adda a jihar. Kiyawa ya ce wannan mataki yana daga cikin kokarin da rundunar ke yi na dawo da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Auwal ya amsa cewa ya daba wa wani...