Sunday, April 26
Shadow
A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

A karin farko, Shugaba Tinubu ya sakawa dokar haramtawa sojojin Najariya yin Luwadi, Madigo da shan giya

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar haramta yin luwadi, Madigo da daudu ko saka kayan mata, da yin zane a jiki wanda aka fi sani da Tattoo a gidan soja. Hakanan kuma dokar ta haramtawa sojojin huda jikinsu, irin su hudar kunne ko hanci da sauransu, sannan ba'a yadda soja ya sha giya a bakin aiki ko kuma ko da baya bakin aiki. Wannan na kunshene a cikin sabuwar dokar aikin soja da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanyawa hannu a watan Disamba na shekarar 2024. Hakanan sabuwar dokar ta haramtawa sojojin shiga kungiyar asiri ko kuma harkar siyasa.
Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan ‘yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda ‘yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan ‘yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda ‘yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Duk Labarai
Lawan Wakilbe, kwamishinan ilimi, da kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire a Jihar Borno, ya yi gargadi kan yawaitar karuwanci tsakanin tsofaffin wadanda kungiyar B0k0 Hàràm ta sace. TheCable ta rawaito cewa Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da Hamsatu Allamin, shugabar cibiyar Allamin Foundation for Peace, ta kai masa a jiya Juma’a a Maiduguri. Wakilbe ya ce an fi samun irin waɗannan matsalolin a ƙananan hukumomin Bama, Banki, da Gwoza. Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda Boko Haram din su ka saki na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su saboda sun fuskanci hakan tun a lokacin da raunin da su ke hannun ƴan ta’addan. Ya yi kira ga haɗa hannu waje ɗaya domin ceto ire-iren yaran.
Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke – Djimon Hounsou

Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke – Djimon Hounsou

Duk Labarai
Shahararren jarumin Hollywood din nan Djimon Hounsou ya bayyana cewa ya na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da sana'ar fim da ya ke yi sama da shekaru ashirin. A wata hira da CNN a wani shirin su na matasan Afirka, a yau Asabar, Hounsou ya bayyana cewa ya na ganin cewa ana yi masa ƙwange a albashi kuma har yanzu ya na fama da talauci. "Har yanzu ina fama yanayi a rayuwa. Na kasance cikin harkar shirya fina-finai sama da shekaru ashirin, tare da lashe lambobin girma na Oscar guda biyu da fina-finai da yawa, amma duk da haka, har yanzu ina fama da rashin kuɗi. Babu shakka ƙwangen albashi ake yi min," inji shi. Wannan tonon silili ya ba wa mutane da yawa mamaki, ganin irin nasarorin da ya samu, gami da lashe lambar yabo ta Academy sakamakon kwazon saba fim din 'Blood D...
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya karkatar da makudan kudade Naira Tiriliyan N2.68tn, da dala Miliyan $9.77m kuma an gayyaceshi dan a yi bincike yaki zuwa

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya karkatar da makudan kudade Naira Tiriliyan N2.68tn, da dala Miliyan $9.77m kuma an gayyaceshi dan a yi bincike yaki zuwa

Duk Labarai
A ci gaba da zargin karkatar da kudaden kasa da suka saka Najeriya cikin halin kaka nikayi, ana zargin kamfanin mai na kasa, NNPCL da karkatar da Naira Tiriliyan N2.68tn, da dala Miliyan $9.77m a cikin shekaru 4 da suka gabata. Babban me binciken hada-hadar kudi na kasa ne yayi wannan zargi bayan kammala bincike akan yanda kamfanin na NNPCL ya gudanar da ayyukansa. Tuni babban me binciken na kasa ya aikewa da majalisar tarayya da sakamakon bincikensa inda yace abinda kamfanin man na kasa, NNPCL ya aikata ya sabawa dokar kasa data haramta karkatar da kudaden kasa. Duk da wadannan zarge-zargen, kamfanin man na kasa, NNPCL har yanzu yaki ya yi magana ko ya bayar da amsa akan zarge3da ake masa.
Duk da ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 Najeriya ta kasa samar da ingantacciyar wutar Lantarki

Duk da ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 Najeriya ta kasa samar da ingantacciyar wutar Lantarki

Duk Labarai
A cikin shekaru 4 da suka gabata, Najeriya ta ciyo bashin Dala Biliyan $3.2 dan gyaran wutar lantarki amma duk da haka ta kasa samar da wutar me karfin da yafi 4,500mgwt da zata wadatar da mutanen kasar. Bankin Afrika da Bankin Duniya da Bankin Japan ne suka baiwa Najeriya wadannan kudade. Saidai duk da wadannan makuda kudade babu alamar canji kan matsalar wutar. Har yanzu dai wuta me karfin Megawatts 4,743MW ne Najeriya ke samarwa wanda tun shekaru 3 da suka gabata haka lamarin yake bai canja ba. A shekarar 2024, sau 12 tashoshin wutar lantarkin Najeriya na samun matsala.
Karanta Jihohin da suka fi biyan masu Gàŕķùwà da mutane kudin fansa da yawa

Karanta Jihohin da suka fi biyan masu Gàŕķùwà da mutane kudin fansa da yawa

Duk Labarai
Jihohin Kudu maso gabas, watau jihohin Inyamurai ne suka fi biyan masu garkuwa da mutane kudi da yawa dan karbo 'yan iwansu da aka yi garkuwa dasu. A gaba daya Najeriya, an biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira Biliyan 1.048 a matsayin kudin fansa inda jihohin kudu maso gabas na inyamurai suka biya jimullar Naira Miliyan dari hudu da sha tara 419.2 Million. Wannan shine kaso 40 na jimullar kudij fansar da aka biya a Najeriya. A jihar Anambra ne aka fi biyan kudin fansar inda aka biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira miliyan 350.2 a jihar. Mutanen jihar Imo sun biya masu garkuwa da mutanen Naira Miliyan 39. Sai jihar Abia data biya Jimullar Naira Miliyan 25 ga masu garkuwa da mutanen, mutanen jihar Enugu sun biya Naira Miliyan 4 ne ga masu garkuwa da mutanen dan k...
Mahaukaciyar gobara da ba’a taba ganin irin taba ta babbake gidaje dubu goma a birnin Los Angeles na kasar Amurka, mutane 11 sun mùtù

Mahaukaciyar gobara da ba’a taba ganin irin taba ta babbake gidaje dubu goma a birnin Los Angeles na kasar Amurka, mutane 11 sun mùtù

Duk Labarai
Wutar daji a birnin Los Angeles na kasar Amurka ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 11. Hukumomin lafiya na birnin Los Angeles sun ce 5 daga cikin anda suka mutu sun mutu ne a yankin Palisades sai kuma guda 6 sun mutu ne a yankin Eaton. Har yanzu dai mahukunta basu san dalilin tashin wannan gobara ba. Hakanan an samu karancin ruwan kashe gobarar kuma ma'aikatan kashe gobarar ma sun yi karanci inda makwauciyar kasar Amurka, Mexico ta aike da taimakon masu kashe gobara zuwa birnin na Los Angeles. Ana dai zargin mahukuntan birnin na Los Angeles, Musamman Gwamnan California, Gavin Newsom da Magajiyar garin da sakaci wajan rashin yin tanadin yanayi irin wannan inda ake zargin basu dauki matakin adana ruwan sama da aka samu me yawa ba dan kashe gobara irin wannan ba. Hakanan an zargi...