Monday, March 9
Shadow
Nan da shekarar 2027 zamu gyara wutar lantarki ta yanda za’a rika samunta tsawon awanni 20 kullun>>Gwamnatin Tarayya

Nan da shekarar 2027 zamu gyara wutar lantarki ta yanda za’a rika samunta tsawon awanni 20 kullun>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace nan da shekarar 2027 zata samar da wutar Lantarki ta awanni 20 kullun. Saidai tace sharadin hakan shine sai ta samu maau zuba jari a bangaren Fetur da iskar gas wanda a yanzu babu su sosai. Me baiwa shugaban kasa shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana haka a wata ziyara da ta kai kasar Africa ta kudu. Tace za'a mayar da hankali ne wajan samarwa Birane da masana'antu karfin wutar lantarkin.

Maganin sanyi kowane iri

Magunguna
MAGANIN SANYI KOWANE IRI INSHA ALLAH Ga masu fama da ciwon sanyi kowanne iri ne insha Allah in suka bi wannan hanya zasu samu sauki,ko masu yawan tari da nura da ciwon gobobi da rikewar baya da kwankwaso da kaikayin jiki dadai sauran illolin da sanyi ke haifar wa. ABIN DA ZAA NEMA. Garin Tafarnuwa 2.Nono mekyau madara ta ruwa mekyau) YADDA ZAA HADA Zaa samu garin Tafarnuwa mai kyau sai a debi chakali daya a zuba a nono rabin kofi a juya asha da safe haka ma zaai da yamma,wato sau biyu a rana. Insha Allah indai an samu garin mai kyau akai kamar na sati 2 zaaga Nasara sosai cikin YARDAR ALLAH Allah yabada lafiya da zaman lafiya
Da Duminsa: Wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis

Da Duminsa: Wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, wutar Lantarkin Najeriya ta sake lalacewa a Yau Alhamis, 7/11/2024. Hutudole ya samu rahoton cewa wutar lantarkin ta lalace ne da misalin karfe 11:20am na yau Alhamis. Hukumar Nigeria National Grid ce ta tabbatar da hakan Wannan ne karo na biyu da wutar ta lalace a cikin satin da muke sannan karo na 12 a cikin wannan shekarar da muke ciki.
Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Tauraruwar Fina-finan Hausa,Asma Wakili ta ajiye mukamin da Gwamnan Kano,Abba Gida-Gida ya bata ta fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Duk Labarai
Mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da komawar Tauraruwar Fina-finan Hausa, Asma'u Abdullahi Wakili zuwa jam'iyyar APC. Ya wallafa hakane a shafinsa na zada zumunta inda ya yi mata maraba zuwa jam'iyyar APC. https://twitter.com/barauijibrin/status/1854270065547329955?t=7dvUTEwRZF-CKrPmAxoNAQ&s=19 Asma Wakili dai Hadimace ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf saidai ta ajiye mukamin nata inda ta kuma fice daga jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyyar APC. Sanata Barau yace Asma Wakili ta sanar da ficewarta daga NNPP a yayin ziyarar data kai masa a Abuja. Barau ya kara da cewa Asma Wakili ta bayyana ayyukan alkhairi na jam'iyyar APC ne ya jawo ta zuwa jam'iyyar. Yayi kira a gareta data zama jakadiya ta gari ga Masana'antarta ta Kannywood, Jam'iyy...
Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial  Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana ra'ayinsa akan mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata da yawa ya kuma dauki Bidiyon faruwar lamarin. Sanata Sani yace Dalilin da yasa ake samun irin mutumin masu lalata da matan mutane a Ofis shine mata basu son mata 'yan uwansu su zama ogannin su. https://twitter.com/ShehuSani/status/1854454657164156931?t=Y3ueoL-V8O9o9aKXhIBBWw&s=19 Lamarin mutumin ya dauki hankula sosai inda akai ta Allah wadai dashi inda wasu suka rika yaba masa.
A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Dangote kotu inda suka ce su ba za su sayi Man fetur daga matatarshi ba dan haka ya kyalesu su siyo daga kasashen waje

A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Dangote kotu inda suka ce su ba za su sayi Man fetur daga matatarshi ba dan haka ya kyalesu su siyo daga kasashen waje

Duk Labarai
Manyan 'yan kasuwar man fetur su A.A Rano, AYM Shafa da Matrix Petroleum Services Limited sun kai Aliko Dangote kotu inda suke bukatar kotu kada ta amince masa da bukatar da yayi na a hanasu siyo man fetur daga kasashen waje saidai su siya a hannunshi. Dangote dai ya shigar da 'yan kasuwar da NNPCL kotu inda yake neman kotun ta hana shigo da man fetur daga kasar waje a rika saya daga hannunsa. Dangote yace kawai ya kamata a shigo da man fetur Najeriya ne idan babu shi a matatarsa ko idan an samu karancinsa. Saidai su kuma 'yan kasuwar sun bayyana cewa Dagote na son ya zama shi kadai ne ke rike da harkar man a kasarnan wanda haka ba zai haifarwa kasuwar da mai ido ba. Sun ce idan aka baiwa Dangote wuka da nama na harkar zai zama shi kadai ne ke kayyade farashin wanda hakan bai k...