Ƙungiyar dattawan arewa ta buƙaci a yi bincike kan rikicin Natasha da Akpabio
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, wato Arewa Consultative Forum ko kuma ACF a taƙaice ta nuna damuwarta kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi wanda kakakin ƙungiyar, Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike mai kyau domin tantance sahihancin zargin, kamar yadda tashar Channels a shafinta na intanet.
"A yanzu dai yadda abubuwa suke shi ne zargin nan zai iya ɓata sunan Najeriya a idon duniya," in ji ƙungiyar, wadda ta nuna damuwa kan yadda a cewarta har zuwa yanzu, sanatocin arewa ne kaɗai suka fuskanci takunkumi kamar dakatarwa a majalisar ta 10.
"Wannan ya sa ACF ke fargabar ko dai abin ɓoye ne ya fara fitowa fili na...








