Alamomin ciwon koda da abincin mai ciwon koda
Aikin Koda a jikin dan Adam shine tace datti da ruwan da bai da kyau daga cikin jini, a yayin da ta daina aiki, datti zai taru a jikin mutum.
Abubuwan dake kawo cutar koda suna da yawa, amma akwai sauran ciwuka dake kawo cutar, kamar ciwon suga, hawan jini da sauran ciwuka dake dadewa a jikin dan adam.
Ciwon koda na saka lalacewar jijiyoyi, da Raguwar karfin kashi, da kuma saka rama.
Idan cutar ta yi muni, hantarka ta daina aiki kwata-kwata, saidai a koma inji ya rika wanke maka koda.
Ire-ire da kuma Abubuwan dake kawo cutar Koda.
Cutar Koda me tsanani:
Wannan itace cutar koda da hawan jini yake haddasawa wadda kuma itace aka fi fama da ita.
Takan dade a jikin mutum kuma za'a ga kullun lamarin kara munana yake.
Hawan jini ta haddasa turawa koda jini da yawa wanda ha...