Ya ake gane daukewar jinin haila
Ana gane daukewar jinin hailane ta hanyoyi kamar haka:
Yawan jinin da kike zubarwa zai ragu, a yayin da kika lura yawan jinin da kike zubarwa ya ragu to kinzo karshe ko kina gab da gama jinin hailarki.
Canjawar Kalar Jini: A yayin da jinin hailarki ya zo karshe, kalar jinin da kike zubarwa zai canja, zai zama kalar brown ko ruwan anta.
Alamomin jinin Al'ada da kike ji zasu kau, alamomin ciwon Mara, zazzabi ko rashin jin dadin jikinki da kike a yayin jinin Al'ada zasu kau
A yayin da kika gama jinin Al'ada, jinin zai tsaya gaba daya. A farkon fara jinin al'adarki zaki iya ganin jini Pink, idan ya kai tsakiya zai iya komawa jaa watau red, hakanan idan ya zo karshe, zai iya komawa light Brown, a yayin da kika gama gaba daya, zaki ga farin ruwane kawai yake fita daga gabanki.
Ya ...



