Ciwon mara bayan saduwa
Ciwon Mara bayan saduwa ko ace ciwon Mara bayan jima'i Abu ne da mata da yawa kan yi korafi akai.
Saidai jin ciwon Mara bayan jima'i a wasu lokutan Matsala ne a wasu lokutan kuma ba matsala bane.
Misali, mace zata iya jin ciwon Mara bayan saduwa idan ya zamana namijin da ta yi jima'i dashi yana da babbar mazakuta kuma a yayin da yake jima'i da ita ya rika tura mata mazakutar cikin farjinta sosai.
Dan kaucewa wannan matsalar, sai mace ta daina yin goho yayin jima'i kuma ta daina kwanciya namiji ya hau kanta, wadannan kalar kwanciyar su ne kesa mazakutar namiji ta rika shiga cikin farjinki sosai Wanda bayan an gama jima'i, zaki iya jin ciwon mara.
Maimakon goho da kwanciya, mace sai ta kwanta a gefen hagunta ko damarta shi kuma namiji ya kwanta ta bayanta su yi jima'in a haka, ko...