Saturday, December 6
Shadow
Da Duminsa: Jami’an tsaro sun dira a gidan tsohon Karamin Ministan Mai a lokacin Buhari, Timipre Sylva wanda ake zargin na da hannu a yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Da Duminsa: Jami’an tsaro sun dira a gidan tsohon Karamin Ministan Mai a lokacin Buhari, Timipre Sylva wanda ake zargin na da hannu a yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Duk Labarai
Rahotanni sun ce jami'an soji sun kai samame gidan tsohon Ministan man fetur a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari watau Timipre Sylva dake Abuja. Rahoton na Sahara reporters yace jami'an tsaron sun yiwa gidan kacha-kacha inda suka kuma tafi da wani dan uwan tsohon Ministan. Rahoton yace Ministan tuni ya bar Najeriya tunda aka fara mai wadannan zarge-zargen. Hakanan Rahoton yace an kuma kaiwa gidansa na Bayelsa samame. A baya dai an bayyana cewa akwai wani tsohon gwamnan Najeriya wanda shine ake zargin ya dauki nauyin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.
Wani Alhaji da ya bayyana a kafafen sadarwa yana sayawa ‘yan Mata Pizza ta Naira dubu ashirin da biyar kyauta ya jawo cece-kuce sosai

Wani Alhaji da ya bayyana a kafafen sadarwa yana sayawa ‘yan Mata Pizza ta Naira dubu ashirin da biyar kyauta ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
Wani Alhaji ya bayyana a kafafen sada zumunta inda yake sayawa 'yan mata Pizza ta Naira 25,000. Lamarin dai ya farane bayan da wata Budurwa ta koka da cewa, wai ace yanzu Pizza farashinta ya kai Naira 25,000. Ya bukaci ta tura masa bayanan bankinta dan ya bata kudin ta saya. https://twitter.com/TahirTalba/status/1982885088804384848?t=RyBzU42LUG7LCtg8opKqYw&s=19 Wannan abu yasa wasu suka rika kiransa da sunaye kala-kala saidai abin bai masa dadi ba inda shima ya rika mayar da raddi. https://twitter.com/TahirTalba/status/1982895187279122573?t=Nv6zKSus3EpNgd7tM6G2kA&s=19
Idan zaka iya ko kasan wani wanda zai iya, ana neman wanda zai iya yin zaman gidan Yarin Kuje dake Abuja na tsawon watanni 6, za’a rika biyan Naita Miliyan 1 duk wata

Idan zaka iya ko kasan wani wanda zai iya, ana neman wanda zai iya yin zaman gidan Yarin Kuje dake Abuja na tsawon watanni 6, za’a rika biyan Naita Miliyan 1 duk wata

Duk Labarai
Wata sanarawa ta bayyana a kafafen sada zumunta inda ake neman wanda zai iya yin zaman gidan yarin Kuje dake Abuja na tsawon watanni 6. Za'a rika biyan Naira Miliyan 1 duk wata, zai bayar da sunan wani na kusa dashi ne da za'a rika baiwa kudin. Sannan idan ya fito za'a bashi Naira Miliyan 5 dan ya kula da lafiyarsa. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1983128388953899185?t=oZbTPz3Vkofe208zwWYd7w&s=19 Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki. Saidai a shekarun baya, Hutudole ya taba ruwaito muku cewa, babban lauya, Femi Falana ya bayar da labarin cewa irin haka na faruwa. Idan aka yankewa wani shahararre hukunci, tun kamin aje gidan yarin akan hanya ko kumama a cikin kotun za'a rika tattaunawa a samo wanda zai yi zaman gidan yarin a biyashi, shi kuma wanda akawa hukunc...
Kalli Bidiyon: Ganin Tankokin dakon Man Fetur na Dangote sun rikita wasu ‘yan Kudu suna ta kukan cewa, zai mamaye ko ina

Kalli Bidiyon: Ganin Tankokin dakon Man Fetur na Dangote sun rikita wasu ‘yan Kudu suna ta kukan cewa, zai mamaye ko ina

Duk Labarai
Bidiyon tankokin Dakon Man fetur na Dangote sun firgita wasu 'yan Kudu inda suka rika fadar cewa Dangoten na son mamaye kowane bangaren kasuwanci. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1983051102062027216?t=PhIr9ISY7B6pqUD_oqQ62w&s=19 Dangote dai ya siyo dubban tankokin man fetur inda zai rika kaiwa wadanda suka sayi man fetur daga matatarsa man zuwa gidajen man su ba tare da sun biya ko sisi ba.
Wannan hoton da aka dauka a Abuja ya dauki hankula inda akai ta muhawara akansa

Wannan hoton da aka dauka a Abuja ya dauki hankula inda akai ta muhawara akansa

Duk Labarai
Wannan wani hoto ne da aka dauka a Abuja inda aka ga wasu na Sallah mace a gabansu itama tana Sallah. Da farko dai mutum zai ga kamar Matar tana jansu Sallah ne amma daga baya wasu sun rika bayyana cewa masallaci ne a cika sai aka yi sahu a waje itama ta shiga jam'i. Amma wasu na cewa, duk da haka wannan abun bai kamata ba. https://twitter.com/_MuhammadN/status/1982847836959002763?t=DB37Rs_cMB9WjlesSRSmHg&s=19
Da Dumisa: Dangote zai fara hako danyen ma Fetur

Da Dumisa: Dangote zai fara hako danyen ma Fetur

Duk Labarai
Rahotanni daga S&P Global sun ce Attajirin Najeriya, Aliko Dangote zai fara hako danyen man Fetur. Rahotan yace Dangote ya ari wasu rijiyoyin mai da ake kira da 71 da 72 wanda kamin karshe shekarar da muke ciki zasu fara hakar danyen man fetur din. Rahoton yace Rijiyoyin man zasu rika samar da ganga 40,000 ne a kowace rana. Wannan ci gaba karine kan matatar man fetur da yanzu haka Dangote ke da ita.
Kalli Bidiyo: Binciken da nayi akan Addinin Musulunci ne yasa na gano shine Addinin Gaskiya kuma na Musulunta>>Inji Wannan Inyamurar data Karbi Musulunci

Kalli Bidiyo: Binciken da nayi akan Addinin Musulunci ne yasa na gano shine Addinin Gaskiya kuma na Musulunta>>Inji Wannan Inyamurar data Karbi Musulunci

Duk Labarai
Wata Inyamura data bar Kiristanci zuwa Addinin Musulunci ta bayyana cewa bincikene ya kaita ga gane cewa Addinin Musulunci shine addinin Gaskiya. Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa ind aka ganta tana cewa, Data yi bincike akan Yahudanci ta gane cewa su basa son A shiga addinin su, wanda aka haifa a cikin Addinin shine kadai Bayahude na gaskiya. Sannan tace a Kiristanci kuma akwai abubuwan rudarwa da yawa inda tace data yi bincike akan addinin musulunci ne ta samu nutsuwa ta kuma karbi Musulunci. https://www.tiktok.com/@thatigbomuslim/video/7565518157373394198?_t=ZS-90v4gwD5XAf&_r=1
Subhanallahi: Kalli Bidiyon yanda wata Budurwa ta fito tana fadar munanan kalamai na zargi akan Abba El-Mustapha, da yawa na kiran cewa ya kamata ya kamata

Subhanallahi: Kalli Bidiyon yanda wata Budurwa ta fito tana fadar munanan kalamai na zargi akan Abba El-Mustapha, da yawa na kiran cewa ya kamata ya kamata

Duk Labarai
Wata budurwa ta fito ta bayyana kalamai na zargi ga Shugaban Hukumar tace fina-finai na Kano, Malam Abba El-Mustapha. Ta yi wannan bayanine a wani Tiktok Live da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta wanda wata me ammafani da sunan @Ummadaboibrahim0 a Tiktok a shirya, sannan wata me amfani da sunan @matandanaljannah ta yada inda take cewa lokacin suna yara, wai Abban ya yi yunkurin neman yayarta da lalata. Matashiyar dai a cewarta, tace Banda sun sha Sunnah da Abba ya lalatasu ita da yayar tata. Da yawa sun rika kira da cewa, Abba ya kamata ya kuma hukuntata saboda wadannan munanan zarge-zargen data yi masa. https://www.tiktok.com/@matandanaljanna/video/7565998277246700811?_t=ZS-90v0pz0IC1I&_r=1 Wannan kalamai zargi ne akan Abba El-Mustapha wanda matashiyar ta yi amfa...