KANO: An sace sadakin wata amarya a masallacin Juma'a na Kano ana shirin daura aure
Bayanai sun nuna cewa wakilin ango ya nemi sadaki ya rasa bayan an fara haramar daura aure…
Matasan turawa 50 maza da mata a kasar Denmark ne suka karbi addinin Musulunci.
Bidiyo ya nuna yanda matasan suke zaune a masallaci a gaban wani malami inda yake basu kalmar Shahada.
https://twitter.com/Saher95755738/status/1808998517387436171?t=9qSwZk823RTN4lC1W5qoQg&s=19
Allah ya sanyawa rayuwarsu Albarka.
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Karbi Bakuncin Tsohon Mawaƙinsa, Wanda Ya Yi Wakar "Yau Nijeriya Riƙo Sai Mai Gaskiya" Ibrahim Yala Kaduna A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina ranar Alhamis.
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Sadiya Haruna Ta Grime Ni, Shekaru Na 35 Ita Kuma Shekarunta 48, Kuma Kafin Mu Rabu Na Ba Ta Hakuri Ya Fi Sau Milyan Duk Da Cewa Ita Ta Yi Min Laifi, Saboda Na Kama Ta Tana Cin Abinci Da Wani Gardi Da Muharraminta Ba, Cewar G-Fresh Al'Amin.
Lamarin dambarwar Auren G-Fresh Al'amin da matarsa Sadiya Haruna ya zama babban batun tattaunawa a kafafen sada zumunta da yawa.
A baya dai Hadiza Gabon ta yi hira da Sadiya Haruna a kafarta ta YouTube inda kuma ta sake gayyato Shima G-Fresh din ta yi hira dashi.
DAMBARWAR MASARAUTAR KANO: Lauyoyin Sarki Aminu Ado Bayero Sun Janye Daga Tsaya Masa
Daga Bashir Gasau
Babbar Kotun Jihar Kano me Lamba 7 dake zamanta a sakatariyar Audu Baƙo, ƙarƙashin jagorancin me shari'a Amina Adamu Aliyu, ta ce tana da hurumin sauraron ƙarar da Gwamnatin Kano da sauran wasu ɓangarori suka shigar.
Alkaliyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take yin ƙwarya-ƙwaryar hukunci akan batun hurumin kotun, a yayin zaman kotun na yau Alhamis harma ta ayyana ranar 15 ga watan nan da muke ciki a matsayin ranar da za ta ci-gaba da sauraron Shari'ar.
Toh sai dai bayan ƙwarya-ƙwaryar hukuncin kotun, Lauyoyin Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero suka fice daga kotun harma kuma bayyana cewa, zasu je su zauna da sarkin domin neman sabbin lauyoyin da zasu ci-gaba da tsaya...
Mun Yi Zaton Za'a Bashi Minista ~ 'Yan Kwankwasiyya Sun Yiwa Gawuna Shăgúbe Kan Muƙamiń Da Tinubu Ya Bashi
"Babu ofis, Babu albáshi, alawus sau ɗaya káwai a shékara wanda hákan ma sai an samu sahalewar mataimakiń shugabań jami'a." Inji su
Menene ra'ayinku?
Ban Taba Zuwa Gidan Sadiya Haruna Ba, Bare Har Na Ci Abinci Tare Da Yin Bacci A Gidanta, Cewar Alkalin Da Ya Yanke Mata Hukuncin Watanni Shida A Gidan Yari
Alkali Mukhtar Dandago ya ci gaba da cewa Sadiya ta yi hakan ne don kawai ta bata masa suna a idon duniya.
Idan ba a manta ba dai, a wata hira da aka yi da Sadiya Haruna ne ta bayyana cewa Alkalin da ya yanke mata hukuncin watanni shida a gidan yari har gidan ta yana zuwa, kuma ta dafa masa abinci har ma ya yi bacci.
Me za ku ce?
Alkali Mukhtar Dandago ya ci gaba da cewa Sadiya ta yi hakan ne don kawai ta bata masa suna a idon duniya.
Idan ba a manta ba dai, a wata hira da aka yi da Sadiya Haruna ne ta bayyana cewa Alkalin da ya yanke mata hukuncin watanni shida a gidan yari har gidan ta yana zuwa, kuma ta dafa masa abinc...
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa, Albashin 'yan majalisar tarayya baya wuce kwanaki 3 ya kare.
Dogara yayi kira ga 'yan majalisar da su bayyanawa 'yan Najeriya kudaden da ake biyansu dan a daina musu kallon suna samun kudaden da ba haka bane.
Yace a lokacin da yake kakakin majalisa yana karbar kasa da Naira Dubu dari hudu a matsayin albashi.
Yace kuma yana karbar Miliyan 25 a matsayin alawus, yace bai taba yin amfani da alawus din ba, ya bude asusun ajiya na daban ne inda ya baiwa akawunsa umarnin ya rika yiwa mutane hidima da kudin kuma idan suka kare, ya rika rantowa.
Yace dama Albashi shine na dan majalisa a yayin da Alawus kuma na yiwa mutanen da suka zabeka aiki ne.
Ya bayyana hakane a wajan wabi taro a Abuja.