Tafarnuwa na daya daga cikin abubuwan da aka dade ana amfani dasu wajan maganin gargajiya shekaru da yawa da suka shide a Duniya.
Misali ana amfani da tafarnuwa wajan magance matsalar Ciwon zuciya, kara karfin tunani da magance ciwon mantuwa, tana karawa garkuwan jiki inganci, tana bayar da garkuwa ga cutar daji watau Cancer kala-kala.
Amma a wannan rubutu, zamu yi maganane akan yanda ake amfani da Tafarnuwa wajan magance matsalar sanyi.
Domin Maganin Sanyi ana tattauna Tafarnuwa ko a daddakata a rika sha.
Hakanan bincike ya bayyana cewa, Cin Tafarnuwa yana baiwa mutum garkuwa daga kamuwa da ciwon sanyi da mura.
Hakanan ko da mutum ya kamu da murar idan dai yana cin tafarnuwa kullun to murar ba zata dade ba zata warke, kamar yanda masana suka sanar.
Masana sun ce ana son...
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa, muƙamin da ɗantakarar jam'iyyar PDP na muƙamin a 2023, ta ce yake ta faman nema har sau shida amma bai yi nasara ba.
Fadar shugaban ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙon Tweeter da ya sanya kwanan nan.
Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa....
Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma.
Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela.
A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel.
A ranar Juma'a al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa.
Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyo...
Hukumar kula da harkokin shari'a ta jihar Kano a arewacin Najeriya ladaftar da wasu ma'aikatanta takwas ciki har da alkalai.
Wani kwamitin ladaftarwa na hukumar ne ya bayar da shawarar ɗaukar matakin bayan kammala bincikensa kan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka gabatar waɗanda suka haɗa da zarge-zargen karɓar rashawa.
Kwamitin karɓar korafe-korafen jama'a na hukumar kula da harkokin shari'ar ya ɗauki matakin ladaftawar ne kan ma'aikatan shari'a su takwas ciki har da alkalan kotunan majisteret.
Kakakkin hukumar Baba Jibo Ibrahim ya ce bincike ya gano yadda wani alkalin kotun majistare ya gudanar da wata shari’a ba tare da an rubuta ta ba, abin da ya saba dokokin shari’a.
Bayanai na cewa an jima ana kokawa da jami’an kotu a jihar game da yadda suke karbar toshiyar baki da sauran laifu...
Ana sa ran binne marigayi babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Taoreed Lagbaja ranar Juma'a a Abuja.
Yayansa da yake bi, Moshood Lagbaja, ne ya bayyana haka a garin Osogbo, jihar Osun a lokacin da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar St Charles Grammar School Osogbo, (SCOBA), ta kai wa iyalan ziyarar ta'aziyya.
Moshood ya ce hukumomin soji sun ce ba za su ba iyalan gawar marigayin ga, amma sun bayar da tabbacin cewa za a yi masa jana'iza da ta dace a Abuja, ranar Juma'a.
Gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar rasuwar babban hafsan sojin na ƙasa ne da ta ce ya rasu ranar 5 ga watan nan na Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Kafin tabbatar da rasuwar, an fara raɗe-raɗin cewa babban hafsa...
Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa.
Taron wanda aka a fara a yau Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.
Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.
Shugaba Tinubu a bayanin da ya yi a gaban taron ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila a Gaza, inda ya yi gargaɗin cewa " an kwashe lokacin mai tsayi ana wannan rikici kuma hakan ya haifar da wahalhalun da ba za su ƙirgu ba."
Ka zalika ya nuna damuwa kan matsalar kayan agaji a rikicin na Gabas ta Tsakiya.
"A matsayinmu na wakilai daga ƙasashen da suke mutunta adalci da...
An daura auren wasu ma'aurata a jihar Katsina su 4 inda daga baya suka tare a birnin Karbala na kasar Iraqi.
Hotunan ma'auratan sun watsu sosai a kafafen sada zumunta inda mutane da yawa ke ta yabawa.
Farashin daukar man fetur daga inda ake kawo shi a Najeriya ya ragu sosai inda ya samu ragowar kaso 20.34 cikin 100.
Man a yanzu ana daukarsa akan farashin 971.57 kan kowace lita.
Da alama hakan zai kawo sauki sosai a Najeriya lura da cewa tashi ko saukar farashin man fetur din na taba abubuwan amfani da yawa.
Saidai abin mamaki, duk da raguwar farashin, a bangaren 'yan kasuwa masu sayarwa da mutane a gidanjen man fetur farashin karuwa yayi.
An dai samu karuwar Naira 443 ko ace kaso 79.71 cikin 100.
Daga Naira 617 zuwa Naira 1,060.
Rahoton jaridar Punchng ya nuna cewa a watan Augusta da ya gabata an shigo da man fetur din akan Naira 1,219 amma a watan Nuwamba an shigo dashi akan farashin N971.5.
Saidai duk da haka maimakon farashin man fetur din ya ragu sai ma karuwa y...
'Yansanda a Ota dake jihar Ogun sun kama wani mutum me suna Olubunmi Johnson dan kimanin shekaru 55 saboda kunnawa matarsa wuta.
Lamarin ya farune da misalin karfe 8:30 pm na ranar Juma'ar data gabata a gidansu dake kan titin Fagbuyi na yankin Ilogbo.
Wanda ake zargin ya jike matarsa da man fetur sannan ya kunna mata wuta.
Kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ta bayyana cewa, dangin matar ne suka sanar dasu abinda ke faruwa.
Tace an garzaya da matar zuwa Asibiti inda shi kuma mijin aka kamashi inda ake bincikensa kan yunkurin yin kisa.