Yadda amarya zatayi a daren farko
Amarya a daren farko, duk yake cewa ke ba bakuwa bace a wajen saurayinki, ya kamata ace ki zama me kunya a wannan dare.
Saboda a bisa zuciyar ango yana tsammanin zaku yi abinda baki taba yi ba, dan haka ko da baki jin kunyarsa, a wannan dare ya kamata ki nunawa angonki kina jin kunyarsa da dardar na abinda zai faru a wannan dare.
Wasu ma'auratan saboda dalilai da yawa, basa samun yin jima'i a wannan dare. Idan haka ta faru dake, sai muce kin zama 'yar gida, duk yadda kuka yi daidai ne ke da angonki tunda kun kwana a gado daya daki daya.
Amma idan za'a yi jima'i a wannan dare, ko kusa kada ki nunawa angonki kin san me zai faru, ki barshi yayi komai da kansa, ko kuma ya jagoranci duk abinda zai faru a wannan dare.
Kada ki ci kazar amaryaci sai ya miki tayi ko kumama ya baki a bak...