Tuesday, April 21
Shadow

Addu’a ga mijina

Addu'a, Auratayya
A matsayinki na matar aure, ya kamata ki rika yiwa mijinki addu'a a gaban idonsa da bayan idonsa. Misali: Idan mijinki ya miki kyauta, ki gode masa da fatan Allah ya kawo karin Arziki. Idan mijinki ya kawo kayan abinci, ya miki dinki, yawa yara dinki ko sayen wani abin farantawa, ya kamata ki masa addu'a a gabansa a bayyane ya ji, hakan zai kara karfafashi da himmatuwa wajan kara yin kamar hakan ko fiye da hakan nan gaba. Hakanan ki koyawa 'ya'yanki godiya, idan nahaifinsu ya musu kyauta, su gode masa su kuma yi masa addu'ar budi da kariya: A yayin da mijinki ya fita nema kuma baya tare dake, yana da kyau ki sakashi a addu'a a yayin da kika yi sallar Walha, da sauran salloli na farilla. Ki mai fatan kariya daga sharrin mahassada, da sharrin karfe, da sharrin baki, da saur...

Sakon fatan nasara ga masoyi

Soyayya
Masoyina ina maka fatan Allah ya kareka. Addu'a nake maka kullun Rabbana ya hore. Allah yasa ka fi haka. Masoyina Allah ya kawo budin kasuwa ya daukaka ka akan sa'anninka. Ina maka fatan kamar yanda kake neman Arziki ta hanyar halaliya, Allah ya Azurtaka ta hanyar halaliya. Ina Addu'ar Allah ya makantar da kai daga ganin haram, ya bude idanunka wajan ganin halal, Allah ya hana bakinka cin haram, ya bude maka shi wajan cin halal, Allah ya daure hannuwanka kada su kai ga Haram, Ya sakesu su yi walwala wajan yakin neman Halal. Masoyina kullun ina alfahari da kai kan yanda kake jajircewa wajan neman na kanka, ina fatan Allah ya wadatar dakai. Makiyanka sai sun yi kunci saboda nasarar da zaka samu, mahassadanka sai ciwon zuciya ya kamasu saboda daukakar da zaka samu, sa'ann...
Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Ji yanda ta kaya bayan da gwamna Abba yace a rushe gidan Nasarawa da Sarki Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki

Kano, Siyasa
A jiyane dai rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rushe fadar Nasarawa wadda sarki Aminu Ado Bayero ke ciki da nufin gyarata. Saidai tuni jami'an tsaro sukawa fadar kawanya dan hana aiwatar da wannan umarni. A jiyandai, Tuni har an kai motocin dake rushe gida fadar ta Nasarawa amma lamarin bai tabbata ba. Tun a jiyan dai, Wasu masu sharhi akan al'amuran yau da kullun ke ganin cewa, wannan umarni kuskurene saboda ba'a kammala shari' ba. Daya daga cikin masu irin wannan ra'ayi shine, Salihu Tanko Yakasai wanda yace gwamnan zai saka ai masa dariya saboda wannan umarni da ya bayar: https://twitter.com/dawisu/status/1803884035124474006?t=sGU-jQHoxSU0qi4uYksphQ&s=19 Wannan hukuncin kotu dai ya kawo rudani a Kano inda kowane...
Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa an sace wata mata mai juna biyu mai suna Mrs Ogunbunmi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Majiyar mu ta rawaito cewa Matar wadda aka ce za ta haihu ta bar gidanta da ke Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar, Ijaiye dake Abeokuta,sai dai an yi garkuwa da ita a hanya. Mijinta, Ogunbunmi Lateef, ya ce ya samu sakon WhatsApp da ke sanar da shi sace matarsa. Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba. A cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Alhamis, ta ce, “Wani Ogunbunmi Lateef na Oke Lantoro ya rawaito cewa matarsa mai juna biyu da za ta haihu ta bar gida zuwa Asibitin Jihar Ijaiye Abeokuta. Ogun na daya daga cikin jihar da ke fama da yawaitar laifuka a yankin Kudumaso Yamma. D...

Sakon rashin lafiya ga masoya

Soyayya
Allah ya baki lafiya masoyiyata. Ina fatan wannan rashin lafiya ta zama kaffara ga zunubanki. Rashin lafiya ka iya zama Alheri ta hanyar kankare zunubai idan mutum ya dauka cewa kaddara ce daga mahalicci ba wanine ko rashin wayonsa ne ya dora masa ba, ina fatan kina da wannan yakini dan samun amfanin wannan dama. Cuta ba mutuwa bace masoyiyata ki koma ga Allah da neman gafarar zunubai. Kullun ina sakaki a addu'a Allah ya baki lafiya masoyiyata. Masoyiyata ki daure ki tashi, Dan amfanin kanki da sauran na kusa dake. Masoyiyata insha Allahu zaki warke, ki yi imani da Allah da kuma fatan cewa zai baki Lafiya. Masoyiyata ba zan iya jure rashinki ba, Insha Allahu kina daf da samun lafiya. Duk runtsi duk wuya ina tare dake, wannan rashin lafiya jarabawace wadda kuma zata ...

Addu’a ga masoyiyata

Addu'a, Soyayya
Ina fatan Allah ya haskaka rayuwarki. Fatana shine ki fi kowa a tsakanin sa'anninki. Allah yasa mu zama mata da miji. Allah yawa soyayyarmu Albarka ta yanda zamu yi aure mu haifi 'ya'ya masu Albarka. Ina fatan Allah ya kareki daga sharrin makiya, Mahassada da kambun baka, masoyiyata kada ki manta da karanta falaki da Nasi safe da yamma. Kina da kyau, dan haka nasan akwai mahassada da masu mugun baki, fatana shine Allah ya kareki daga dukkan sharrinsu. Kina da Basira, Fatana shine Allah ya kareki daga sharrin mahassada. Babyna ki kasance kullun cikin zikiri, zaki rabauta daga sharrin shedan la'ananne. Insha Allahu duk inda zaki shiga sai Allah ya hadaki da masoya na gaskiya. Babban burina shine inga Allah ya daukakaki a tsakanin sa'anninki. Masoyiyata Ki rike s...
Duk da Sallah ta wuce, Farashin Timatir bai sakko ba

Duk da Sallah ta wuce, Farashin Timatir bai sakko ba

Kasuwanci
Duk da cewa bukukuwan sallah sun wuce farashin timatir da na yaji basu sauko ba a Arewa. Hakan kuma na faruwane duk da yake cewa, a yanzu ne sabbin wadannan kaya suka shigo kasuwa. Bincike a jihohin Kaduna, Gombe, Nasarawa, Kogi, Adamawa, Taraba, Benue, da Sokoto ya nuna cewa maimakon farashin kayan ya sauka, kara tashi yayi sosai. Mutane da dama sun koka kan wannan lamari.

Kalaman yabo ga masoyiyata

Kalaman Soyayya
Kece tawa wadda ba zan bari kowa ya taba min ke ba. Ina sonki fiye da yanda kike tunani. Ke kyakkyawace ga kwarjini. Idan kika yi murmushi ji nake kamar shokin din wutar lantarki ya kamani. Babu wanda zai rabani dake ba zan taba yadda ba. Idanunki farare kamar farin wata. Shin wai meke faruwane, kullun idan na ganki sai inga kina kara kyau. Hakoranki fari tas babu datti kamar Alli. Gaki da dogon hanci kamar biro. Ke ba balarabiya ba amma kinfi larabawa gwarjini. Ke ba baturiya ba amma kinfi turawa kyan diri. Ke ba 'yar Indiya ba amma kinfi matan indiya zubi. Dirinki kamar na kwalbar lemun koka kola ko kuma ince kalangu. Diddigenki daf-daf be yi fadi ba kuma bai yi kankanta ba. Fatarki kullun sheki take kamar madubi. Fuskarki tana matukar burgeni...
Bidiyo:Kalli Yanda murna ta barke a fadar Nasarawa inda Sarki Aminu yake bayan hukuncin kotu

Bidiyo:Kalli Yanda murna ta barke a fadar Nasarawa inda Sarki Aminu yake bayan hukuncin kotu

Duk Labarai
Hukuncin Kotu yasa murna ta barke a fadar Nasarawa inda Sarki Aminu Ado Bayero yake. An ga matasa na buga wutar murna inda suke nuna cewa sune suka yi nasara a kotu: https://twitter.com/Maxajee/status/1803838154002071587?t=IpCb8x85m_7JUThqy_OdsQ&s=19 Kano dai ta dauki dumi inda kowace bangare tsakanin na Sarki Muhammad Sanusi II da na Sarki Aminu Ado Bayero ke cewa shine yayi nasara a kotun.