“Mataimakin Gwamna A Najeriya Kamar Ba Ka Da Aiki Ne” — Tsohon Mataimakin Gwamna
Yanzu haka dai wani tsohon ministan lantarki kuma tsohon mataimakin gwamna a jihar Yobe, ya ce babban sirrin zama mataimakin gwamna da gwamnan kansa shi ne yin gaskiya da riƙon amana da kuma biyayya.
Injiniya Abubakar D. Aliyu ya ce duk da yake tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi muƙamin mataimakin gwamna, amma kuma bai tanadar masa wani taƙamaiman aiki ba, don haka “in dai kana so ka yi, ka zauna kawai. Abin da gwamna ya ce ka yi, ka yi. In ya ce kar ka yi, ka bari”.
A cewarsa: “Ba zancen kai Mataimakin gwamna (ne ba), ai tare muka je mu kai kamfen, ai tare muka je! Ai gwamnatin, tsarin mulki ne yake ajiye ta, to kai kuma tsarin mulki ba abin da ya ba ka”.
Tsohon Ministan ya Bayyana hakan ne a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya albarkacin cikar...







