Wednesday, March 11
Shadow
ALLAH SARKI: Ga Damina Ta Zo Amma Kauyyka Da Dama A Jihar Sokoto Sun Zama Kufai Babu Halin Noma Saboda Matsalar Tsaro

ALLAH SARKI: Ga Damina Ta Zo Amma Kauyyka Da Dama A Jihar Sokoto Sun Zama Kufai Babu Halin Noma Saboda Matsalar Tsaro

Sokoto
ALLAH SARKI: Ga Damina Ta Zo Amma Kauyyka Da Dama A Jihar Sokoto Sun Zama Kufai Babu Halin Noma Saboda Matsalar Tsaro Tun daga1-Tashar Bagaruwa,2-Gidan Auta,3-Teke mai kasuwa,4-Tashar Ango,5- Teke mai Fuloti,6- Gidan Alewa,7- Kuka Majema,8- Kuka Tudu,9-Kuka,10-Inwala,11-Gidan Ayya,12- Santar Dan Hillo,13- Hawan Diram,14- Dakwaro, duk sun watse ba mutane, gashi ruwan shuka sun sauka amma an kori jama'a daga gidajen su maimakon suyi shukar da za su noma, wannan tashin hankalin dame ya yi kama? Muna kira ga hukumomin da wannan al'amarin ya shafa da suyi gaugawar ɗaukar matakan da suka dace. Ya Allah albarkacin wannan ranar ta Juma'a ka kawo mana karshen wannan tashin hankalin. Daga Rabiu Abdullahi KG31/5/202423/11/1445
Tsananin zafi na ci gaba da kashe mutane a Indiya

Tsananin zafi na ci gaba da kashe mutane a Indiya

Duk Labarai
Rahotanni na cewa an samu mutuwar mutane da dama sakamakon tsananin zafi a Indiya. Hukumomin jihohin gabashin ƙasar, Odisha da Bihar sun ce mutane 15 ne suka rasu a ranar Alhamis, kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin. An haramtawa ma'aikata zirga-zirga a tsakiyar rana. Ana hasashen cewa za a ci gaba da fuskantar tsananin zafi a gabashi yayin da ake hasashen za a samu sauƙin zafin a Arewa maso Yamma da kuma tsakiyar Indiya.
Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Siyasa
Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya. Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma'a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin. A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin. Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya. Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta....
‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

‘Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi’

Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Siyasa
Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi 'yan ƙasar a kan fifita siyasar kuɗi maimaikon zaɓar mutane masu aƙidar da za su iya kawo canji. Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce dimokraɗiyyar Najeriya ta samu koma-baya saboda wasu 'yan siyasa da kan sayi ƙuri'un mutane ta hanyar ba su atamfa ko taliya. A cewarsa, irin wannan tunani na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa al'ummar ƙasar cikin halin matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaron da hukumomi suka gaza shawo kansu ya zuwa yanzu. Ya kuma ce rashin iya mulki ne ya haddasa taɓarɓarewar al'amura kamar tsaro da tattalin arziƙi a Najeriya. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana haka a jerin hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasar Nijeriya a wani ɓangare na cika shekara 25 da mulkin dimokraɗiyya karon...
Bidiyo: Ya Allah ka Bani Yarinya me Hali da Dabi’u irin na Murja Kunya>>G Fresh Al’amin

Bidiyo: Ya Allah ka Bani Yarinya me Hali da Dabi’u irin na Murja Kunya>>G Fresh Al’amin

G-Fresh Al'amin, Murja Ibrahim Kunya, Nishadi
Tauraron dan Tiktok kuma mawaki, G-Fresh Al'amin yayi rokon Allah ya bashi diya kamar Murja Kunya. An ganshi a wani Bidiyo ya daga hannuwa sama yana rokon Allah ya bashi diya irin Murja. G-Fresh ya kuma yi fatan cewa duk abinda yake yi, yana son dansa shima yayi. Kalli Bidiyon anan: https://www.tiktok.com/@kanostatematerial/video/7375257438032874757?_t=8mpTddptPJl&_r=1 G-Fresh dai na daya daga cikin mutanen da suka fi daukar hankula a shafin na Tiktok shi da murja Kunya. Da yawa dai na Allah wadai da abinda Murja Kunya ke yi a shafin na Tiktok inda kwanannan sai da aka kamata har aka kaita Asibitin Mahaukata a Kano. Saidai daga baya ta bar Kano inda tace ita da garin har Abada.
Hotuna:Hadiza Gabon ta bayyana ainahin shekarunta yayin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta

Hotuna:Hadiza Gabon ta bayyana ainahin shekarunta yayin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta

Hadiza Gabon, Kannywood
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta inda tace ta cika shekaru 35. Hadiza ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda kuma masoya da abokan arziki suka yi ta tayata murna. Da yawa dai masu murnar ranar haihuwarsu basu cika bayyana shekarunsu ba, amma Hadiza Gabon ta yi ta maza ta bayyana cewa shekarunta 35. Ko da yake a hakan ma wasu da yawa sukan karyata. Daga cikin abokan aikin Hadiza Gabon: Shamsu Dan iya ya tayata Murna inda ya saka hotonsu tare a shafinsa da yi mata fatan Alheri: Sauran wanda suka taya Hadiza Gabon murna sun hada da Dj Abba, Hassan Giggs, da dai sauransu.
Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dawo da taken Najeriya na daya daga cikin muhimman abubuwan da yake son yi a mulkinsa. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar dattawan Najeriya, ACF. Tinubun dai ya sakawa dokar data dawo da tsohon taken Najeriya hannu wanda hakan ya jawo cece-kuce inda mutane ke cewa ba wannan ne matsalar kasar ba. Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankali kan samun hadin kai a Najeriya.
Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar ‘Yansanda

Siyasa, Tsaro
Hukumar 'yansandan jihar Legas ta bakin tsohuwar kakakin hukumar, Dolapo Badmus ta bayyana cewa rashin iya taken Najeriya, kwakaki 3 bayan shugaban kasa ya saka shi a matsayin doka babban laifi ne. Ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda take bayar da misalin wani me makaranta data sa a kama saboda yana rera tsohon taken Najeriyar. Tace rashin iya taken Najeriyar cin amanar kasa ne. Ta baiwa mutane shawarar su samu lauyoyi su musu karin bayani. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria signed and assented the New National Anthem into law and you are not able to recite it in a whole, then you are a suspect I just passed through a private school and I could here them singing the old National Anthem! "Arise oh compatriots"! (We are...
Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Za’a kama shugaban wata makaranta saboda ya bar dalibansa na rera tsohon taken Najeriya

Siyasa, Tsaro
Tsohuwar kakakin 'yansandan jihar Legas, Dolapo Badmus ta yi kiran a kama shugaban wata makaranta me zaman kanta da babban malamin makarantaar saboda rera tsohon taken Najeriya. Ta bayyana cewa, ta zo wucewa ta kusa da makarantar ne sai ta ji suna rera tsohon taken Najeriyar. Tace tuni ta yiwa 'yansanda magana kan a kamasu tare da gurfanar dasu a gaban kotu dan musu hukunci. Tace kwanaki 3 bayan da shugaban kasa ya sakawa dokar canja taken Najeriyar hannu, duk wanda aka samu bai iyashi ba, to me laifi ne. Tace kada wanda ya tambayeta laifin me suka yi, duk wanda ke da tambaya, ya samu lauya ya masa karin bayani. Tace duk wanda bai iya sabon taken Najeriya ba, to yana cin amanar kasane. ‘’If, as at today, three days after the President of Federal Republic of Nigeria sign...