
Rahotanni daga jihar Imo na cewa, ‘yansanda sun kama malaman jami’ar Imo State University (IMSU) dake karkashin kungiyar malaman jami’a ta ASUU dan sun bayyana cewa zasu je yajin aiki.
Rahoton yace an kamasu ne bayan wani shiri da aka yi dasu a wani gidan rediyo na jihar inda suka bayyana aniyarsu ta shiga yajin aiki saboda rashin cika alkawarin da Gwamnati ta musu.
Malaman sun bayyana cewa ya kamata alkawarin da gwamnatin tarayya tawa jami’o’in Najeriya ya hada hadda jami’o’in Jihohi.
Daga cikin wadanda aka kama hadda shugaban kungiyar ASUU din na jihaa, watau Chairman, Stephen Oguji.
Saidai Rahoton Vanguard ya ce daga baya an sakesu.
Amma kungiyar ta ASUU tace wannan ba zai bata tsoro ba.
Tuni dai kungiyar ASUU ta kasa ta sanar da cewa, zata bayar da kwanaki 14 a biya mata bukatunta ko kuma ta shiga yajin aiki.