
Wani bincike da aka gudanar a kasashen Duniya guda 105 inda aka yi gwajin akan mutane 60,000 ya bayyana cewa, Najeriya ce kasa ta Daya a Duniya wadda mutanen ta suka fi kirki da taimakon mabukata da bayar da kyauta.
Wata kungiyar bayar da Agaji ta Duniya, the Charities Aid Foundation (CAF) ce ta gudanar da wannan bincike.
Binciken ya gano cewa a mafiya yawan kasashen da aka gidanar da binciken, an gano cewa, mutane suna bayar da kyauta ko sadakar kaso 1 cikin 100 na kudin da suke samu.
Kasashen Africa ne kan gaba inda su kuma suke bayar da kaso 1.6 na kudin shigarsu sadaka, kyauta ko dan ci gaban addini.
Kasashen turawa kuwa, suna bayar da kaso 0.6 cikin 100 ne na kudin shigarsu a matsayin sadaka ko kyauta.
Saidai a gaba dayan kasashen duniyar, Najeriya ta zo ta daya inda mutanen Najeriya ke bayar da kaso 2.8 cikin 100 na kudin shigarsu a matsayin tallafin ci gaban addini, ko kyauta, ko sadaka ga mabukata.
Hakanan Binciken ya gano cewa kasashe 10 da suka fi kowane kasashe a Duniya bayar da taimako da tallafi suna kasashen Afrika da Asia ne.
Shugaban Kungiyar agajin, Mark Greer yace bayar da agaji ga mabukata da kungiyoyi, da kasuwanci, zai taimaka matuka wajan inganta zamantakewa.