BABBAR MAGANA: “Na auro matata daga ƙasar Morocco amma Shaik Ahmed Gumi ya zalunce ni ya ƙwace mun ita, yau tsawon wata 11 kenan tana hannunsa. Ina neman shugaban ƙasa da gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani da hukumomin tsaro su shiga maganar shari’a ta yi aikinta” In ji wannan mutumin mai suna Nasir Musa Idris.

Yace Sheikh Gumi ya rika kokarin yi masa wayau yana cewa wai matar tasa yarinyace ya saketa duk da cewa ta haura shekaru 20.
Ya kara da cewa Sheikh Gumi bai taba sanin matarsa ba kuma baida alaka da ita ko ta kusa ko ta nesa, yace sun je sayen maganine a wani kemis suka hadu.
A cewarsa daga nan Sheikh Gumi ya ke ta kokarin ganin sai ya saki matar tasa yace har kotu ya kai maganar
Ko yaya kuke ganin wannan zargi nasa?