Saturday, May 17
Shadow

Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba.

Ya bayyana hakane a wajan taron Jam’iyyar PDP da aka gudamar a Jiya Asabar inda yace masu ruguguwar komawa APC suna yi ne dan neman na Abinci.

Yace ba dan mutane ‘yan siyasar suke komawa APC ba inda yace ta yaya zasu rika saurin komawa Jam’iyyar duk da matsin tattalin arzikin da ake fama dashi da kuma rashin iya mulki na Jam’iyyar.

Yayi kira ga ‘yan Adawa da su hada kai a shekarar 2027 su kawar da Jam’iyyar ta APC daga mulki.

Karanta Wannan  A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *