
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Asiya Nasiru El-Rufai da kishiyarta, Aichatou sun kira taron manema labarai inda a ciki suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya taimaka ya saka baki a maganar shari’ar mijinsu.
Tace babu lungu da sakon da bata shiga ba a Kaduna tawa Shugaba Tinubu yakin neman zabe sannan kuma shima mijinta ya masa yakin neman zabe.
Tace ba wai sun ce kada a hukunta mijin nasu ba amma a bashi hakkokin da doka tace a bashi na ganin likitansa da bayar da belinsa.
Tace suna neman a sassauta sharudan belin da aka gindaya masa inda tace wanda aka saka masa yanzu sun yi tsauri ba zai iya cikasu ba.