Monday, September 14
Shadow

Zainab ta baiwa mutane Tausai saboda Labarin rayuwarta

Zainab kenan wadda labarinta ya haiwa mutane da yawa tausai sosai.

Tace lokacin data taso basu da abinci a gidansu, Takan yi kawaye wanda gidansu akwai abinci kawai dan ta samu abinda zata rika ci.

Tace bata da kayan sakawa Uniform kayan makaranta take bari a jikinta har dare yayi sannan ta cire ta wanke.

Tace makarantar ma kyauta ta yi, me makarantar bama musulmi bane amma haka ya barta ta yi karatu bai taba tambayar mahaifiyarta kudin makaranta ba.

Tace kuma data gama ya biya mata JAMB

Tace yanzu ta bude shagonta sannan ta kai mahaifiyarta aikin Umrah

@tubless_media_concept

Mun sha kwana ba mu ci abinci ba… wata magana daga bakin Zainab Muhammad, wadda aka fi sani da Mrs. Zanel, yayin da take ba mu labarin wasu daga cikin ƙalubalen rayuwar da ta fuskanta kafin ta kai matsayin da take a yau. Daga rayuwar ƙalubale zuwa zama ɗaya daga cikin fitattun masu ɗinkin zamani na maza a birnin Abuja, Mrs. Zanel ta bayyana mana yadda jajircewa, haƙuri da taimakon Allah suka sauya mata tafiyar rayuwa. A cikin wannan hira ta musamman a Rayuwata Talk Show, za ku ji labarin mutumin da ya taimaka mata wajen biyan kuɗin makaranta, yadda ta fara sana’a tun bayan zuwanta Abuja domin NYSC, da kuma yadda daga ƙarshe ta gina nata Company kuma ta zama sananniya a fannin fashion. Wannan labari nata cike yake da darussa ga duk wanda yake cikin ƙalubale kuma yake da burin canza rayuwarsa. Ku kalli cikakkiyar hirar yanzu domin jin wannan labari mai cike da ƙoƙari, haƙuri, taimako da ikon Allah. 🎙️ Rayuwata Talk Show — Telling Real Life Stories Powered by Tubless Media Concept

♬ original sound – tubless_media_concept
Karanta Wannan  Kalli Hotunan wata halitta da ba'a taba ganin irinta ba da Turawa suka gano a karkashin ruwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *